Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA
Alhamis

30 Yuni 2016

18:45:09
763335

Cibiyar Ahlul-Baiti{a.s} ta Duniya ta Bukaci Al’ummar Musulmi da su Fito Ranar Quds.

Ranar Quds ta wannan shekara na zuwa a lokacin da al’ummar musulmin Duniya ke fuskantar matsaloli da musifu daga manyan Kasashe na Duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-cibiyar Ahlul-Baiti ta Duniya ta fitar da wani sako inda ta bukaci al’ummar musulmin Duniya da su fito kwansu da kwarkwata ranar Juma’a ta karshen watan Ramalana domin nuna goyon bayan su ga al’umma Palastinawa wadanda suke cikin danniya da zalunci na haramtaciyar kasar Isra’ila wanda ya kwashe tsayon shekara da  shekaru amma manyan kasashen Duniya sun saka ido suna kallo da kuma nuna goyon baya ga haramtaciyar kasar Isra’la.

Ita dai rana Quds Imam Khumaini ne{r} ya assasata a dukka nin Juma’ar karshe ta watan Azumi domin hadin kan musulmin Duniya da kuma nuna goyon baya ga al’ummar Palastinawa.288