Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

28 Afirilu 2024

08:21:32
1454674

Ayatullah Ramezani: Imamai Ma’asumai (A.S) Su Ne Jagororin Tattaunawa Da Musayar Ra'ayi

Ayatullah Ramezani: Imamai Ma'asumai (A.S) Sun Kasance Jagororin Tattaunawa / Yadda Musulmi Suke Ji Na Nauyin Da Ya Doru Akansu Game Da Dukkan Bil'adama. ya fadi hakane a A taron kasa da kasa “Musulunci Addini Ne Ta Tattaunawa Da Rayuwa"

Babban shugaban majalisar Ahlul Baiti (a.s) ta duniya ya dauki Imamai (a.s) a matsayin jagororin tattaunawa kuma ya bayyana cewa: Limamanmu da jagororin addininmu kamar Imam Sadik (a.s.) da Imam Rida (a.s.) suna tattaunawa tare da kowa da kowa ciki har da Kiristoci da Zoroastrians kuma suna yin Magana da su.


Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA - ya kawo maku rahoton cewa: An gudanar da taron kasa da kasa na Musulunci Addini Ne Ta Tattaunawa Da Rayuwa" a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, tare da halartar Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalissar Ahlul-Baiti ta duniya a matsayin babban bako, da wasu manyan shugabannin addinai da na kimiya daga Kudancin Amurka.

Imamai Ma’asumai (A.S) Su Ne Jagororin Tattaunawa Da Musayar Ra'ayi

Ayatullah Ramezani babban shugaban majalisar Ahlul Baiti (a.s) ta duniya a jawabin da ya gabatar a wajen wannan taro, yayin da yake ishara da muhimmancin ilimi a mahangar Shi'a ya bayyana cewa: Ilimi shi ne ginshikin dukkan alheri, alhali kuma jahilci shi ne tushe na dukan sharri. Imam Amirul Muminin Ali (a.s.) a cikin ruwaya yana cewa: "Duk wanda ya san kansa ya kasance yafi sanin waninsa, wanda kuma ya jahilci, kansa ya kasance yafi jahiltar waninsa";

«مَنْ عَرَفَ نَفْسَهُ كانَ لِغَيْرِهِ أَعْرَفَ وَ مَنْ جَهِلَ نَفْسَهُ كانَ بِغَيْرِهِ أَجْهَلَ «

Idan mutum ya san kansa daidai da kyau, zai kuma san sauran mutane daidai da kyau. Dukkanmu an umarce mu da sanin kanmu, "Kasan Kanka / Kasan kai Waye". Aristotle ya rubuta a cikin littafinsa ​​cewa: Ku san kanku, sanin kai shine mabuɗin ci gaban ɗan adam kuma yana sa mutum ya ji daɗin dukan mutane.

Ya ci gaba da cewa: Imam Amirul Muminin Ali (AS) yana da fitattun siffofi, daya daga cikinsu shi ne “Adalci”. Ina ba da shawarar cewa a fassara littafi mai suna "Sautul Adalah / صوت العدالة " wanda "George Jardaq", shahararren marubucin Kiristanci na Labanon ya rubuta, a fassara shi cikin yaren Espanya da Fotigal. George Jardaq shi ya kasance masoyi mai kaunar Amirul Muminin (AS). Sayyidina Ali Amirul Muminin (AS) yana wani furucin Magana da ke cewa: : Mutane gungu guda biyu ne, Gungu daya na iya zama ‘yan’uwan juna a addini, dayan gungun kuma su zamo suna kama a cikin halitta.

Ayatullah Ramezani ya ci gaba da daukar limamai ma’asumai  (a.s) a matsayin jagororin tattaunawa kuma ya bayyana cewa: Limamanmu da malamanmu kamar Imam Sadik (a.s.) da Imam Riza (a.s) sun kasance suna tattaunawa da kowa da kowa, ciki har da Kirista da Zoroastrian. Ya kamata mu yi magana da juna mu fahimta da mutunta juna. Musulunci ya inganta rayuwa ta lumana. Ya kamata mutane su kasance tare. Musulunci ya ba da shawarar ci gaban sadarwa mu’amala; mu’amalan nan kuwa ta hada alaka da kai, alaka tare da wasu, alaka tare da Allah, alaka tare da yanayi.

Bugu da ari, ya yi la’akari da aikin annabawan Allah na fitar da ‘yan Adam daga rayuwa ta zahiri da ta badini kuma inda ya kara da cewa: Ba a halicce mu don wannan duniya kawai ba, domin dukanmu za mu bar duniya wata rana. Barin duniyar nan ba ya na nufin karewa da halakar gaba daya bane, sai dai yana nufin rayuwa a cikin wata duniya mai faɗi da tafi wannan, Dole ne mu ji mu daukin nauyin alhakin junanmu.