Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

1 Mayu 2024

11:30:18
1455505

Ayatullah Ramadani: Addinin Musulunci; Shi Ne Hakikanin Mai Kare Hakkin Mata

Babban magatakardar Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya ce: Allah yana daukaka suto da martabar mata ta yadda Allah ya gabatar da wasu mata a matsayin abin koyi a cikin Alkur'ani.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA - ya kawo maku rahoton cewa Ayatullah Reza Ramezani, babban shugaban majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya, wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil don halartar taro mai taken: "Musulunci Addini Ne Na Tattaunawa Da Rayuwa" ya isa zuwa wannan kasa, kuma a wani taron dimbin mata musulmi daga yankin Latin Amurka cikin jawabinsa yayi nuni da irin halaye na musamman na mata, inda ya ce: Mace tana da karfi na kanta da na gamayyar jam’i, kuma daya daga cikin wadannan karfi na kanta shine batun tarbiyya tausayin da ke cikin mace misali ne na soyayyar Allah, ko da yake son Allah ya fi na uwa girma sau dubbai. Matsayin ilimi da ake baiwa mace a cikin iyali da kuma aikin uwa na ilimi ya yi fice sosai, kuma wadannan al'amura suna komawa ne kan yadda ake baiwa mace kwarin gwiwa. A fagen halayya da tausasawa, ruhin mace na iya girma da yawa. Ta fuskar karfafa zamantakewar mata, za a iya cewa idan aka tattara tarin karfin mata a cikin harkokin zamantakewa, zai zama wani abu mai karfin gaske.

Addinin Musulunci; Shine Mai Hakikanin Mai Kare Hakkin Mata

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya kara da cewa: A karnin da ya gabata, bada kariya na karshe ga mata a yammacin duniya shi ne a fagen kare hakkin mata, kuma har yanzu suna amfani da mata a matsayin makami. Turawan Yamma sun ce mu ne muka kafa ‘yancin dan Adam, wanda tarihin wannan da’awar shekaru dari ne kacal; Alhali Imam Sajjad (a.s.) ya rubuta risala a kan shari’a shekaru dubu dari biyu da hamsin da suka gabata. Akwai maganar Manzon Allah (SAW) da ta Amirul Muminin (a.s) game da mata kuma duk wadannan abubuwan suna daga cikin hakkokin mata a Musulunci. Ya kamata ku gabatar da asalin kariya da Musulunci ya ba mata ga al'ummar yammaci da al'ummar duniya.

Ya kara da cewa: Mata babbar al’umma ce ta zamantakewa, ba shakka, a tarihi, nau’ikan mata sun wuce zamani daban-daban, akwai lokacin da ake gabatar da mata a matsayin halittun da ba a san ko suwa ye ba, har ma ta fuskar al’ada ta kai ga samun ‘ya mace an dauke ta abin kunya! Rashin sanin suna da amfani da kayan aiki sune mafi munin ƙalubale ga mata kuma wannan batu ya kasance sosai a zamanin jahiliyya. A irin wannan lokacin ne Manzon Allah (S.A.W) ya dauki kansa a matsayin mai kare mutuncin mata, kuma ya zamo shi ne mai kare hakkin mata, ta wata ma'ana ya zama wanda aka dorawa nauyin hakan ta hanyar kare hakkin mata, saboda haka. Mushrikai suka gabatar da shi a matsayin abtar mai yankakken tsatso. Har ta kai ga Annabi ya sumbaci hannun diyarsu don kare wannan mutunci kuma ya gabatar da wani sabon salo mai zurfi da inganci na mata.