Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar Musulunci A Nageria
Litinin

14 Nuwamba 2016

10:15:13
791847

Jami'an tsaro sun kaiwa masu tattakin Arbaeen hari amma tattaki na ci gaba da gudana

Tun da safe a yau Litinin 'Yan uwa musulmi na Harkar Musulunci a Nigeria karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky suka fara gabatar da tattakin juyayin Arbaeen na lumana na shekara shekara da suka saba gabatarwa daga yankin Kano wanda Sheikh Sunusi Abdulkadir yake jagoranta.

Rahotanni sun tabbatar mana da cewa bayan da tattakin ya kankama su nufo Unguwar Dawaki sai jami'an tsaro suka fara harba hayaki mai sa kwalla, sannan daga baya suka rika harba harsasai masu rai, amma babu Shahidi da aka samu kawo ya zuwa hada wannan labarin.

Sannan kuma rahotannin sun tabbatar mana da cewa cikin ikon Allah masu Tattakin sun riga sun wuce shingen jami'an tsaron dake Unguwar Dawaki sannan sun ci gaba da tattakin zuwa Zariya in Allah ya yarda.

Kamar yadda aka sani dai a ko wacce shekara 'yan uwa musulmi suna gudanar da irin wannan tattakin na lumana don nuna juyayi da kisan gillar da aka yiwa Imam Hussaini[AS] jikan fiyayyen halitta Manzon Allah[SAWA].

In Allah ya kaimu ranar Arbaeen ambaliyar 'yan uwa zasi iso Zariya inda za'a gabatar da jawabin Arbaeen sannan a salami al'umma. 288