Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Litinin

27 Janairu 2020

06:51:42
1005819

Palasdinawa Sun yi Barazanar Ficewa Daga Yarjejeniyar Oslo

Kungiyar gwagwamayar yancin Palasdinawa ta PLO, ta yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar Olso, idan har shugaba Trump na Amurka ya yi gaban kansa, game da shirinsa na zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

(ABNA24.com) Kungiyar gwagwamayar yancin Palasdinawa ta PLO, ta yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar Olso, idan har shugaba Trump na Amurka ya yi gaban kansa, game da shirinsa na zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kungiyar Hamas, Ismaïl Haniyeh, ya bayyana cewa shirin sulhun makirci ne Trump ya kullawa Palasdinawa don haka shirin ba zai samu karbuawa ba.

Shugaban kungiyar ta Hamas, ya kuma karayi dukkan sauran kungiyoyin Palasdinawa zuwa halattan wani taron gaggawa a birnin Alkahira na kasar Masar, domin tattauna martanin da zasu mayar kan shirin zaman lafiya na shugabaTrump.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da mahukuntan yahudawan mamaya na Isra’ila suka bayyana shirin na Trump da cewa na tarihi.

A wani lokaci yau Litini ne shugaban na Amurka zai gana da fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kuma abokin hamayarsa Beni Ganz a birnin Washingtong.




/129