Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : tsk
Lahadi

18 Maris 2018

12:45:44
886139

DUK WANDA ANNABI YACE DA SHI MUNAFUKI NE MU A WAJENMU MUNAFUKI NE In ji Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

A karatun littafin Muqaddimatul Azeefa na ranar Juma’a, 16/3/2018, wanda Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya gabatar a Masallacin Jami’u Amiril Jaishi dake Kano. Malamin ya bayyana cewa duk wanda yace shi munafuki ne mu a wajenmu munafuki ne. Shehin malamin ya ce:

 “ A gun mu duk wanda Annabi ya ce da shi munafuki ne mu a wajenmu munafuki ne, ko kuma yace shi ‘ashqan nasi’ ne, ba yanda za a yi mu ce makashin Ammaru thiqa ne, ko mu ce ‘radiyallahu anhu’, ko mu ce ‘min man shahidallahu lahu…., bayan Manzon Allah (sawa) ya ce masa ‘fin nar’. Ba bu hali. Ka tsaya da wadancan din, mu mun tsaya da Manzon Allah(saw). Muna tsaye a in da ya (Annabi) ya tsaya, ku je da wadancan.”
Malamin yace tsarin mulkin kasar nan ya ba da ‘yanci har ga marasa addini da su bauta ma abinda suka ga dama balle wanda kuma yake da addini illa kawai yana da ra’ayi ne.
 “ (Annabi) Ya bada hukunci kan wadancan mutanen, muna nan tare dashi (a wannan hukuncin). Wanda zai mara masu bamu hana shi ba yana da ‘yanci amma ka da ya tilasta mu sai mun masa nasa. Kowa yayi ra’ayinsa. Kasar nan da ta ce in baka yarda da addini kana da ‘yanci ka rayu ma, rashin addinin daddai ne, bare kana addini illa ra’ayi ne da kai a cikin addinin” A cewar malamin.
Malamin ya kara da cewa:
 “ Wannan shine addininmu, duk wanda Annabi ya soka ko waye duk girmansa zamu soke shi, ko duk sunnah ta hadu karkashinsa. Annabi ya soke shi, ta tabbata ya sokar zamu soke shi, ba ruwanmu. Wannan shine tsarin addininmu, ba mu hana wani yayi nasa ba. Abin da dokar kasa tace bata yarda dashi ba kace sai mutum yayi dole abinda kake yi ko kace baka yarda yayi nashi ba. Ba wanda muka ce sai yayi akidar nan.”
Malamin ya tabbatar da cewa ‘yan salafiyyah har Annabi suna jifa da shi’anci da rafdu a lokacin da ya dauki wata matsaya kan wasu gwarazansu domin suna mutane sauraron Annabi.
 “ Har Annabi suna kira da Rafidiy ba wai Abduljabbar ba cikon gari a numba. Annabi (sawa). A tsarin Salafiyyah suna ce masa dan shi’a idan suka ga yana dafa wa Imamu Ali. Suna ce masa dan shi’a, a guje shi zai halaka mutane…”