Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Asabar

19 Oktoba 2019

11:59:10
988150

Dakarun Hashd Al-Sha'abi Dubu Uku Ne Suke Aikin Tabbatar Da Tsaro A Taron 40

Kimanin dakarun sa kai na Hashd Al-sha’abi dubu uku ne suka shiga shirin bayar da tsaro ga masu ziyarar arbaeen na Imam Husain (a.s) a Karbala.

(ABNA24.com) Kimanin dakarun sa kai na Hashd Al-sha’abi dubu uku ne suka shiga shirin bayar da tsaro ga masu ziyarar arbaeen na Imam Husain (a.s) a Karbala.

Tashar talabijin din Al-alam dake watsa shirye-shiryenta daga birnin Tehran ta ruwaito kafar watsa labaran Hashd Al-sha’abi cikin wani bayani da ta fitar a jiya lahadi, na cewa kimanin dakaru dubu uku ne na kungiyar suke aiki tare da dakarun tsaron Iraki wajen bayar da tsaro ga masu ziyarar ranakun Arba'in kama daga kan iyakokin kasar zuwa ga shingayen da aka kafa na bincike da kuma bayar da tsaro da kuma yin hidima ga maziyartan.

Maisam Al-zaidy daya daga cikin kwamandojin rundunar tsaron kasar Iraki ya ce a shekarar da ta gabata kimanin masu ziyara dubu dari ne suka yiwa hidima da kan iyakar Zurbatiyah , amma a shekarar bana da taimakon kungiyar Hashd Al-sha’abi suna sa ran masu ziyara dubu 250 zuwa dubu 400 ne za su bawa hidima a wannan iyaka.

Ana hasashen cewa sama da mutane miliyan 15 ne za su halarci taron 40 na wannan shekara.



/129