Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

30 Afirilu 2024

11:46:14
1455235

Majalisar Dokokin Amurka: Za Mu Mayar Da Martani Mai Tsauri Kan Hukuncin Da Ake Yankewa AKan "Isra'ila".

Majalisar Dokokin Amurka Ta Yi Wa Kotun Hague Barazana: Za Mu Mayar Da Martani Mai Tsauri Kan Hukuncin Da Aka Yanke Kan "Isra'ila".

Wakilan majalisar dokokin Amurka sun yi wa kotun Hague barazanar cewa "idan ta bayar da sammacin kama wasu manyan jami'an Isra'ila, to za ta fuskanci martanin Amurka, kuma ana daukar matakan shari'a a kan haka."

"Mike Johnson", Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, ya fitar da wata sanarwa tare da rubutawa a cikinta cewa: "Idan gwamnatin Biden ba ta nuna adawa ba, kotun hukunta manyan laifuka ta Hague za ta iya samun iko da ba a taba yin irinsa ba tare da bayar da sammacin kama 'yan siyasar Amurka, jami'an diflomasiyya da kuma soji."

"Johnson" ya roki gwamnatin Biden da cewa: "nan da nan ta nemi kotu da ta daina bayar da sammacin kama jami'an Isra'ila da kuma yin amfani da duk wata hanya da ake da ita don hana irin wannan abin kyama."