Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausa TV
Lahadi

12 Janairu 2020

16:10:25
1001711

Wasu ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun bukaci ganin an kori jakadan Birtaniya daga Iran saboda shiga cikin masu Zanga-zanga da ya yi.

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24-ta nakalto Burujardi wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin tsaro na Majalisa ya ce; Birtaniya tana taka gagarumar rawa wajen aiki da takunkumin da aka kakabawa Iran, kamar kuma yadda take da hannu a cikin matsaloli da dama da al’ummar Iran ke fama da su a wannan lokacin.
Burujardi ya yi kira ga ma’aikatar harkokin wajen Iran da ta sanya korar jakadan na Birtaniya daga Iran a cikin ayyukan da za ta yi.
A daren jiya ne dai jakadan na Birtaniya a Iran, ya karya dokokin kasa da kasa da tsarin aiki diplomasiyya inda ya shiga cikin daliban jami’ar Amir Kabir masu Zanga-zanga.
Birtaniya dai tana da bakin suna a wurin al’ummar Iran gabanin da bayan juyin musulunci a Iran.