Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Laraba

5 Faburairu 2020

10:47:26
1008126

​Iran Ta Jaddada Goyan Bayan Ta Ga Palasdinu

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da goyan bayan kafa gwamnatin Palasdinu da ta kunshi Qudus babban birni.

(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da goyan bayan kafa gwamnatin Palasdinu da ta kunshi Qudus babban birni.

M. Zarif, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya kuma kalubalanci yarjejeniyar da ake dangantawa data karni ta shugaba Donald Trump na Amurka kan rikicin Palasdinawa da yahudawan mamaya na Isra’ila.

A don haka a cewarsa Iran, za ta ci gaba da tsayin daka kan al’ummar Palasdinu, na samar wa kansu ‘yanci da kafa gwamnati mai babban birni a Qudus.

Mahukunatan Palasdinawa dai sun yi watsi da tsarin na Trump, wanda suka ce tuni ya shiga kwadon shara na tarihi.


/129