Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

29 Afirilu 2024

08:30:45
1454947

A Ci Gaba Da Gudanar Da Taron Masana Da Jagororin Cibiyoyin Addini Na Latin Amurka

Ayatullah Ramezani: Makiya Suna Son Share Shari'ar Musulunci

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya ce: Idan Musulunci bai kasance a cikin fagen zamantakewa da siyasa ba, babu abin da zai saura a cikinsa. Makiya suna son rufe shari'ar Musulunci ne, Wannan muhimmin batu ne da ya kamata mu mai da hankali a kai.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku bayanin shugaban majalisar Ahlul-Bait AS ta duniya a cikin taron da ya gudana a kasar Brazil Ayatullah Reza Ramezani babban sakataren majalisar dinkin duniya na Ahlul-Baiti (A.S) wanda musulmin kasar Brazil suka gayyace shi don halartar taron kasa da kasa mai taken "Musulunci Addinin Ne Na Tattaunawa Da Rayuwa” wanda samu damar yi wannan tafiya zuwa kasar, a gefen wannan taro, a wajen taron malamai da jagororin cibiyoyin addini na Latin Amurka, yayi bayani dangane da matsayin mazhabar Ahlul Baiti (a.s) inda ya ce: Alhamdulillah Allah ya sananar da mu mazhabar Ahlul baiti (a.s). Muna fuskantar gagarumin lamari a lokacin da Musulunci ya bayyana a fagen zamantakewa da siyasa. Babu wanda ya yi tunanin hakan zai faru. Tare da juyin juya halin Musulunci a Iran, an samar da wata dama ta zinari ga kowa da kowa.


Farfagandar Kasashen Yamma Akan Mazhabar Ahlul Baiti

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya kara da cewa: A yau Turawan Yamma suna rike da katafariyar kafafen yada labarai, kuma suna kokarin bayyana mabiya mazhabar Ahlul-baiti (AS) a matsayin masu neman tashin hankali, yayin da Mazhabar Ahlul Baiti (AS) ta zamo makaranta ce ta tausasawa da kyautatawa. Duk abin da suke magana akan shi fa ne, ba komai bane sai domin mabiya mazhabar Ahlul Baiti (a.s) sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar zalunci, saboda hakane suke jinginawa ‘yan Shi’a wannan.

A yayin da yake ishara da yunkurin karkatar da Musulunci, Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa: A yau muna fuskantar wani nau'i na gurbacewar Musulunci. A da makiya sun nemi gurbata Musulunci ta hanyar kawar da Musulunci gaba daya daga fagen zamantakewa da siyasa, amma a yanzu Turawan Yamma suna neman bullo da Musulunci mai sassaucin ra'ayi.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya yi la'akari da muhimmin aikin masu tabligin addini suke da shi na gabatar da sanarwar duniya yadda hakikanin mazhabar Ahlul Baiti (a.s.) ta ke. Ya kuma yi karin haske da cewa: Abun ba wai kawai daga karanta wasu kwarorin hadisai daga Imamai Ma'asumai (As) ne ba za mu iya fahimtar maganarsu cikin sauki ba a'a. Imam Amirul Muminina (AS) yana cewa a cikin ruwaya: “Al’amarinmu (Imamancinmu) ya na da tsanani sosai; Kuma babu wanda zai iya (kamar yadda ya kamata) har yayi furuci da shi; Sai dai mala'ika makusanci, ko annabi da aka aiko, ko bawa wanda Allah ya tsarkake zuciyarsa da imani.

Ayatullah Ramezani ya kara da cewa: Muna son mu gaya wa mutane yadda musuluncin Ahlul-Baiti As ya ke. Dole mu sanar da matasa da mazhabar Ahlul Baiti.

Mu'amalar Mabiya Ahlul Baiti (a.s) Ita Ce Sanar Da Mazhaba Da Kuma Ahlul Baiti (a.s).

Ya kara da cewa: Imam Musa Sadr yayi wata kyakkyawar magana. Ya kasance yana cewa idan muna son gabatar da Amirul Muminin (AS) ga wadanda ba musulmi ba, ba zai yiwu ta hanyar karanta tarihi ko nakalto ayoyin Alqur'ani ba, domin ba su yi imani da Alkur'ani ba. A yau ta wannan hanyar ne kadai za mu iya gabatar da Imam Ali (a.s.) ga wadanda ba musulmi ba ta hanyar zamowa wakilan maganganu da ayyukan Imam Ali (a.s.) a cikin halayenmu. Imam Amirul Muminin (a.s) ya ce a cikin Nahjul Balaghah: 

امیرالمومنین(ع): «وَ لکِن اَعینونی بِوَرَعٍ وَ اجتِهادٍ وَ عِفَّةٍ وَ سُدادٍ»

"Kuma sai dai ku taimakeni da tsantsar da kai (takawa) himma da ijtihadi da kamewa da dakewa (bin tafarki madaidaici". 

Idan aka gabatar da Imam Ali (AS) da kyau, duniya za ta so shi. Idan muka gabatar da Imam Ali (AS) daidai yadda ya kamata me zai faru a duniya? Abunda zai faru shi ne: Ba za a ƙara yin zalunci ba, za a raba dukiya bisa adalci, ba za a yi talauci ba, abubuwa da yawa za su faru na ci gaba.