Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Alhamis

30 Janairu 2020

05:48:34
1006374

Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Yarjejeniyar Karni Ta Trump Da Abin Kyama

Shugaban kasar ta Iran Dr. Hassan Rauhani wanda ya wallafa sako a shafinsa na Twitter a jiya da dare ya ce; Ya kamata a kawo karshen wannan irin mataki na wauta. Yarjejeniya mafi zama abin kyama, ita ce yarjejeniyar karni.

(ABNA24.com) Shugaban kasar ta Iran Dr. Hassan Rauhani wanda ya wallafa sako a shafinsa na Twitter a jiya da dare ya ce; Ya kamata a kawo karshen wannan irin mataki na wauta. Yarjejeniya mafi zama abin kyama, ita ce yarjejeniyar karni.

Shi ma ministan harkokin wajen Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya wallafa wani sakon a shafinsa na Twitter cewa; Shin Mandela ya tsammaci cewa shekaru bayan ‘yantar da Afirka Ta Kudu, wani tsarin nuna wariyar zai sake bayyana?

Zarif ya kuma kara da cewa; Yarjejeniyar karni ta yi kama da mikakkiyar hanya dodar zuwa jahannama.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma bayyana cewa; Wajibi ne a gare mu musulmi da mu farka, mu fahimci cewa Amurka ba za ta taba zama mai shiga tsakani mai adalci ba.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya kaddamar da shirin da ya kira; Yarjejeniyar karni wacce ta fifita Yahudawa akan Palasdinawa.



/129