Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Alhamis

30 Janairu 2020

05:48:34
1006372

Mahmud Abbas Ya Zanta Da Haniyya Ta Wayar Tarho

Shugaban Falastinawa Mahmud Abbas ya zanta da shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya kan shirin Amurka na mu’amalar karni a kan Falastinu.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a zantawar ad ta gudana sakanin bangarorin biyu ta wayar tarho, Isma’ila Haniyya ya tabbatar wa Abu Mazin da cewa, Hamas tana tare da shi kuma tana goyon bayansa a kan matakin da ya dauka na yin watsi da shirin Trump.

Haka nan kuma Haniyya ya sheda wa Mahmud Abbas Abu Mazin cewa, dole ne su ajiye duk wani sabani da ke tsakaninsu, domin su fuskanci wannan shiri da ke rusa Falastinu baki daya.

Shi a nasa bangare Abu Mazin ya tabbatar wa Haniyya da cewa, ya zama wajibi a kan dukkanin bangarori na falastinawa da su dunkule wuri guda domin fuskantar wannan shiri na Amurka da Isra’ila.

A nasa bangaren Khalid Batash daya daga cikin jagororin kungiyar Jihadul Islami ya bayyana cewa, wanda ya goyi bayan shirin Trumpa akn Falastinu, yana matsayin makiyi ne a wurin al’ummar Falastinu baki daya.

Haka nan kuma Khalid Batasha ya yi kira ga Falastinawa mazauna kasashen ketare, da su gudanar da gangami a gaban ofisoshin jakadancin Amurka, domin nuan rashin amincewarsu da wannan shiri.



/129