Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Litinin

3 Faburairu 2020

06:11:51
1007368

Yarjejeniyar Karni Babban Laifi Ne Da Amurka Ta Tafka Akan Al’ummar Palasdinu

Jami’i a cikin kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas, Mahmud al_Zahhar, ne ya bayyana haka, sannan ya kara da cewa; Shugaban kasar Amurkan ya kaddamar da wannan yarjejeniyar ne, saboda ya cetar da kansa daga shari’ar da ya ke fuskanta a majalisar dattijan kasar saboda ka da a tsige shi.

(ABNA24.com) Jami’i a cikin kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas, Mahmud al_Zahhar, ne ya bayyana haka, sannan ya kara da cewa; Shugaban kasar Amurkan ya kaddamar da wannan yarjejeniyar ne, saboda ya cetar da kansa daga shari’ar da ya ke fuskanta a majalisar dattijan kasar saboda ka da a tsige shi.

Mahmud al-Zahhar wanda kamfanin dillancin labarun “Irna” na Iran ya yi hira da shi ya ci gaba da cewa; Abin takaici ne cewa da akwai wasu kasashen da su ka halarci wajen zaman kaddamar da wannan yarjejeniyar, da hakan yake a matsayin abin kunya a gare su, wanda kuma za a hukunta su da shi.

Jami’in na kungiyar Hamas,ya kuma yi kira ga al’uumun larabawa da musulmi da su fito fili su bayyana matsayarsu na kin wannan yarjejeniyar.

Har ila yau, al-Zahhar ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wacce ta ke cin karo da ‘yan adamtaka da kuma duk wasu kyawawan halaye. Haka nan kuma ya yi kira da a samar da hadin kai a tsakanin al’ummar Palasdinu domin fuskantar dukkanin ‘yan kanzagin Amurka akan wannan yarjejeniyar.


/129