Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Alhamis

17 Oktoba 2019

05:36:35
983165

​Iraki: An Bankado Wani Shirin Kai Harin Ta’addanci A kan Masu Ziyarar Arbaeen

Jami’an tsaron kasar Iraki sun bankado wani shirin kai harin ta’addanci a kan masu ziyarar arbaeen.

(ABNA24.com) Jami’an tsaron kasar Iraki sun bankado wani shirin kai harin ta’addanci a kan masu ziyarar arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran saumaria News ya bayar da rahoton cewa, a jiya Jami’an tsaron kasar Iraki sun bankado wani shirin kai harin ta’addanci a kan masu ziyarar arbaeen a yankin Biji a kan hanyarsu ta zuwa Karbala.

Bayanin ya ce an kame mutane 10 wadanda dukkaninsu ‘yan ta’addan Daesh ne dauke da bama-bamai a cikin sahun masu tafiya ziyarar arbaeen, kuma wasu daga cikinsu manya ne a cikin kungiyar, inda suke da nufin aiwatar da wani mummunan kisa a kan masu ziyarar.

Baya ga haka kuma an kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan bayan da asirinsu ya tuno a lokacin da suke shirin tayar da jigidar bama-bamai a tsakiyar masu tafiya ziyarar arbaeen acikin lardin Salahuddin da ke arewacin Iraki.

Jami’an tsaron kasar Iraki sun ce sun kammala dukkanin shirinsu domin bayar da tsaro ga masu ziyarar, a kan dukkanin hanyoyin da suke isa zuwa birnin Karbala.




/129