Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Taskar Alkhairi Naija
Litinin

28 Agusta 2017

16:40:00
851011

A DUNIYAR SHI’A BABU WANI LITTAFI WANDA YAKE INGANTACCE DARI BISA DARI Inji Sheikh Bashir Lawal Kano kashi na uku

A cigaba da raddin littafin “lillahi thumma lit tarith” wanda Sheikh Bashir Lawal yake karantawa a cikin littafin “lillahi wa lil haqiqah” a Husainiyyar Hauzar Baqirul Ulum dake Dambare Kano, ,ya bayyana cewa a duniyar Shi’a babu wani littafi wanda yake ingantacce dari bisa dari.Yana cewa

“Mu a duniyar shi’a babu wani littafi wanda yake ingantacce dari bisa dari.Mu ba mu yarda ba,shi yasa kofar ijtihadi a duniyar shi’a take a bude.Don haka,don wani malami ya fadi wani abu,na farko ba hujja bane,domin bai isa ya massala mazhaba ba.
  “Wa’yanda ke da haqqin su massala mazhaba sune ma’asumai sha hudu kawai.Duk wani mutum a cikin malamai wakilin mazhaban ne,amma ba shine mazhaban ba.Saboda ijtihadi yayi,kuma malamai suna iya mai raddi.Zasu iya sukar ijtihadin sa,shi yasa kofar ijtihadi take a bude.
  “To,shi wannan sokon,yai ta kwaso hadisan da ba ka bugatan sai ka karyata,amma kafin mu shiga,a irin wa’yannan bayanai dole muyi wa’yannan muqaddimat din.Na farko,hanyoyin da ake tantance ingancin hadisi ba sanadi kadai bane,sanadi juzu’I ne,mafi qaranta ma a cikin tantance ingancin riwaya.
  “Abu wanda ya fi karfi shine matani.Menene hadisi ya kunsa?wannan abin da ya kunsa na hadisi,bayanin da yake dauke dashi dole kar ya ci karo da nassi sarihi sahihi na Alkur’ani da sauran sunnah tabbatacciya da ainihin tarihi tabbatacce.”
Malamin a dai cikin wannan karatun ya bayyana cewa wannan riwaya ta  Ziyarar Ashura akwai malaman da suka tabbatar da rashin ingancinta,wato bata da inganci a sanadi.Wajen da ake cewa ALLAHUMMA IL’AN AWWALA ZALIMIN ZALAMA ……..wato wannan wajen ba ingantacce bane sanadan.Akwai mujtahidai maraji’ai wadanda basu inganta ta ba,kuma da hujjoji.
Sannan Sheikh Bashir yayi kira ga ‘yan uwa ‘yan ja’afariyyah da ka da su shigo da gullanci a shi’anci,saboda ba maslahar Ahlulbait bane.Ya bugaci ‘yan jafariyyah da su yi shi’anci wanda ya dace da marja’iyyah,sannan ka da su shiga gaban Imamai,wato ka da su nuna sun fi Imami sanin shi’anci.
Sannan Sheikh Bashir ya rusa da’awar marubucin littafin na “lillahi thumma lit tarith”na cewa  yayi karatu a Hauzar Najaf har ya kai ga darajar Ijtihadi da shahada mafi girma.