Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : tsk
Lahadi

15 Afirilu 2018

11:31:14
889447

IN KACE DAN SHI’A BA MUSULMI BANE KAI DAN SUNNAH WA YA TABBATAR MA DA MUSULUNCI?

IN KACE DAN SHI’A BA MUSULMI BANE KAI DAN SUNNAH WA YA TABBATAR MA DA MUSULUNCI? In ji Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

A karatun Muqaddimatul Azeefah ta ranar Juma’a, 13/4/2018, Sheikh Abduljabbar ya bayyana cewa in ka ce dan Shi’a ba musulmi bane, kai dan Sunnah wa ya tabbatar maka da musulunci?
Malamin ya ce:
 “ Ko kafiri an yarda ka zalunce shi bare dan Shi’a musulmi? In ka ce dan shi’a ba musulmi bane, kai dan Sunnah wa ya tabbatar ma da musulunci? Ka wo min aya da tace dan Sunnah musulmi ne, kawo ta. Amma akwai “ WA INNA MIN SHI’ATIHI LA IBRAHIM”, daga ‘yan shia’arsa akwai Ibrahim amma ba MIN SUNNATIHI LA IBRAHIMA. Ko akwai ayar? Saidai SUNNATALLAHI LILLAZINA KALAU MIN QABLU WA LAN TAJIDA LI SUNNATALLAHI TABDILA. Kuma du ba ka gani meye SUNNATALLAHI LILLAZINA KALAU…? Fata fata Allah yayi dasu. DAMMARNAHUM, haka Allah yace, Mun bace su mun dammara su, haka yace. Sunnar Allah kenan cikin wa’yanda suka wuce, ba zamu sauya ta ba cikin masu zuwa. Ashe ma da hatsari a sunan.
Malamin ya bayyana cewa kowaye ya saba da koyarwar Annabi basa tare shi, kuma suna girmama shehunnan darika ne matukar sun dace da gaskiya.
 “ Don haka ku daina, ku zama tare da Manzon Allah kawai. Ko darika ta barku ko darika ta juya maku baya, ko su hadu da izala ko su rabu su ta shafa. Mu muna darika ne dan Allah. Kuma duk abinda ya saba da Manzon Allah bama tare da wannan abu. Ba ma tare da wannan abu ko meye shi, darika ce ko waninta. Su kansu shehunnan muna binsu ne saboda bin da suke ma Annabi. Da basu kyautata biyayya ga Annabi ba, wallahi ba zamu bisu ba. Akwai me cewa yana bin Shehu ko me zai faru ya faru. Mu wallahi bama bin  Shehu ko me zai faru ya faru, sai mun ga alheri zai faru zamu bi Shehu. In mun ga tsiya zamu bar Shehu mu rabu da shi. Muna bin Shehu ne don mu tsira, in muka ga zamu halaka zamu barshi.”
A lokacin da malamin yake bambamtawa tsakanin ‘shi’a’ da ‘rafdu’ sai yace:
“ Abinda ake ta’arifin Tashayyu’I shine jibintar lamarin Imami da fifita shi kan waninsa a cikin dukkan Sahabbai. Wannan shine ta’arifi na gaskiya. Jibintarsa da fifita shi. Shi ko “Rafdu” shine gaba da kalifofin nan uku. Ko kuma ku kara sauran kalifofin da Annabi ya wanke ya tabbatar da nagartarsu a ingantacciyyar riwaya ba a riwayar son rai ba. Gaba da su da kinsu da juya masu baya, wannan shine ‘rafdu’.”
Malamin yace cewa da ‘yan shi’a suke yi wai Imami (Sayyidina Ali) ya fi dukkan Annabawa kuskure ne, kuma bah aka bane.
 “ A gaskiyar Magana ma bai fi Annabi ko daya ba, ba dukkansu ba. Autan Annabawa gaba yake da shi, in dai Annabi ne, Autansu gaba yake dashi. Na’am, wurin da  Manzon Allah yake fada ‘duk wanda nake uban gidansa, Ali ubangidansa ne, a wannan al’ummar yake nufi. Na’am, muna tare da wannan tunani, domin shine tunanin da Annabi ya karfafa. A cikin wannan al’ummar kakaf wanda duk ba Annabi (saw) Sayyidina Ali na gaba da shi. Na’am, wannan bai hana sabani ba, ra’ayinmu kenan. Duk wani lokacin muna shiga tababan tsakanin Shi da Tsohon nasa wa yafi wani kuma? In ka kalli wasu abubuwan sai ka ga Imamun mu ya fi tsohon nasa, Sayyidina Abu Talib. In kuma kallo wasu abubuwan sai ka ga Tsohon nasa ya fi shi.
 “ Sannan tababa ta biyu wadda har yau ni dai ban gushe ba a cikinta ba, shine; a cikin wannan al’ummar ta Annabi a samu wanda ya fi Sayyidina Abdullahi Tsohon Annabi? Waqi’I da hakika suna nuna maka ba za a samu ba. In kuma kalli wasu dalilan sai ka ga kamar a samu. Kun ga kofar tana nan a bude. Saidai a gaskiyar Magana shine fifita shi don kyautata ladabi ga Manzon Allah(saw). Haka zalika mahaifiyar Manzon Allah (saw), in ka kalla ta ya za a samu wani a wannan al’ummar ya kai ga ita balle ya fi ta? To, wayannan kadai sune. Kuma in kun tashi kalla sai ku ga ai wayannan gaba daya da su da Imami abu daya ne kuma. Ai abu daya ne ba zai rabu ba. Da Sayyidana Abu Talib da Sayyidina Abdullah da Nana Aminatu a gun Annabi abu daya ne. Haka Sayyidana Ali da wayannan abu daya ne. Nana Amina, Nana Khadija, da Nana Fatima abu daya ne. Sannan kuma duk wand aka fifita din ma sauran ka fifita, domin dukkansu abu daya ne, tsoka daya ce da ba zata rabu ba. “