Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Asabar

1 Faburairu 2020

10:48:27
1006842

Zanga-Zangar ​Al'ummomin Bahrain Da Jordan Sun Yi Watsi Da Shirin Yarjejeniyar Karni

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, dubban mutane ne suka fito a kan manyan tituna a dukkanin biranan Jordan domin nuna rashin amincewarsu da shirin na Amurka da ake kira yarjejeniyar karni.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, dubban mutane ne suka fito a kan manyan tituna a dukkanin biranan Jordan domin nuna rashin amincewarsu da shirin na Amurka da ake kira yarjejeniyar karni.

Masu jerin gwanon sun yi ta rera taken mutuwa ga Amurka mutuwa ga Isra’ila, yarjejeniyar karni yaudara ce da munafunci, haka nan kuma sun yi ta rera taken yin kira ga gwamnatin Jordan da ta kori jakadan Isra’ila da ke a kasar.

Tashar Almanar ma ta bayar da rahoton cewa a kasar Bahrain ma mutane sun gudanar da irin wanann jerin gwanon, inda suke bayyana wannan shiri da cewa yunkuri ne na sayar da falastinu.

Haka nan kuma masu gangamin sun rika rera taken cewa Amurka ce ne babbar shaidan na duniya.

Wannan na zuwa ne adidai lokacin da kasashen an Jordan da kuma Bahrain suke daga cikin kasashen da suka amince da wannan shiri na Trump, wanda al’ummomin larabawa ke kallonsa a matsayin yunkurin wargaza Falastinu a hukumance.


129