Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

2 Mayu 2024

09:16:29
1455664

Ayatullah Ramezani: Hikimar Ahlul Baiti (AS) Ita Ce Mahangar Ɗaukar Nauyi Da Tabbatar Da Adalci A Duniya Baki Daya.

Babban shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya ya ce: Babban aikin da mu mabiya Ahlul-baiti (AS) ke da shi shi ne mu gabatar da addini da dabi'unmu da ayyukanmu da maganganunmu. Ta yadda za a iya cewa wannan mutum ma'abucin addini ne na hakika, wanda aka horar da shi a mazhabar Ahlul Baiti, kuma mumini na hakika.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Reza Ramezani babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (a.s) wanda ya samu gayyata daga musulmin kasar Brazil don halartar taron kasa da kasa na “Musulunci Addinin Tattaunawa Da Rayuwa". ya isa zuwa wannan kasa, a wajen taron gungun musulmin kasar Brazil a Husseiniyar Sayyidina Muhammad Rasulullah (SAW) a birnin Sao Paulo, dangane da samar da wata dama ta zinare ga Musulunci, ya bayyana cewa: a tsawon tarihi makiya sun yi ta kokarin karkatar da addini, amma yanzu an samu dama ta zinare a gare mu na yada addinin ga Musulunci.

Kafin nasarar juyin juya halin Musulunci, masana akidu sun ce babu wani juyin addini da zai faru a duniya. Amma a wannan zamanin, an yi juyin juya hali na addini wanda ya gayyaci al'umma zuwa ga addini da gabatar da addini a fagen zamantakewa. Yanzu mafi mahimmancin cibiyoyin kimiyya na duniya suna sake nazarin addini ne. Addini ba lamari ne da za mu iya yin watsi da shi cikin sauki ba. Addini yana koyar da mutane darussan rayuwa. Alkur'ani mai girma yana magana ne ga dukkan bil'adama wanda ke cewa idan ka saurari maganar Allah da Manzon Allah, za ka kai ga rayuwa ta hakika.

Yanayin Halin Binciken Addini A Zamanin Yanzu 

Babban shugaban Majalisar Duniya ta Ahlul Baiti (AS) ya kara da cewa: A mahangar Ahlul-Baiti (AS) addinin Musulunci addini ne cikakke, madaidaici kuma mai zurfi, kuma wannan addini ba wai kawai ya hada da sallah da azumi ba ne; A maimakon haka, ya kasance a fagen zamantakewa da kuma tsayin daka da mayar da martani ga zaluncin da ake yi a cikin al'umma. Don haka a tsarin Musulunci, idan aka yi zalunci a cikin al’umma, bai kamata musulmi ya ji ba ya da wani nauyi a kan azzalumi ba; 

.«کونا للظّالم خصماً و للمظلوم عوناً

"Ku Zamo Masu Fada Ga azzalumi, Ku Zamo Masu Taimakon Wanda Aka Zalunta." 

Ahlul Baiti (AS) sun ba da ma’anar addini mafi fa’idar inganci. Don gane ingantaccen mai addini, dole ne a dauki matakai biyu; Na farko dole ne mu san addini sannan mu yi imani da shi. Bayan mun san tauhidi da addini mun yi imani da shi, to za mu zama masu addini. Babban aikin da ya rataya kan mu mabiya Ahlul Baiti (AS) shi ne gabatar da addini da dabi’unmu da ayyukanmu da maganganunmu; Ta yadda za a iya cewa wannan mutum mai addini ne na hakika, wanda aka horar da shi a mazhabar Ahlul Baiti, kuma mumini na hakika.

Yayin da yake ishara da sifofin rayuwar addini, Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa: Rayuwar addini ta bambanta da rayuwar da ba ta addini ba. A cikin wata ruwaya Imam Riza (a.s) ya ambaci siffofin rayuwa ta a Addinan ce. Imam Riza (a.s.) ya ce: Mumini ba ya zama mumini sai ya kasance yana da halaye guda uku: wata halin siffa daga Ubangijinsa, da siffa daga Annabinsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa, da siffa daga waliyin Allah. Amma siffar Ubangijinsa ita ce, boye sirri; Kuma siffa ta Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa, ita ce tausasawa da mutane; Kuma siffa ta waliyin Allah ita ce haquri a cikin tsanani.

Musulmi Na Gaskiya Yana Faɗa Da Tsanantawa

A zamanin yau mun ga mutane suna ta karatun ayoyin Alqur'ani suna cewa Allahu Akbar da Laala ila Allah, amma sai suna yakewa mutane kawuna. Ya kamata a lura da cewa wadannan mutane ba ruwansu da addini, kuma su ne suka kirkiro mulkin mallaka da amfani da su wajen haifar da sabani a tsakanin musulmi. Tabbas, sifa ta tsananantawa itace ta dace da su don kawai su alakanta hakan da musulmi. Musulmi na gaskiya ba mai neman Tsanantawa da tashin hankali ba ne, kai ma yana yakar tsanantawa da tashin hankalin ne ma.

Mahangar Shi’a Mahanga Ce Ta Tunani Da Ruhiyya 

Ya yi nuni da cewa: Idan muna so mu kasance tare da waliyin Allah, dole ne mu kasance masu hakuri da lura. Ma’anar Shi’a ita ce mahangar tunani da Ruhiyya. Mahangar Ahlul Baiti (AS) mahanga ce ta daukar nauyi da adalci a duk duniya. Don kada a zalunce kowa, kuma a samu adalci da zaman lafiya ga dukkan al'ummomi, al'ummomi kuma su ci moriyar mulki da girma da daukaka. Imam Khumaini (RA) ya kasance yana cewa na zo ne domin in mayar maku da mutumtakarku da girmanku. Sanin abun ya hau kan mutum yana da matukar muhimmanci a wannan zamani, a wannan zamani da ake kashe mata da yara da tilasta yin gudun hijira. A yau wajibi ne dukkan musulmi da wadanda ba musulmi ba su farka, su isar da kalmar Allah da kalmar addinin Allah ga al'ummar bil'adama. Dole ne mu isar da saƙon zaman lafiya, soyayya da ƙauna ga ɗan adam ga kowa da kowa kuma mu gabatar da bayyana da waɗanda ke da mulkin kama-karya da zalunci ga al'ummar ɗan adam a fili.

..........