Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausa.ir
Litinin

14 Nuwamba 2016

09:57:05
791838

Jamia'n Tsaro Fiye Da 30,000 Ne Ke Gudanar Da Ayyukan Tsaro A Taron Arba'in A Karbala

Babban kwamandan rundunar da ke kula da ayyukan tsaro na yankin Furat ya bayyana cewa fiye da jami’an tsaro dubu 30 ne za su gudanar da ayyukan tsaro a taron arba’in.

Tashar al’alam ta bayar da rahoton cewa, babban babban kwamandan rundunar tsaro da ke kula da yankin Furat manja janar Qais Khalaf ya bayyana cewa fiye da jami’an tsro dubu 30 ne za su gudanar da ayyukan tsaro a taron arba’in na imam Hussain (AS) a shekarar bana.

Ya ce a halin yanzu haka sun riga sun fara gudanar da ayyukansu, domin tabbatar da cewa sun bayar da kariya ga masu gudanar da wannan babban taro na ziyarar arbain na Imam Hussain (AS) a birnin karbala mai alfarma.

Daga cikin ayykan har da kula da zirga-zirgar jama’a da kuam sanya ido kan dukkanin masu kai komo, domin tabbatar da cewa yan ta’adda ba su kawo wani cikas a taron ba.

Haka nan kuma an kafa wuraren binciken ababen hawa da kuma jama’a a ciki da wajen birnin karbala mai alfarma, kamar yadda kuma wasu dubban masu ayyukan agaji za su hada karfi da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa komai ya tafi cikin tsari.

Kimanin mutane miliyan 15 ne dai akee sa ran za su halarci taron arba’in na Imam Hussain (AS) a wannan shekara.288