Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : VOA
Laraba

14 Faburairu 2018

17:32:45
881964

An Karrama Firdausi Amasa A Taron Ranar Hijabi Ta Duniya A Abuja

An Karrama Firdausi Amasa A Taron Ranar Hijabi Ta Duniya A Abuja

Gamayyar kungiyoyin mata Musulmi ta Abuja ta gudanar da gagarumin taron ranar Hijabi ta Duniya, a inda ta karrama Malama Firdausi Amasa, wadda aka ki bai wa takardar shaidar kammala karatun lauya bayan da ta sanya hijabi a bayan kayan lauya lokacin da aka yi bukin yaye lauyoyi kwanakin baya.

Matan suka ce zasu dauki dukkan matakan da suka dace na kwato wa Firdausi hakkinta, abinda zai kai su gaban wani Kwamiti na Majalisar Wakilan Tarayya.

Malama Rahama Musa Sani, wata jigo a wannan taro, ta shaidawa wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu el-Hikaya, cewa mata da yawa da suka riki addininsu da sosai, su na kyamar yin aiki a wasu wurare kamar hukumomin tsaro na soja, 'yan sanda da wasunsu ganin yadda aka tsani mai sanya Hijabi. Tace haka ma a wasu ma'aikatu na gwamnati.

Malama Rahama, ta koka da cewa yanzu ga wannan batu ya shiga makarantu, har an hana wannan baiwar Allah takardar shaidar kammala karatunta na lauya a saboda kawai ta sanya hijabi dan karami a karkashin kayansu na lauya.

Ta ce sun ziyarci ma'aikatu da hukumomi da yawa domin wayar da kai game da wannan lamari, inda aka ba su tabbacin cewa za a rika mutunta sanya hijabi, har ma hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya ta tabbatar musu da cewa hakkin duk mai son sanyawa ne ya sanya karkashin tsarin mulkin kasa.

Ustaz Abubakar Sadiq na masallacin An-Nur, wanda ya halarci wannan taro na Ranar Hijabi, yace fargabar tsaro ba hujja ce ta hana mata sanya hijabi ko kuma yi musu wani kallo dabam ba.

Yace masu sanyawa, su na yi ne don bin umurnin Mahaliccinsu, don haka ba zasu yarda da duk wani yunkurin take wannan hakkin ba.