Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

30 Afirilu 2024

13:17:29
1455251

A taron matasan yankin Latin Amurka, aka gudanar da hakan

Ayatullah Ramezani: Matasa Mabiya Ahlul Baiti (AS) Suna Da Muhimmayar Rawa Da Zasu Taka A Wannan Zamanin Da Muke Ciki.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya: Idan muna son yin wani abu a duniya, dole ne mu ci gaba da ayyuka a kungiyance, domin aikin daidaikun mutane ba ya bayar da wata mafita.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul Baiti (AS) - Abna - Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul Baiti (AS), wanda ya samu gayyatar musulmin Brazil don halartar taron "Musulunci Addinin tattaunawa da rayuwa” aka gudanar kasar, ya fadi hakan a cikin wata tawagar matasa da dama da ke bin mazhabar Ahlul Baiti (AS) a yankin Latin Amurka, inda ya ce: Mu san mene ne babban aikin da ya doru akanmu a matsayin muminai mabiya Ahlul Baiti (AS) a zamanin alfasha da tsiraici. Kasashen Yamma na neman jagorantar jefa al’umma zuwa ga fasikanci da tsiraici da fasadi. Mu kuma bisa fito na fito da hakan, wane nauyi ne muke da shi a kan mabiya addinin mu da sauran matasa? Misali, a fagen jiran Imamuz Zaman As, in sha Allahu, dukkanmu mu kasance daga cikin masu jiran Imam Mahdi (AS), ayyuka guda uku ne a gare mu: aikin farko shi ne ingantawa tare da gina kai, shine mu gina kanmu da karfafa kanmu a ruhiyyarmu da tunaninmu da dabi’unmu, aiki na biyu shine canza wasu; ta yadda zamu iya yin gwargwadon ikonmu wajen gina wasu. aiki na uku shine aza harsashi da share fage ga daukacin al'ummar bil'adama don jin dadin adalci.

Idan muna son yin wani abu a duniya, dole ne mu ci gaba da gudanar yinsa a tare a ƙungiyance domin aikin mutum ɗaya ba shine mafita ba (a wannan fannin). Don haka Imam Zaman (AS) ba zai zo shi kadai ba, har sai sahabbansa sun kammala, to lallai kana zai bayyana ba.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya ci gaba da daukar Iran a matsayin daya daga cikin kasashen da suka ci gaba da ilimin kimiyya inda ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da gogewar shekaru 45 a fagen ilimi, al'adu, siyasa da kuma al'amuran zamantakewa ta kasance a mataki na 57 a duniya, amma yanzu ta kai matsayin daraja ta 16. Iran na daga cikin kasashe 10 da ke kan gaba a duniya a wasu fannonin kimiyya. Ci gaban kimiyyar Iran yana karuwa kowace rana, kuma yana yiwuwa a kai wadannan ci gaban ga matasan kasashen Latin Amurka. Za su iya zuwa Iran su yi karatu a fannoni daban-daban da suka hada da likitanci da injiniyanci.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da wasu matsalolin da matasan wannan yanki suka gabatar, Ayatullah Ramezani ya ce: A gaskiya ba mu saba da rayuwar Ahlulbaiti (AS) ta ilimi da aikace-aikace a fannonin iyali da zamantakewar al'umma da al'adu da siyasa ba. Yakamata a san salon rayuwar Ahlul Baiti (AS) kuma wannan salo shine kadai mafita mai ceto. A cikin bayanin mataki na biyu na juyin juya halin Musulunci Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar da shawarwari da wasiya guda bakwai wadanda idan har al'umma tana son ci gaba to sai ta bi wadannan shawarwari guda bakwai. Shawara ta farko ita ce ci gaban kimiyya, shawara ta biyu ita ce Halayya da Ruhi; Shawara ta uku neman a fagen adalci, Yaki da fasadi kuma ita ce shawara ta hudu sannan kuma a shawara ta bakwai a cikin bayanin mataki na biyu shi ne salon rayuwar Musulunci, wanda shi ne manhaja na wayewar Musulunci.

Ya kara da cewa: Dole ne matasa su shigo fagen kuma niyya mai karfi na da matukar muhimmanci. Shahid Qassem Suleimani ya kasance yana cewa dole ya zamo kun kasance cikin fage. Addini shine sigar ceton dan Adam kuma dole ne mu koma ga addini da hakikaninsa. Al'amura suna farawa ne ako da yaushe da kadan-kadan Manzon Allah (S.A.W) ya fara sallar jam'i a Makkah da mutane uku yayin da mushrikai suke zuba tunbin rakumi a kan Manzon Allah (SAW), amma a yau mutum nawa ne ke halartar sallar jam'i a duniya. ? Ikhlasi yana da matukar muhimmanci kuma idan muka fara aiki daidai, Allah zai taimake mu, kuma Allah Ya nuna mana ikonsa a fagen matsaloli. Misalin wannan shi ne labarin Annabi Musa da sojojin Fir'auna suka bi Annabi Musa da mabiyansa har suka isa kogin Nilu, ya zamo a nan gaban Annabi Musa da mabiyansa akwai teku, a bayansu kuma akwai sojojin Fir'auna. Mabiya Annabi Musa suka ce: Tamu ta kare; 

«فَلَمَّا تَراءَا الْجَمْعانِ قالَ أَصْحابُ مُوسى‌ إِنَّا لَمُدْرَكُونَ»

Amma sai Annabi Musa As Yace da su." Ba haka ba ne lalle Allah na yana tare da ni kuma shi zai shiryar da ni.

 «قَالَ كَلَّا إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهْدِينِ»

Babban sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya bayyana cewa: Tattaunawa kamar irinsu karancin kasafin kudi tattaunawa ce ta gefe, kuma mutanen da ke da karancin kasafin kudi sun yi ayyuka masu kyau. Wasu kuma suna da kasafin kuɗi da yawa, amma ba za su iya yin komai ba. Muna buƙatar gano hanyoyin da za mu iya yin aiki a fagen matasa a ƙasashen Latin Amurka. Ɗaya daga cikin hanyoyin ita ce amfani da ƙarfin sararin samaniya da cibiyoyin sadarwar jama'a. A yau, kasa mafi girma a duniya ita ce kasar da ke da sararin samaniya, inda kashi 63.2% na mutanen duniya, watau mutane biliyan biyar, suke a wannan sararin samaniya, kuma mafi girman kaso na samuwa a sararin samaniya na Amurka ne. Dole ne mu yi amfani da wannan sarari da dandamali.

..................