Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausa.ir
Alhamis

24 Nuwamba 2016

16:50:03
794019

Wani Bom Ya Tashi A Kasar Iraqi Ya Kuma Kashe Mutane Akalla 80

Wata babbar mota makare da boma bomai ta yi bindiga a garin hilla na kasar Iraqi ya kuma yi sanadiyyar kisan mutane akalla 80 mafi yawansu Iraniyawa ne wadanda suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan makokin arba'en a ranar litinin da ta gataba.

Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa garin Hilla yana kilomiya 100 daga kudancin birnin Bagdaza, kuma tuni kungiyar Daesh ta dauki alhain kai harin a wani sakon da ta aike a cikin yanar gizo.

Majiyar asbitoci da na yansanda sun bayyana cewa mutocin masu ziyarar arba'in guda biyar ne harin konan bakin waken ya shafa. Labarin ya kara da cewa mutanen sun tsaya ne son cin abinci a cikin wani dakin cin abinci kusa da wurin.

Wannan dai shi ne hari na fako masfi moni wanda kungiyar Daeh ta kaiwa musulman shia wadanda take daukarsu kafirai, wadanda kuma suka yi ruwa da tsaki wajen yakar Kungiyar a tungarsu ta karshe a birnin Musil na kasar Iraqi daga ranar 17 ga watan Octoban da ya gabata.288