Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausa.ir
Talata

15 Nuwamba 2016

16:35:19
792130

Adadin Mutanan da suka yi shahada sanadiyar harin da 'yan sandar Kano sun kaiwa Masu tattaki ya karu.

Adadin Mutanan da suka yi shahada sanadiyar buda wuta da 'yan sandar Kano suka yi a kan 'yan uwa musulmi almajiran shekh Ibrahim Elzakzaky ya karu

Tashar telbijin din Press Tv dake watsa shirye-shiryen sa daga nan birnin Tehran ya nakalto wakilan  'yan uwa musulmi almajiran shekh Ibrahim Elzakzaky na birnin Kano na cewa jami'an 'yan sandar Birnin Kano dake arewacin Najeriya sun buda wuta kan mabiyar mazhabar Shi'a almajiran Shekh Ibrahim Yakubu Elzakzaky yayin da suka fito domin yin tattaki na tsagayowar arba'in din Imam Husain (a.s) jikan Ma'aikin Allah (s.a.w.a) kamar yadda suka saba ko wata shekara, lamarin da ya yi sanadiyar shahada da kuma jikkatar mutane kimanin sama da 100.

Lamarin ya auku ne a yayin da jami'an 'yan sandar suka yi kokarin tarwatsa masu tattakin, inda su kuma suka ci gaba da yin tattakin kamar yadda kundin tsarin milkin Najeriya ya baiwa ko wani dan kasa damar yin addinin sa kamar yadda ya fahimta.

Wannan ta'addanci na jami'an tsaron Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin kare hakin musulmi dake birnin Landan ya bukaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da tsaron musulmin kasar a yayin gudanar da jimamin jagayowar ranar Arba'in na Imam Husain (a.s).

A watan da ya gabata ma, sama da 'yan uwa musulmi almajiran shekh Elzakzaky 20 ne suka yi shahada a gariruwan daban daban na kasar a yayin da 'yan sanda suka hai musu hari domin hana su zaman jimami na zagayowar shahadar Imam Husain (a.s) jikan Ma'aikin ....(s.a.w.a), alhali kuma kundin tsarin milkin Najeriya ya baiwa ko wani Dan kasa damar gudanar da addininsa kamar yadda ya fahimta.288