Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

30 Afirilu 2024

08:01:08
1455204

An Kashe Mutane Bakwai Tare Da Jikkata Wasu Da Dama A Wani Harin Ta'addanci Da Aka Kai A Wani Masallacin 'Yan Shi'a A Birnin Herat Afganistan +(Hotuna)

Kafofin yada labaran kasar Afganistan sun bayar da rahoton cewa, a lokacin sallar magariba da Isha’i 'yan ta'addar takfiriyya sun kai hari a masallacin Imam Sahib Al-Zaman da ke yankin Andishiya na lardin Herat a yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA - ya kawo maku rahoton cewa: akalla mutane 7 da suka hada da yaro guda ne suka yi shahada, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin ta'addanci da 'Yan takfiriyya suka kaddamar a wani masallacin 'yan Shi'a da ke lardin Herat a yammacin Afganistan.

Shahadar Limamin masallacin Sheikh Jawid

Kafofin yada labaran kasar Afghanistan sun bayar da rahoton cewa, a lokacin sallar magariba da Insha’i, 'yan ta'addar takfiriyya sun kai hari a masallacin Imam Sahib al-Zaman da ke yankin Andishiya na lardin Herat da ke yammacin kasar.

Kafafen yada labaran kasar Afganistan sun bayyana cewa, harin ta'addancin ya yi sanadiyar mutuwar wasu masallata bakwai da suka hada da yaro daya da limamin masallacin, Sheikh Jawid, yayin da wasu masallata kusan biyar suka samu raunuka, inda suka kara da cewa 'yan ta'addan sun gudu bayan sun aikata munanan laifukan da suka aikata.

Har yanzu jami'ai a ma'aikatar harkokin cikin gida ta Taliban ba su bayar da cikakken bayani kan wannan harin ta'addanci ba

Muguwar kungiyar ta'addanci ta ISIS Khorasan ta kan dauki alhakin kai hare-haren ta'addanci a Afganistan, kuma wannan ta'addancin kungiyar ta kara yawan kai hare-haren ta'addanci tun bayan janyewar sojojin Amurka da na kasashen waje daga kasar bayan da kungiyar Taliban ta kwace mulki a ranar 20 ga watan Agustan 2021.

 

................................