Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : tsk
Lahadi

22 Afirilu 2018

16:09:00
890431

Me Yasa Makiya AhlulBaiti Suke Jifan Imam Shafi’I, Hakeem, Da Sauran Masu Ra’ayinsu Da Shi’anci?

Me Yasa Makiya AhlulBaiti Suke Jifan Imam Shafi’I, Hakeem, Da Sauran Masu Ra’ayinsu Da Shi’anci?

Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara a lokacin da yake gabatar da karatun littafin Muqaddimatul Azeefa na ranar Juma’a, 20/4/2018, ya bijiro da tambaya yana cewa me yasa makiya AhlulBait suke jifan manya malamai magabata irinsu Imam Shafi’I da Hakeem da sauransu da Shi’anci?
Sai Shehin malamin ya amsa wannan tambayar da cewa:
 “ Saboda iyaka dai suna fifita Ali kan Usman, ko kuma su yi wata Magana ko juya baya ga wanda ya yaki Ali. Juya baya ga wanda ya yaki Ali. Kun ga ya sakaye? Saboda baya son ya fito da zance karara a gane ma’alan Shi’ancin nan shine fadar abinda Annabi ya fada akan Mu’awiyyah, sai ya boye sunan sai ya fadi sifar, wato wanda ya yaki Ali. To iyakar gayan Shi’ancinsu Kenan.
 “ Kun ga ashe magana ta fito, ma’anar Shi’anci gunsu fadar wayannan maganganu da Annabi ya fada kan Mu’awiyyah. Ga shi karara Ibn Taimiyyah ya hutar da kai. In dai zaka gaskata Annabi kan wannan dan Shia sunanka. A nan ya bayyana karara makiya AhlulBaiti a gunsu ma’anar Shianci.”
Shehiin Malamin ya kara da cewa su makiya AhlulBaiti ba suna fassara shianci bane da kiyayya da Abubakar da Umar;
 “ Shi’anci a gunsu ba ma’anarshi kin Sayyidina Abubakar da Umar bane, kai ba ma ma’anarsa fifata Imami kan su ba. Kana sonsu ka fifita shi kansu ba. In sun ce Shi’anci suna nufin juyawa tawagar azzaluman da suka yaki Imami bisa zalunci da ta’addanci. In ka ki yarda da wannan da waliyyartakarsu da yardar Allah gare su cewa ‘yan Aljanna ne, Shuwagabanni ne na Kuraish zuwa karshe, to, kai dan Shi’a ne. To, shi kuma mai ce masu azzalumai ka karyata shi sannan ka zama Ahlus Sunnah. Ka karyata mai Sunnah ka zama Ahlus Sunnah. Yace masu Azzalumai kace masu Mujtahidai, Yace masu ‘yan Wuta kace masu ‘yan Aljanna, Ya la’ance su kace masu Radiyallahu Anhum, Yace wanda ya bi su wuta zai tsinci kansa suka ce wanda ya bi su shine dan Sunnah dan Aljanna. To, wannan shine ma’anar Shi’anici a gunsu da Sunnanci. To, zamu yarda da wannan Sunnanci? Karyata Manzon Allah ya zama shine Sunnanci? Duk bala’in da za a yi ayi ba zamu karyata Manzon Allah ba.
 “ Wadannan da ake su ka ga girmansu da biyayya gare su shi kuma Annabi yace ka kadure cewa Azzalumai ne makira ya zuwa ga wutan Jahannama. Inda zaku rika gasgata ni Shi’anci a gurinsu shine juyawa Mu’awiyyah da bayyana jibantar Imamul Mu’uminina- Ai mun karanta maganar Yahaya Ibn Mu’in a manyan jiyan ma wayanda aka sa sahun manya. Me Yahaya Ibn Mu’in ya fada kan Imam Shafi’I? Yace Imam Shafi’I dan  Shi’a ne. Ahmad dan Hambali da ya tambayi shi Yahaya Ibn Mu’in meye hujjarka na cewa Shafi’I dan Shi’a ne? Sai yace saboda na duba littafinsa gaba daya da Ali ya kafa hujja. Kafa hujja da Ali shi kadai baka raba da wani ba a Sahabbai shima Shi’anci ne, kuma a gun Yahaya Ibn Mu’in. Kun ga irin kwamacalar da take cikin Jarh da Ta’adili. Yanzu ya kamata Ibn Mu’in a saki da Jarhinsa da Ta’adilinsa mudlaqan? Gashi yanda ya so yayi ta’addanci kan Imamu Shafi’I da hujja ta zalunci.