Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HAIDAR CENTER ACADEMY
Alhamis

10 Nuwamba 2016

17:22:34
791117

MARAJI’AN SHI’A SUN HARAMTA GABA DA SHUGABA BUHARI

A Iran inda malamai suke da maraji'an shi'a gaba daya kaf sun yi ittifaki kan wani abu, sun haramta sam gaba da shugaban kasa General Buhari da duk wani shugaba da aka zaba in ba gaba ta siyasa ba amma gaba da sunan addini babu shi, shi'anci bai yarda da sunansa ka yi gaba da shugaban kasa ba ko waye!. In Ji Dr. Hafiz Muhammad Sa’id

Gabatarwa:
 
Dr. Hafiz Muhammad Sa’id yana da digiri na uku (PhD) a fannin Falsafa, kuma malami ne a Jami’ar Al-Mustapha ta Iran. Ya rubuta litattafai da dama a kan Musulunci da rayuwa. Sannan ya rubuta daruruwan maqaloli a fannoni daban-daban na ilimi. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu na Kano, Muhammad Ahmad Sulaiman, a lokacin da ya kawo ziyarar ganin gida, Daktan ya fayyace lamurra da dama kan matsayin aqidar Shi’a game da tsarin dimokuradiyya da nauyin da ya hau kan dan Shi’a a qasa irin Nijeriya.
 
Tattaunawa:
 
AHLULBAITI: Dr. ka dau lokaci kana karatu a Iran har ka kai wannan matsayi na Daktan ilimi, shin me za ka ce game da bambancin salon mulkin dimokuradiyya tsakanin qasar Iran da qasarka Nijeriya?
 
Dr. Hafiz: A gaskiya na ji dadin wannan tambaya, tana da muhimmaci sosai dangane da bambancin salon mulkin dimokuradiyya tsakanin qasar Nijeriya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Akwai wani abu da muke cewa asasin mutum ba asasin jam’iyya ba; mutum shi ne muhimmi a cikin qasa, don haka wannan mutumin da za a zaba a cikin qasa domin ya jagoranci al’umma, ya zamanto yana da siffofi na qasa, wato na iya gyaran qasa, to kusan wannan ita ce fomular da ta fi qarfi a dimokuradiyyar Iran. A qasashenmu, abin da aka fi qarfafawa ita ce jam’iyya. Kowane mutum idan ya shiga jam’iyya yakan yi qoqari ya kare wannan jam’iyya, kuma idan yana son ya yi wani aiki, za ka ga ya koma jam’iyya kaza, domin ya yi aiki kaza, to wannan yakan sa idan jam’iyya ta ci mulki sai wadansu mutane su zo su yi dafifi su maqale wa wannan jam’iyyar domin su ci albarkacin wannan jam’iyya mai mulki saboda mutum yana son wanda yake damawa da shi, wanda qarfi da iko yana hannunsa da’iman, sai ka ga ya karkata zuwa ga wannan jam’iyyar.
Wannan ne ya sa za mu ga magana kan jam’iyya ta yawaita sosai a cikin Nijeriya, amma a dimokuradiyyar Iran ba jam’iyya da jam’iyya ba ce, a’a, ra’ayoyi ne, za ka ga mutum ya tsaya shi kadai ba tare da wata jam’iyya ba, wato ‘independent’ ke nan. Za ka ga kuma akwai wadanda ake ce wa ‘reformists’ ko ‘conservatives’ masu ra’ayin riqau, da kuma ‘islahiyyun’ masu neman gyara a harshen siyasa, sai ya zama wadannan su suke tsayawa domin takara. A Nijeriya kuwa za ka ji an ce jam’iyya kaza ta tsaida wane, to wannan jam’iyyar takan zamo wata katanga, za ka ga shugaban jam’iyyar bai cancanci mulki ba, ko bai cancanci jagoranci ba, amma jam’iyya ba ta ba ni damar in zabi wani ba. A Iran babu irin haka. Su suna ganin idan mutum ya san dan takarar jam’iyyarsa ba zai iya ba, to cin amanar qasarsa ne ya zabe shi. Sai ya zabi dan wata jam’iyyar daban. Wannan na daya ke nan.
Na biyu, wannan dimokuradiyyar takan ba wa mutum damar zabar irin wanda zai kama salon mulkin da yake so ne a Iran. A Nijeriya ma mun ga yawanci bayan wannan ya samu amma sau tari wadanda suke zabar suna son su tsira daga azabar wani ne wanda ya gabata, saboda haka sai su yi riqo da duk wanda ya zo ko da waye kuwa domin kore wancan. Wannan yana faruwa ne a Nijeriya, ba kasafai yake faruwa a Iran ba. Domin a Iran yawanci a kan duba manufar shi wanda za a zaba ne. A dimokuradiyyar Nijeriya mafi yawanci a kan duba wane ne ya gasa su, sai su bar shi, kuma koda waye za su kama bayan shi, muhimmi dai su tsira daga azabar wancan da suke ganin ya zo ya gasa su. Wannan ma yana daga cikin bambancin dimokuradiyyar da ake da shi.
 
Amma a tsarin dimokuradiyyar za mu ga ofishin da ake zaba a Nijeriya yana da qarfi sosai fiye da ofishin da ake zaba a Iran. Saboda tsarin can akwai wanda yake shi ne jagoran al’umma mai shiryar da su, wato abin da ake kira ‘spiritual leader’ da turanci, wanda kuma malami ne mai taqawa, mai ilimi, wanda zai tsaya kai tsaye mai hankali, mai zurfin tunani, kuma uba ga kowa. Shi ne zai tsaya ya kalli aikin shugaba sosai kuma duk inda ya ga ya yi kuskure ya gyara masa, sabanin Nijeriya inda shugaba yake da pawa sosai. 
 
Sai dai kuma sun yi tarayya wajen yin zaben abin da suke so, sannan kuma akwai wahala sosai a iya ture ko canza abin da mutane suka zaba a Iran. Yana da wahala sosai, sabanin Nijeriya zai iya yin sauqi, saboda kwamiti din da yake qarqashin zabe, kwamiti ne na malamai goma sha biyu masu tsoron Allah da taqawa, wadanda suke jin tsoron hisabi ranar Lahira, da kuma manya-manyan masana dokar qasa da qasa ta duniya guda goma sha biyu, wanda wannan kwamitin shi zai duba zabe da sakamakon zabe da shirya zabe da tsara duk wanda za a tura duba zabe tsakaninsa da Allah, tunda qasa ce da babu cin-hanci, don haka ba za ka samu wanda zai ba ka ko kwabo ba. Don haka ba za ka iya shelanta sabanin zabe ba, tunda ba wanda zai ba ka kudi.
 
Sannan kuma a rantsar da kai saboda Allah cewa akwai ranar hisabi, a kan me za ka yi qarya a kan abin da za ka shiga wuta? Kuma har ila yau babu inda za ka samu mutanen gari wai wani ya zo ya ba su kudi, saboda haka zabe suke yi ba tare da an ba su kudi ba sai dai don kishin qasa. A Nijeriya akwai masu fitowa don kishin qasa, amma kuma akwai wadanda biyansu ake yi su dangwala wa mutumin da sai ya yi shekara hudu ma ba su sake ganinsa ba. A Nijeriya akwai irin wannan babbar matsala sosai da muke ganin tana faruwa saboda ba da kudi.
 
Haka nan a can babu ’yan hayaniya a titi. Kamfen a can a talabijin ake yinsa. Misali, hukuma za ta ce ta ba wa kowane dan takara awa hamsin ya yi kamfen a talabijin da rediyo, sannan kuma akwai tattaunawa tsakanin dan takara da dan takara a lokuta daban-daban kamar sau biyu ko sau uku, kowa ya fadi manufofinsa, a yi masa tambaya, kowanne zai yi alqawarin abin da zai iya, saboda haka babu batun kudi a ciki gaba daya. Wannan ya sa siyasar Iran tana da tsafta fiye da ta Nijeriya. Lallai akwai buqatar a tsarkake siyasar Nijeriya game da kudi ta yadda talaka don kishin qasa zai je ya yi zabe, ba don kudi ba. Shi kuma wanda za a zaba ya san idan ya je ba dukiya zai samu ba, babu wanda zai ba shi cin-hanci shi ma wahala zai sha wajen kare doka da qasa. Ke nan ba wanda zai fito sai mai ikhlasi wanda yake yi don qasa kuma don Allah.
 
Sannan ba ka buqatar ka zama babban mai kudi kafin ka fito takara, wannan ma akwai shi a Nijeriya wanda a can yana da qaranci. Malamin jami’a zai iya fitowa takara ya zama shugaban qasa. Kowa zai iya fitowa ya zama shugaban qasa matuqar ya cika siffofin da aka nema domin yin kamfen, saboda haka ba za a hada da Nijeriya ba wacce kana buqatar mutanen da za su ba ka gudummawar kudi masu yawan gaske saboda sai ka je jiha-jiha yin kamfen, can ba ka buqatar zuwa jiha-jiha don yin kamfen, a talabijin za ka yi da rediyo, kowa zai ganka, ya ji ka da manufofin ka, saboda haka akwai bambanci ta wannan fuskaci, shi ya sa ba za mu ga ’yan daba da ’yan sara suka da ’yan jagaliya suna hayaniya da hargitsi a kan tituna ba, bare ka ga fitina da sare-sare, duk babu wannan a cikin wannan qasa gaba daya.
 
Wannan kadan ke nan daga cikin abin da za mu iya fada na bambancin salon siyasar dimokuradiyya a Nijeriya da Jamhuriyar Muslunci ta Iran. Akwai wasu ababen masu yawa da na bar su wadanda suke nuna wannan bambanci a tsakanin wadannan qasashe guda biyu saboda gudun tsawaitawa.
 
AHLULBAITI: Mece ce fahimtar Shi’a a kan tsarin dimokuradiyya?
Dr. Hafiz: Abin da za mu iya cewa game da fahimtar Shi’a a kan tsarin dimokuradiyya shi ne, Shi’anci, wanda yake shi ne madarar Musulunci baki daya, mene ne shi, wato mene ne Shi’anci?
Shi ne biyayya ga Manzon Allah (sawa) da wasiyyarsa. Manzon Allah (sawa) ya ce wa duniyar Musulmi: “Na bar mu ku littafin Allah da Itra ta, Ahlin gidana,” to Shi’a sai suka riqe wannan wasiyya ta Manzon Allah (sawa). Duk wani abu daga Manzon Allah (sawa) da Itrarsa suka karba. Karantarwar Musulunci a mahangar Ahlulbaiti (as) shi ne Allah ne yake da ikon ayyana shugabanni. Shi ya ayyana Manzon Allah (sawa) ya kuma ayyana masa halifofi goma sha biyu daga Ahlulbait (as) wadanda ya ce a bi su, kuma ya fadi sunayensu su goma sha biyun, ya kuma ayyana su. To idan mutane ba su karbi hukumar itrar Manzon Allah (sawa) ba, kamar yadda duniyar Musulmi ma ta qi su, ta qi karbarsu a lokacin da ma suke raye, bayan wucewarsu kuma mabiyansu sun samu tsangwama har zuwa yau, to wadannan mabiya Ahlulbait (as) a karantarwarsu shi ne akwai hukumar mutane. Imam Ali (as) shi ya koyar da wannan cewa, idan mutane ba su yarda da hukuma ta Ahlulbaiti (as) ba, to dole fa su yi hukuma ta mutane. Amma muhimmin abin da ake buqata a nan shi ne, ita wannan hukumar ta mutane ta yi adalci. Ita wannan hukuma tana iya zuwa bisa yardar mutane, kuma babu wata hanya da take nuna yardar mutane kamar hanyar dimokuradiyya a yau, saboda ta zo da tsarin yadda jama’a za su zabi shugaba.
 
Yarjejeniya ce tsakanin al’ummu, kuma duk abin da mutane suke so shi ne za a yi a hukumar mutane. Muhimmin abu shi ne, wanda yake jagorantar hukumar mutane a kowane ofis, dole ne ya tabbatar da adalcin da aka nema ya yi, kuma da wannan adalcin zai samu rahmar Allah (swt). Amma idan ka sake ka yi zalunci, ba kai ba tsira a ranar lahira. Don haka a hukumar mutane babban musiba ce ga shugaba ya ware wasu a kan wasu, ko ya fifita wasu a kan wasu, ko ya saurari wasu, ya qi sauraron wasu. Wannan ya tanadi azabar Ubangiji domin ba shi da wata mafita sai dai azabar wutar jahannama wa’iyazu billah. Don haka hukumar mutane take da hatsari, idan za ka iya ta, to ka ce zan iya, ka yi irin ta Annabi Yusuf (as) da ya ce: “…ij’alni alaa khazaa’inil ardhi, inni hafizun alim,” ka tsaya mutane su zabe ka, amma ahir aka zabe ka kuma ka kasa, to a nan bala’in yake. Amma idan ka san ba za a yi adalci ba, kada ka zo. Wannan shi ne mahangar mazhabin Ahlulbaiti (as) a kan abin da ya shafi dimokuradiyya. Dimokuradiyya hanya ce a yau da ake amfani da ita domin ayyana wane ne zai jagoranci ofisoshin mutane, wannan shi ne.
 
AHLULBAITI: A tsarin qasa irin Nijeriya, shin ya dace a ce wasu masu kiran kansu ’yan Shi’a su yi da’awar samar da gwamnatin Musulunci a cikinta?
 
Dr. Hafiz: A tsari irin na Nijeriya babu wani mai haqqi da zai danqara wa mutane wani tsari sabanin yadda aka yi yarjejeniya. Shi’anci bai taba yarda wani ya zo ya ce zai danqara wa mutane hukumar Musulunci ba alhali mutane ba su zabi hakan ba. Abin da Shi’anci yake cewa shi ne, duk abin da mutane suka yi yarjejeniya a kai shi ne muhimmi. Za mu ga irin wannan yarjejeniya Manzon Allah (sawa) ya yi ta da Kiristoci da Yahudawa lokacin da ya yi hijira zuwa Madina. Ya rubuta tsare-tsare da dokoki ayyanannu wadanda suke dauke da halaccin kiyaye haqqin juna da tafiyar da hukuma ta addini da Musulunci qarqashin jagorancin Manzon Rahma (sawa), bisa yarjejeniyar mutane baki daya na Madina, mutanen da suke maqwabtaka da su daga Yahudawan banu Qainuqa da banu Nadir da banu Quraiza suna wajen Madina a gefe, su ma akwai yarjejeniyar zamantakewa a tsakaninsu da Musulmi da sauran mushrikai da suke qarqashin wannan daula mai shalkwata a Madina.
 
Manzon Allah (sawa) bai taba tilasta wa Yahudawa da Kiristoci sai sun yi hukunci da Muslunci ba, bai kuma tilasta wa mushrikan da suke cikin Madina su musulunta ko a yi mu su hukunci da Alqu’ani dole ba. Saboda haka a Nijeriya ka samu kan ka, ko a Amurka, ko Australia, ko ma a ina ne a duniya, yarjejeniyar da mutane suka yi na zamantakewa, shi ne abin la’akari. A cikin China akwai addinai, a Indiya akwai addinai wajen dari da hamsin da mazhabobi wajen dari takwas, suna da yarjejeniyar zamantakewa, suna zaman lafiya da juna, me ya sa Nijeriya ba za mu samu irin wannan ba?
 
Don haka babu batun cewa zan zo in danqara wa mutane kirana ko ra’ayina, a’a. Ko kuma in ce dole sai na yi mu su hukumar Musulunci, ko kuma idan ba a kafa hukumar Musulunci ba akwai matsala, wannan wata magana ce wadda babu ita a cikin Musulunci kuma bai yarda da ita ba. Kawai abin da Musulunci ya ce a yi yarjejeniya ne. Kowanne ya yi nasa. Su yi yarjejeniya bisa tsari kamar yadda muka ce a baya, tsarin da mutane suka yi yarjejeniya a kai, tsarin hukumar mutane. Kuma muhimmi shi ne wanda ya zo, ya yi mu su adalci. Dama dai ko dai hukumar Allah, ko kuma in kun qi ta, sai ku yi hukumar mutane. Wannan wani abu ne wanda yake tabbatacce cewa sai mutane sun samu jagora mutumin kirki ne ko na banza wanda zai zamanto ya tsaida hukuma ko dokoki. Saboda haka babu tunanin cewa lalle sai na yi gwagwarmaya na tabbatar da Musulunci a karantarwar mazhabin Ahlulbaiti (as) sam-sam! Shi’a karantarwa ce da take cewa yarjejeniya tsakanin mutane ita ce muhimmi.
 
A Nijeriya muna da Kiristoci da wadanda ba Musulmi ba, ya za a yi mutum ya zo ya ce sai an yi tsarin da ya zo da shi dole? Sannan Musulmi nawa ne suka yarda sai an yi hukumar Musuluncin su ma? Sannan idan an yi hukumar Musuluncin, waye ya fahimci hukumar Musuluncin? Waye zai iya tafiyar da hukumar Musuluncin? Ina tabbatar maka a Nijeriya babu mutum qwara guda goma da suka san yaya za a tsara hukumar Musuluncin. Mun ga wadansu sun ce za su yi shari’ar Musulunci, amma daga zuwa sai suka samo injin datse hannaye. Sun dauka Musulunci shi ne wannan, wa-iyazu billah! Sai hakan ya ba da mummunar sura ga Musulunci. Sannan kai ba halifan Manzon Allah (sawa) ba wanda ya ayyana a cikin halifofinsa goma sha biyu, to kai waye da za ka ce sai ka zo ka danqara mu su hukumar Musulunci a fahimtarka? Sam ba mu da wannan ma’ana ta sai ka danqara wa mutane Musulunci a fahimtarka, ko dole sai an yi tsarin hukumar Musulunci. Kirista yana zama shugaba a Habasha ya zama adali. Manzon Allah (sawa) kuma ya ce wa Musulmi su je wajensa: “Inna bihaa malikan adilan.” Ma’ana, “Haqiqa a can (Habasha) akwai shugaba adali.” Kuma da ya rasu Manzon Allah (sawa) ya yi masa sallah (salatul ga’ib), shi ya sa ma wadansu suka ce ya musulunta. Ko da dai bai musulunta ba, to mun ga ya samu uzuri ya samu rahma saboda adalcin da ya yi, saboda haka wannan muhimmi ne, mu san da haka.
 
AHLULBAITI: Mece ce fahimtar Shi'a kan bin dokoki a qarqashin qasar ba ta hukunci da Qur'ani?
 
Dr. Hafiz: Wannan tambayar reshe ce ta abin da ya gabata, duk lokacin da mutum ya shiga qasa, ko me take bi, ko wane tsari take bi, da ake cewa yana rayuwa qarqashin qasa bisa yarjejeniyar zamantakewa ta wannan qasa da wannan al’ummu suka rattaba hannu a kanta, wannan yarjejeniya da suke a kai wajibi ne ya kiyaye ta, haka Musulunci yake cewa. Sannan akwai dokoki na hankali wanda ake cewa duk abin da hankali ya zartar, to shari’a ta yarda da shi, duk da cewa da yawan mutane sukan yi kuskure sai su ce dokokin da mutane suka tsara ba na Alqu’ani ba ne. Abin da suka kasa ganewa shi ne, akwai dokoki na hankali, misali: muna so mu tsara Jihar Kano bangare-bangare, ko mu tsara yadda za a share Kano, yadda za a jawo ruwa, ko yadda za a jawo wuta da yadda za a samar mata da tsaro, shin a duk wannan muna buqatar ayar Qur’ani ko hadisi? Mu duba kundin tsarin mulkin da Manzon Allah (sawa) ya rubuta na yarjejeniyar zamantakewa tsakaninsa da mutanen da suke kewaye da Madina na daga Yahudawa da Kiristoci da mushrikai, shin aya ya jawo a ciki? Ba aya ya jawo ba. Shin hadisinsa ya fada a ciki? Ba hadisinsa ya fada a ciki ba. Yarjejeniya ce tsakanin zamantakewar mutane. Idan ka ji an ce akwai wata doka da ta saba wa Qur’ani, to kamar doka ce da za ta ce dole ne ko wajibi ka sha giya a wannan qasa, to a nan sai ka ce a’a, ba zan yarda da dokar da ta ce wajibi a sha giya ba. Amma tsarin qasa da dokar tsarin qasa suna qarqashin “amruhum shura bainahum” ne. Al’amari ne tsakanin mutane shi ya sa ma muka ce mata hukumar mutane. Akwai hukumar Ahlulbait (as) wadda Allah (swt) ya ayyana ta (spiritual hukuma) wadda take nufin alaqar wilaya tsakanin bawa da su. Wajibi ne wanda ya mutu bai yi imani da Imaminsa ba, ya yi mutuwar jahiliyya, wanda bai san Imamansa ba, wadannan Imaman guda sha biyu da Manzon Allah (sawa) ya ayyana wa mutane, “Kitabullahi wa Itrati Ahlubaiti,” littafin Allah da itrata, abin da addini ya ce ke nan.
Amma tunda babu su a zahiri dole a samu hukumar mutane, wannan wani abu ne wanda suka tabbatar. A hukumar mutane, muhimmin abu shi ne ta yi adalci, saboda haka akwai mugalada sosai mutum ya ce ai wannan hukuma ba ta aiki da Qur’ani, ko ba ta aiki da kaza, a’a, hukuncin wannan yana bin adalcin yarjejeniyar da mutane suke a kai kuma a bisa wannan Allah zai mu su hisabi ga duk wanda bai kiyaye wannan yarjejeniyar ba, saboda haka wannan tambayar reshe ce ta wancan mas’alar da ta gabata dangane da hukumar mutane.
 
AHLULBAITI: Wane tsari aqidar Shi'a ta tanadar don gudanar da rayuwa a tsakanin al'ummu masu bin aqidu da addinai daban-daban?
 
Dr. Hafiz: Aqidar Shi’a kamar yadda muka ce Shi’anci shi ne madarar Musulunci, kitabullahi wa itrati, littafin Allah da itrar Manzon Allah, su ne wasiyyar Manzon Allah, kuma su za a bi, to Shi’anci yana ganin wajibcin kiyaye mutunci da qima da daraja da jini da dukiya da aqidar (ra’ayin) kowane mutum. Ba a taba samun Shi’anci ya dorawa wani mutum ra’ayinsa da qarfin tsiya ba. Kuma har yanzu babu wata qungiya ta Shi’anci da za a ce ta kai hari kan wadansu mutane, ko ta rusa mu su gida, ko ta lalata mu su kaya saboda kawai ba su yarda da ra’ayinta ba, ba a taba samu ba. Ba yadda za a yi ka samu wannan a cikin aqidar Shi’anci. Shi ya sa duk inda Shi’anci yake, zaman lafiya yana wurin a duniya. Wannan an shaidi Shi’a da shi.
Saboda haka Shi’anci abin da yake cewa shi ne tattaunawa ta ilimi, abin da Ahlulbaiti suka koyar ke nan. Idan ka ce ni ina da yaqini nawa ne daidai shi ke nan. Lakum dinukum waliyaddin. Ka yi naka ni ma in riqe nawa. Ni ina ganin haka ne daidai, kai kana ganin haka ne daidai ba rigima. Ubangiji yana nan kuma shi ne wanda zai yi hisabi a kan abin da muka riqa na aqida. Shin abin da nake yi, ko kai kake yi, a wurin Allah daidai ne ko kuskure muke aikatawa? Allah ne dai mai hisabi. Saboda haka wannan shi ne sirrin zaman lafiya. Da a ce duniya za ta bi Shi’anci, da an zauna lafiya. Saboda Shi’anci ne ya zo da wannan fomular. Kuma za mu ga qasashe da yawa na yammacin duniya sun riqi wannan fomula cewa a rayu da tattaunawa. Aqidu su tattauna idan ana da buqatar tattaunawa.
 
Yanzu misali a Nijeriya babu buqatar wani mutum ya je wajen gwamna ko shugaban qasa ya ce su wane ’yan kaza ne, ya yi ta zuga shi a kan haka saboda yana ganin shi dan boko ne bai san addini ba. Yaya za a yi shugaban qasa ko gwamna ko minista ya san waye yake kan daidai? Ba zai sani ba. Abin buqatar shi ne a tara malaman wuri daya, a ce ku zo dukkanku. Ina ’yan Shi’a? Ina ’yan Dariqu? Ina ’yan Izala? Ku zo ku zauna, ga abin da ake so a tattauna a kai. Ya ji wannan ya fada, ya ji wancan ya fada. Ya ji hujjojin kowa, wannan zai sa ya fahimci kowa. Amma ba a buqatar a tunzura mutane a zuga su cewa ku far wa aqida kaza. Saboda haka tattaunawa ita ce mafita. Wannan shi ne abin da Shi’anci ya zo da shi, kuma yake qarfafawa a tsakanin al’ummu. Tsohon shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Khatami, ya je da wannan qudurin kuma Majalisar Dinkin Duniya ta karbe shi da muhimmanci sosai.
AHLULBAITI: Me Dakta zai ce kan aqidar Wahabiyyanci da Wahabiyawa a Nijeriya?
 
Dr. Hafiz: To, matsalar da muka samu shi ne aqidar Wahabiyanci ita ta fi kowace aqida rashin jurewa aqidu da rashin iya zama da su waje daya. Ba sa iya jurewa ra’ayin da ba nasu ba. Wannan shi ne babbar musibar da take tattare da Wahabiyanci. Wahabiyancin nan da ya zo Nijeriya ya kafirta sauran mutane. Da yawan mutane idan an ce Wahabiyanci ba su san meye shi ba. Wahabiyanci mutane ne daban-daban suna da qungiyoyi a Nijeriya, ba mamaki qungiyoyin Wahabiyawa su kai goma a Nijeriya, amma wadda ta fi shahara ita ce Izalatul bidi’a wa’iqamatus sunnah, da irin su Jama’atud-Da’awa, da irin su Alfurqan da sauransu, za ka gan su daban-daban dai. A Kudu ma akwai irin su Ansarus-Sunnah da sauransu, wanda za mu ga duk Wahabiyawa ne. Akwai kuma masu zaman kansu, ga sunan da yawa za ka ji su a gidajen rediyo. Sannan akwai ma qungiyoyin da ba su ce su Wahabiyawa ba ne amma suna tasirantuwa kuma suna da aqidu irin na Wahabiyawan. Akwai wasu wanda cibiyarsu ma a Kano take. To za mu ga wadannan aqidu da’iman ba sa jurewa wanda ba su ba.
 
Wannan shi ne babban matsala. Shi ya sa ma za ka ga akwai wata magana ta hikima da aka jingina ta kwanan nan ga Shugabar Jamus, cewa, a Indiya akwai addinai dari da hamsin, akwai mazhabobi dari takwas, dukkansu suna zaman lafiya. Amma Musulmi dukkaninsu suna zaune addini daya, amma ba a zaman lafiya. Sakamakon me? Sakamakon Wahabiyanci. Ba ya iya jure wani abu ba shi ba. Wahabiyanci da’iman ya daukar wa kansa sai ya yi makirci da sharri da qage ga mazhabin Ahlulbaiti (as) da kuma sauran mazhabobi. Wannan muna gani a fili, wanda yake sauraron rediyo ko yake kallon talabijin, ko yake ganin rubuce-rubuce a jaridu da facebook da whatsApps yanzu haka a Nijeriya zai fahimci yadda Wahabiyanci yake zuga wasu mutane domin su far wa mabiya Ahlulbaiti (as), ba don komai ba saboda Wahabiyanci yana gadan koyarwar Umayyawa wadda take qiyayya da gidan bani Hashim da Manzon Allah (sawa) ya tashi a kai da Imam Ali da Imam Hasan da Imam Husain (as). Su kuma Shi’a suna riqo da koyarwar bani Hashim wadda take cikin gidan Manzon Allah (sawa) da ta tashi daga Ali, Hasan, Husaini da mabiyansu da jikokinsu, to wancan rikicin na bani Hashim da bani Umayya sai aka sake kawo shi cikin Musulunci, sai aka samu mazhabobi guda biyu; ko dai kana tare da bani Umayya, ko kuma kana tare da bani Hashim, shi ne kitabullahi wa itrati Ahlabaiti, wato wasiyyar da Manzon Allah (sawa) ya bari wadda bani Umayya ba su yarda da ita ba.
Wannan ne ya sa shi wancan bangaren na bani Umayya duk inda yake, yana koyar da kashe wannan bangaren na bani Hashim ne. Shi ya sa ma bani Umayya suka kashe Hasan suka kashe Husain (as), suka kashe duk wani wanda Manzon Allah ya ayyana a matsayin wakilansa a bayan qasa daga Ahlulbaiti (as), kuma suka kashe mabiyansu.
 
A qwaqwalwar Wahabiyawa na yanzu, suna ganin za su iya ci gaba da wancan abin na da. Saboda haka suke amfani da hukumomi da masu muliki wajen cimma wannan manufa da zarar sun samu dama. Ba komai ne ya sa suke rusa qasashe na mabiya Ahlulbaiti (as) ba sai wannan dalili. Iraqi ba su bari ta zauna lafiya ba. Baharaini ma haka. Hutsawan Yamen ma wadanda jikokin Imam Hasan (as) ne, su ma ba a bar su sun zauna lafiya ba. Alawiyyawan Siriya da Bashar Asad da ake ta kashewa yanzu, da Alawiyyawan Turkiyya da ake kashewa, duk ba wani laifi suka yi ba sai kasantuwarsu jikokin Imam Ali (as). Duk wannan yana nan a tarihi an dauwana. Sharri da qage da kisa wasu ababe ne da Wahabiyanci ya tsayu a kai.
Wannan dalilin ya sa da wannan koyarwar ta zo Nijeriya sai ga shi tana yin aiki irin wannan. Da Wahabiyanci ya zo sai ya kafirta ’yan Dariqa saboda ma’abota Dariqar Qadiriyya da Tijjaniyya suna riqo ne da koyarwar tsatson gidan Annabi (sawa) daga jikokin wadannan Halifofi na Manzon Allah (sawa) guda sha biyun nan da ya ayyana daga Ahlulbaiti (as). Babban laifinsu shi ne daga wannan gidan suke shi ke nan.
 
A yau din nan, da za su ce sun yi riqo da bani Umayya, sun qyamaci mazhabar gidan Annabi (sawa) da koyarwarsu, to da sun zauna lafiya. Ko su ce ba ma qaunar Maulidi, ba ma qaunar tawassuli da Annabi (sawa), ba ma qaunar tawassuli da jikokin Annabi (sawa), ko kuma su ce ba ma ziyartar qaburbura muna nema mu su matsayi wajen Allah, muna neman gafara, muna kuma tawassuli da su, da a yau za su zauna lafiya a wurin Wahabiyawa. Wahabiyanci ya dauki wannan alamomi na gidan Manzon Allah (sawa) a matsayin shirka da kafirci, to kuma da ka kafirta mutum sai ka halasta jininsa, wannan wani abun mamaki ne game da Wahabiyanci. Wanda ko da ka kafirta mutum, ba yana nufin ka halasta jininsa ba ne, wannan bai isa ba.
 
A Musulunci ba a yarda a kashe kafiri ba. Ko da ka ce dan Dariqar Qadiriyya da Tijjaniyya kafirai ne, dan Shi’a kafiri ne, to bai halasta ka kashe su ba, don bai halasta ka kashe kafiri ba, ko wanda ba Musulmi ba. A Musulunci jininsa amintacce ne.
 
AHLULBAITI: Shin me Dakta zai ce game da haramta qungiyar ’yan Zakzakiyya mai suna IMN da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi? A Shi’ance me ya kamata ’yan IMN su yi?  
 
Dr. Hafiz: To, ni kaina na yi tsammanin bayan kwana daya da shelanta haramta IMN, za su kai kotu a washegari na ranar shelanta wannan abu, amma kuma sai muka ji shiru, saboda haka wani abu ne wanda yake sananne, babu wata hanya sai kaiwa kotu, domin kana da haqqi ka yi abubuwan ka na addini matuqar ba ka takurawa kowa ba, ba ka lalata tsarin qasa ba, saboda haka idan mutum aka haramta masa al’amarinsa sai ya je kotu, haka ya kamata Islamic Movement ta yi. Idan haramcin nan ba bisa doka ba ne to kotu za ta ce ba daidai ba ne, idan kuma daidai ne meye hujja sai a ba su hujja. Idan kuma rajista ce, a yi mu su rajista misali, sai dai kada a cakuda haramta qungiya da haramta addini, saboda na ga wannan a maganganun Wahabiyawa Izalawa, da yawansu sun rubuto cewa an haramta Shi’a a Nijeriya, sai dai su sani cewa Shi’anci ba zai hanu ba, ba wanda ya isa ya haramta Shi’anci. Manzon Allah (sawa) shi ya zo da shi ya assasa shi a matsayin makomar al’umma “Kitabullahi wa itrati Ahlubaiti,” biyayya ga littafin Allah da Ahlin gidana. Wannan ita ce wasiyyar Manzon Allah (sawa).
 
Idan kai ba za ka bi wasiyyar Manzon Allah (sawa) ba, to ba za ka hana wani ya bi ba. Wannan ce qa’ida. Wannan wasiyyar Manzon Allah (sawa) din ka kira ta son Ahlulbaiti (sawa) ko ka kirata Shi’anci wani abu ne daban, amma ita ce dai wasiyyar Manzon Allah (sawa) ga al’ummarsa. Saboda haka yana da kyau su gaggauta zuwa kotu domin warware wannan matsala sosai kuwa.
 
AHLULBAITI: A qarshe wane kira za ka yi ga al'ummar Arewa da suka kusa bankwana da fitinar boko haram, sai kuma ga shi ana qoqarin sake maida su cikin wata rigimar da ta fi waccan?
 
Dakta Hafiz: Gaskiya ne, tabbas idan mutane ba su yi hattara ba, rigimar da ake so a kunno za ta fi ta da. Domin tana da hatsari sosai. Saboda a wancan lokaci jami’ai suka takura wasu jama’a da ake ce mu su Jama’atu Ahlus-Sunnah Lidda’awati Wal Jihad, wannan ya sa suka takura su har suka kai ga daukar makami. Wadannan kuma mutane ne marasa yawa da suke a gefe. Saboda haka ina ganin hukuma ita ya fi kyau ta yi hattara sosai don kada wani bangare ya yi amfani da ita a kan wani bangaren daban.
A qasar da aka ce kowa zai iya yin addininsa, zai iya yin ra’ayinsa da tunaninsa, a yi hattara sosai da fitintinun da ake neman haifarwa. Yana da kyau a zaunar da Wahabiyawa a sa mu su iyaka a tunaninsu, su daina kafirta Musulmi. A cikinsu na san akwai wasu qalilan masu hankali da tunani wanda suka yi nuni da cewa wannan abin fa Musulmi ake nufi gaba daya, ’yan uwanmu ku yi hattara. Amma wadancan ba su yarda ba. Sun ci gaba da ingiza mutanensu domin ganin an zubar da jinin mutane an rusa gidajensu da makarantunsu, to wannan fitina ce wadda in ta taso, ba fa za ta shafi kawai dan Izalar da ya tayar da ita ba, har kai da sauran mutanen gari za ta shafa. Izala kake yi, ko Dariqa, ko Shi’a, za ta shafi kowa. Saboda haka muna kira da jan halin mahukunta da su bincika su kama kowaye yake da hannu a cikin wannan kashe-kashe ko da kuwa sarki ne ko kwamishina ko wani jami’in na daban don kaucewa afkuwar irin wannan nan gaba.
 
Gwamnoni da ’yan boko su yi hattara. Su sani addini ba wasa ba ne. Su nemi addini inda ya cancanta. Idan ma suna kokwanto su dinga hada ma’abota mazhabobi su hada su a dinga tattaunawa a gabansu domin su ga waye yake da hujja, waye ba shi da hujja, me ya sa ake jin tsoron tattaunawa da mutane sai dai a kai mu su hari? Sai dai a kira malamin Izala, ga shugaban qasa ko gwamna, malamin Shi’a kai ma ka zo; malamin Dariqa duk ku zo, ku tattauna a kan mas’alolin da ake rigima a kai. Wace mas’ala ce, meye hujjarku ta shari’a a gani a tabbatar da abin da ya dace. Yana da kyau lalle mu yi hattara al’ummar Arewa, saboda kullum makirci ake qulla mu ku, kuma ba a qulla makircin sai an saka tunanin Wahabiyanci domin kawo fitina a wannan qasa. Ina kuma kira ga su Wahabiyawan da su janye qoqarinsu na son kawo fitina cikin wannan qasa tamu.
Haka nan ina kira ga ’yan uwa ’yan Harkar Musulunci, su ma su tabbata duk abin da za su yi, su bi doka da oda. A Iran, inda malamai suke da Maraji’an Shi’a baki daya kaf sun yi ittifaqi kan wani abu, sun haramta gaba da Shugaban qasa Muhammadu Buhari da duk wani shugaba da aka zaba, in ba hamayya ta siyasa ba. Shi’anci bai taba yarda da ka yi gaba da shugaba ba kowaye. Haka nan bai taba yarda ka zo ka yi abu babu neman izinin hukuma ba a duk abin da ake neman izini a kansa. Idan za ka yi taro, ka nemi izinin hukuma, ta tabbatar akwai aminci, sannan ta ba ka tsaro. Idan kuma kana da wasu ayyuka da ake buqatar rajista lallai ka yi rajista, ka halarci zabe, ka zabi wanda kake ganin zai yi maka adalci a cikin wannan hukuma, da sauran dokoki wanda ya zama dole ka kiyaye su inda kai dan Shi’a ne. Saboda haka kira na ga ’yan harka da su kiyaye wadannan dokoki da dokokin qasa sau da qafa.
 
Haka nan muna godiya ga malaman Dariqar Tijjaniyya irin su Malam Halliru Maraya da Sheikh Dahiru Bauchi, da kuma malaman Dariqar Qadiriyya irin su Sheikh Qasiyuni da dan uwansa Sheikh Abduljabbar da makamantansu, wanda yake dukkaninsu ’yan uwanmu ne a tafiya daya, kuma yawanci abokai sahihai nagari, wanda babbabn hadafinmu shi ne hada kan mabiya Ahlulbait (as), Tijjaniyya Qadiriyya da sauran mabiya Ahlulbaiti daga Shi’a musamman ma Haidar Center kusan fatanmu ke nan kullum a samu hadin kai, ta yadda za a dinga ziyartar juna, misali gobe za a gayyace ni don in ziyarci wazifa a Tijjaniyya, jibi za a gayyace ni don in ziyarci zikiri a Qadiriyya, kuma duk in halarta. Saboda wuri ne na Zuriyyar Ahlulbaiti (as). Lallai muna godiya sosai da abin da suka yi, kuma yana nuna cewa su Musulmi ne na qwarai, wadanda suke ganin cewa wajibi ne kare jini da dukiya da mutuncin duk wani Musulmi. Kuma har ila yau, abin da suka dauka na matsaya,  na ganin cewa sun ji haushin abin da ya faru, dama wannan shi ne abin da ya kamata kowane Musulmi ya yi. Muna jinjina mu su a kai. Muna gode mu su da wannan dattako da suka yi. Kuma muna roqon Allah ya qara mu su qarfin gwiwa a kan wannan ’yan uwantaka da suka nuna.
 
Kuma ina jan hankalin sauran Musulmi baki daya da malamansu, su dauki mataki irin wannan na juyayin abin da aka yi wa ’yan uwansu Musulmi, domin gobe ta iya yiwuwa ta kanka za a fara. Sannan kuma wani abin mamaki shi ne, da a ce Wahabiyawa za su gama da duk ’yan Shi’an duniya da ’yan Dariqun duniya, to da su kansu Wahabiyawan ba su zauna lafiya ba. Saboda su ma sai an gwara kansu su yi ta kashe junansu. Ba za su taba zama lafiya ba su ma.
 
Muna ga yadda Izala take a da, irin gwaren da suka dinga yi a tsakaninsu. Saboda haka meye amfanin su ce sai sun ga bayan al’ummar Musulmi wadanda ba su da ra’ayi irin nasu? Allah ya sa mu dace.288