Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

21 Oktoba 2019

09:03:48
983808

​Ruhani Ya Yaba Wa Gwamnatin Iraki Kan Kyakkyawan Daukar Bakoncin Masu Ziyarar Arbaeen

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya yabawa shuwagabanin kasar Iraqi dangane da gudanar da da kyakkywan shiri na daukar bakuncin masu ziyarar ziyarar arba’in na Imam Husain (a) a kasar.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya yabawa shuwagabanin kasar Iraqi dangane da gudanar da da kyakkywan shiri na daukar bakuncin masu ziyarar ziyarar arba’in na Imam Husain (a) a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Iran Press ya nakalto shugaban yana fadar haka a ciki wasikun da ya rubuta wa shugaban kasar ta Iraqi Barham Saleh da kuma Firai Ministan kasar Adil Abdul Mahdi.

Shugaban ya bayyana cewa ziyarar arba’in ta wannan shekara, wadda miliyoyin mutane daga kasar Iran da wasu kasashen duniya suka halarta, wani sako ne na ‘yanci ga kasashen duniya.

Har’ila yau shugaban ya kara da cewa ziyarar ta 40 ta kara fito da hadin kai da ke tsakanin mutanen kasashen Iraqi da Iran, sannan ta hada kan mutanen duniya don fuskantar azzaluman kasashen duniya.

A jiya Asabar ce miliyoyin mutane daga kasashen duniya da dama suka harlarci juyayin 40 na shahadar Imam Husain (a) jikan manzon Allah (S) da wasu iyalan gidansa da sahabbansa, fiye da karni 14 da suka gabata, wato a shekara ta 61 bayan hijira a Karbala da ke kasar Iraqi.

..........
340