Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Alhamis

30 Janairu 2020

05:48:34
1006373

Palasdinawa Sun Tsame Hannuwansu Daga “Yarjejeniyar Oslo

Shugaban gwamnatin kwarya-kwaryar palasdinawa Mahmud Abbas Abu Mazin ne ya bayyana haka a cikin wani sako da ya aike wa Firai Ministan HKI Benjamin Netanyahu.

(ABNA24.com) Shugaban gwamnatin kwarya-kwaryar palasdinawa Mahmud Abbas Abu Mazin ne ya bayyana haka a cikin wani sako da ya aike wa Firai Ministan HKI Benjamin Netanyahu.

Majiyar Palasdinawa ta ambata cewa ministan Palasdinu Husain Sheikh ne ya isar da sakon na Mahmud Abbad zuwa ga Netanyahu ta hannun ministan kudi na HKI, Mushe Kahlun.

Sakon ya kuma kunshi zargin da Mahmud Abbas ya yi wa Netanyahu da take yarjejeniyar ta Oslo.

A gefe daya manzon musamman na shugaban palasdinawa, Nabil Sh’aath ya fadawa tashar talabijin din al-mayadeedn cewa; HKI ba ta aiki ko kadan da yarjejeniyar Oslo, don haka shugaban Palasdinawa ya umarcemu da kalubalantar ta.

Sha’ath ya kara da cewa; Za mu yi duk abinda za mu iya yi domin ganin an sami hadin kai a tsakanin al’ummar Palasdinu.



/129