Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausa.ir
Lahadi

20 Nuwamba 2016

12:11:39
793095

Birnin Karbala Ya Cika Makil Da Miliyoyin Masu Ziyarar Arbaeen

Miliyoyin musulmi mabiya mazhabar shi'a sun cika birnin Karbala domin halartar tarukan Arbaeen na Imam Hussain (AS).

Kamfanin dillancin labaran Alfurat News ya bayar da rahoton cewa, Nasif Alkhitabi shugaban majalisar lardin Karbala ya bayyana cewa, adadini mutane da suka isa Karbala ya zuwa yanzu ya kai mutum miliyan ashirin.

Ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da aka fara gudanar da tarukan na arbaeen daga makon da ya gabata, ya zuwa masu ziyara daga kasashen ketare miliyan 3.5 ne suka isa birnin karbala, yayin da kuma fiye da Irakawa fiye da miliyan 16 daga sassa na kasar suka isa birnin domin gudanar da tarukan na ziyarar arbaeen.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, za a ci gaba da gudanar da ayyukan ziyarar ta arbaeen daga nan har zwa ranar Litinin, a kan ba zai yiwu a iya bayar da hakikanin alkalumma na karshe ba dangane da adadin masu ziyarar na ciki da wajen kasar Iraki ba.

Ya ce a halin yanzu za a iya cewa adadin masu shiga da fita birnin na Karbala ksan daya ne, domin a halin yanzu mutanen da suka yi ziyara suna fita ne, saboda babu wurin zama, garin ya gama cika makil da mutane.288