Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Litinin

3 Faburairu 2020

06:11:51
1007369

Palasdinu Ta Yanke Duk Wata Hulda Da Amurka Da Isra’ila

Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abass, ya sanar da yanke duk wata irin hulda ciki har da ta tsaro, a tsakanin mahukuntan Palasdinawa da Amurka da kuma yahudawan mamaya na Isra’ila.

(ABNA24.com) Wannan na a matsayin nuna fishin Palasdinawa a game da yarjejeniyar karnin da shugaba Trump ya gabatar kan rikicin Palasdinawa da Isra’ila.

M. Abbas, ya bayyana hakan ne a birnin Alkahira na kasar Masar, a lokacin da yake halartar taron gaggawa na kungiyar kasashen larabawa, wacce a yayin taron ta yi watsi da yarjejeniyar, tana mai cewa bata tafiya da bukatar al’ummar Palasdinawa.

Saidai duk da hakan wasu kasashen larabawan, sun yi taka tsatsan akan abun suke fada kan yarjejeniyar, a yayin da wasu ke bukatar a sake yin nazari kan ta.




/129