Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Mu'assasatu thaqalain
Alhamis

28 Afirilu 2016

11:58:10
750564

CIKAKKIYAR HIRAN JARIDAR RARIYA DA SHAIKH HAMZAH MUHAMMAD LAWAL DANGANE DA ZUWAN SHI JUDICIAL COMMISSION OF INQUIRY Daga Yusuf

A asali shi wannan dan jarida na Rariya yace ne zai yi hira da Shaikh Hamzah ne akan zuwan sa JCI da kuma dalilin zuwan sa komitin,kuma akan haka yayi hiran amma sai ya yiwa labarinsa taken da bai dace ba da hiran ba wanda yana daga cikin dalilan da yasa ba kasafai Malam yake hira da yan jarida ba. Samsam abinda yace Malam ya fadi a taken labarin sa da ya buga jiya,ba haka malam yace ba akwai gyara.Mai son sanin hakikanin abinda Malam ya fadi zai iya karanta cikakkiyar hiran a kasa.

RARIYA:Mun ji an ce Malam ya bayyana a wannan komiti na binciken rigimar Zariya,ko Malam zai fada mana a taqaice abubuwan da ya gabatar ga wannan komiti?
SHAIKH HAMZAH :A’uzu billahi minash-Shaidanir Rajim,Bismillahir Rahmanir Rahim,Wasallalahu ala Muhammadin wa Alihid Dayyinad Dahirin wa As’habihil Muntajabeen.
A ranar litinin da ta wuce ne na je wannan komiti din,ya kamata da a ce ranar alhamis da ta zo kafin litinin din ne ya kamata in yi nawa bayanin,amma saboda yawan mutane da wasu abubuwa sai ya zama mun samu jinkiri zuwa litinin din.
A takaice abinda na so na nuna ko kuma na nuna a wurin shine tsankwama ga ‘yan shi’a gabaki dayan su suka samu kansu a ciki bayan wannan rikicin na Zariya 12/14 ga watan Disamba 2015 wato shekarar da ta wuce,daya kenan.
Da kuma kokarin karkatar da akalar komiti din da wani ga bangare na musulmi yake so yayi domin cimma manufofin shi da karfi dangane das u ‘yan shi’a din-karkatar da akalar komitin ya tashi daka aikin da aka bashi tun farko wato tun da aka kaddamar dashi zuwa aikin shi shi irin wannan mutanen na nuna cewa ‘yan shi’a kamar wasu ‘yan kungiyar asiri ne ba musulmi bane,ya kamata a kashe su ne,ya kamata a haramta samuwar su a cikin kasa,da nuna hatsarin su da abubuwa da suka yi kama da wannan.To na koka akan wannan,kuma Alhamdulillahi Shugaban komitin yayi kokari ya nuna cewa ba haka suke ba.Na kafa mashi hujja da abinda shi Gomnan ya fada mashi a lokacin da ya rantsar dasu,kuma na kafa mashi hujja da wasu rubuce rubucen gobna din musamman littafin day a rubuta mai suna THE ACCIDENTAL PUBLIC SERVANT wanda a ciki gobna ya dinga nuna cewa shi ba wai bin dan shugaba ko dan siyasa yake ba,ka’idoji da dokoki yake bi.Saboda haka su ma kada su damu da wanda ya kafa su,su ka’idoji da dokoki,su dabbaqa adalci a ciki ba tare da la’akari da wane ne ake bincike ba,adalci shine abinda yafi komai muhimmanci.
To na ci sa’an samun hankalin shi shugaban komitin wanda yayi dogon bayani akan damuwa ta.Kuma yace akan haka suka doru da sauransu.Sannan muka cigaba,na nuna mashi dan kunci da nake ciki da ‘yan shi’a.Sannan na yi kokari na nuna mashi su waye suke so su sanya ‘yan shi’a a cikin wannan kunci da damuwa din,wanda wadannan sune Wahabiyawa,Salafawa masu akidar kafirtarwa wanda a wajen su duk wani wanda ba cikin su yake ba shi ba musulmi bane sannan MURTADDI ne kuma ya fita daga cikin Milla,sannan kuma mai bidi’a ne.To kuma na kafa hujja da littafansu na asali wato littafan Malaman su na asali,sannan nayi bayani me ake nufi da Shi’a,cewa ba yadda ake tsammani bane,tana da asali a addinin musulunci sannan na kawo hujjoji a taqaice tun dab a lokaci sosai da wannan.
Sannan nai magana akan tawaye wa kasa wanda ake so a zargi shi’a.Nayi bayanin iyakar Constitution,cewa shi yarjejeniya ne tsakanin ‘yan kasa da yanda ya kamata suyi mu’amala da junan su,iyaka nan iyakar shi,bai da dangantaka da addini domin bai iya warware min matsaloli na na addini,bai iya warware min tambayoyi na addini saboda haka ba ni kadai bad an shi’a ba kowanne musulmi akwai inda yake nemo amsoshin tambayoyin shin a addini,ba ma musulmi kawai ba har da kiristoci da darikokin su daban daban a cikin kiristanci din kowa akwai inda yake zuwa ya nemo abinda addinin shi yayi mai bayani akai.Sannan ba aganin shi a matsayin tawaye ma tsarin mulki ko kasa,to da ire iren wadannan abubuwan.Da kuma irin tambayoyin da suka yi min da kuma amsoshin da na basu.Daga karshe kaman sun dan gamsu da abinda na fada masu saboda sun ce jawabin da nayi din in sawo masu shi a rubuce suna so su amfana dashi a wurin shawarwarin da zasu ba da na karshe.To ka ji abinda ya faru a taqaice.
RARIYA:Gabanin ka Shaikh Sale Zariya shima ya halarci wannan komiti ya bada nashi bayanin,a hannu guda su kaman almajiran Shaikh Zakzaky wato bangaren su su basu ce komai ba akan wannan ba,wannan an samu wasu wadanda suke ganin cewa kaman akwai rarrabuwan kawuna tsakanin ‘yan Shi’a
SHAIKH HAMZAH:A ‘a,wannan bai da dangantaka da rarrabuwan kawuna.Su ‘yan uwa Musulmi,sune abin ya shafa kai tsaye kuma a kungiyance ne suka dauki wannan matakin cewa ba zasu je wannan komitin ba,saboda tun daga asali suna ganin ba za a masu adalci ba domin komitin bai hadu daidai ba,sannan kuma  suna da sharuddan da suka kafa.Ka ga wannan ba zaka iya sa baki a ciki ba ai?Bai da dangantaka da rarrabuwan kawuna,mataki ne wanda suka dauka a siyasance wanda suke ganin zai sa matsi akan shi komitin da kuma gomnati ma,sannan zai jawo masu tausayi daga wajen mutane,ko daidai su kayi ko ba daidai su kayi ba,mataki ne wanda su suka dauka,bai da dangantaka da cewa su ‘yan shi’a ne ko ba ‘yan shi’a bane balle a ce ‘yan shi’a kansu a rarrabe suke.To sauran mutane wadanda suka je mahangar su kenan,ka gani ?to shi yasa ka ga haka.Mataki ne wanda suka dauka kuma ra’ayin su ne sukai wannan,sannan kuma basu hana wani ya je ba,kuma kila nan gaba in suka ga dama su je kafin komitin ya gama aikin shi wato idan suka ga dama suka canja ra’ayin su saboda yanda suke ganin yana tafiya zasu iya canjawa.To ka ga bai da dangantaka damu ai sannan bai da dangantaka da kowa ko da ba ‘yan shi’a bane saboda irin wannan abinda aka yi masu ya kamata a kalle shi sosai ba tare kallon cewa yan shi’a ne ko ba ‘yan shi’a bane.
RARIYA:Bayan rikicin Zariya din an ce kayi wani bayani,kuma an ce ka siffata wadannan wadanda suka tare sojoji da AREA BOYS wato tsageru,menene gaskiyan maganan?
SHAIKH HAMZAH:Nayi jawabi kuma yana nan an dauke shi,saboda haka ba wahami bane ,ko wani abu wanda mutum zai yi karya akai,za a iya komawa a ji abinda na ce.Na auna abinda ya faru ne akan yanda ya faru,kuma akan labarun da suka zo mana a lokacin,na ga kurakuran sojoji,sannan na ga kurakuran su ‘yan uwan,sannan na ba da shawarwarin abinda ya kamata,kuma nace kofofin mu a bude suke idan suna neman shawarwarin mu za mu iya basu shawarwari.
Wannan batun area boys din,wadannan wadanda suka tsaya suna rigima din da sojoji sun yi kama da area boys,kuma mu’amalar da sojoji ya kamata su yi da su ita ce mu’amalar area boys.In da zasu yi adalci idan sun saurara jawabin sosai cewa nayi ya kamata sojoji suyi mu’amala dasu irin mu’amalar area boys sai su wuce.To amma wasu kananan yara ne,sannan ko da manya ne ba zai yiwu ya zama suna da wayewar su ga ne abinda na fadi ba domin yana bukatar gogayya,yana bukatar sanin abubuwa masu yawa,sannan yana bukatar zuciya budaddiya.In mutum ya riga ya maka hukuncin karshe, to baka da magani tunda ba ka yi bane don kana so ya yabe ka ba.Kana da kuma ‘yancin ka karanci abu yanda ka gan shi da hankalin ka,hankali na ne nayi amfani dashi na karanci yanayin na bada shawarwari na akai saboda ina da ‘yanci,kuma kowa ma ‘yanci ya fadi nashi ra’ayin da ya fahimta.
RARIYA:Dalilin wannan komitin shine bincike akan akan rikicin Zariya amma wasu jama’a da yawa na ganin kamar ba za yi adalci ba,me Malam zai ce dangane da wannan?
SHAIKH HAMZAH:Wannan shine abinda na fadakar da akan cewa ko da akan haka aka tafi daga farko,to su komitin su fi karfin wadanda suka kafa su,kuma sun yi alkawarin zasu fi karfin shi din,sannan mun fadi abubuwa suna faruwa.Jiya nayi amfani da wasu jumlolin turanci guda biyu,nace masu muna so mu ga THE PROOFS OF THE PUDDING,sannan nace mashi WE WILL SEE IT WHEN YOU FRIED THE EGGS.Abinda ake ce ma “Proof of the Pudding”-akwai karin magana a kowane yare wato PROVERB-wato ba zaka iya yin hukunci akan abu ba sai ka jaraba shi a taqaice kenan a hausa.Sannan nace muna so mu ga wannan gwajin ne a lokacin da suka yanke hukunci,suka bada shawarwarin su,a lokacin ne za a yi hukunci akan su.Ko da ce ba don suyi daidai aka sasu ba,to su yanzu sun fi karfin wadanda suka sasu din kuma ya lura da wannan ya fadi haka.To kuma yanda muka abin na tafiya da kuma yanda duk idanun duniya suke akan komitin ina tsammanin mutumin da yake da mutumci-in da kana da mutumci ka zo cikin komitin ka da ka yarda ka zubar da mutumcin ka gabaki daya ta hanyar yin abin da bai da kyau.
Mutane suna bukatar su ta sa masu wannan matsin sosai,kowa da kowa a ta sa masu matsi saboda a taimaka domin ana so ne a ga wannan abin an warware shi,kuma kowa na da hakki domin a ga an warware shi.A taimake su su din ma domin su yi abin da yake shine daidai,wannan shine dalili
RARIYA:Wasu na ganin wannan abin da ya faru kaman sojoji sun daidai,me Malam zai ce akan wannan?
SHAIKH HAMZAH:A asali daman bai kamata a yi amfani da bullet ba,sannan kuma mutum ya kasa fahimta har zuwa yau me yasa aka yi amfani da bullet din.Mecece dangantakar Husainiyyah da Gyellesu?Sai da abinda ya faru a Husainiyya da awowi sannan aka je Gyellesu,kuma a Gyellesu aka yi kwana biyu?nan awowi aka yi wanda nan ne wurin da rigima ta faru.To amma Gyellesu da aka je sai aka yi kusan awa arba’in ana yi.To ka ga a cikin abin akwai alaman rashin tunani,shi yasa nake ganin kaman kila sojojin sun fada tarkon wasu-haka nake sawwalawa domin in basu dama cewa akwai wasu mutane wadanda suke da matsala dashi Malam din a Zariya ko a wajen Zariya wadanda suka yi amfani da abinda ya faru a Husainiyyah domin su warware wannan matsalar tasu ta gaba da Malam din,sai suka yi amfani da sojoji.
Amma sojojin sun yi babban kuskure har daga karshe suka fada.A komitin na fada cewa babban kuskuren da soja suka yi a boko haram shine kashe Muhammad Yusuf alhali sun kama shi da rai da lafiya saboda kowa ya ganshi yana da ranshi da lafiyan shi kuma bai da ciwo a jikin shi,amma kawai a hannun hukuma sai aka kashe shi da harbi.Irin wadannan kurakuran bai kamata a dinga maimata su kowaye ne aka yi ma wa.Ina da bambamci na akida da mahanga da Muhammad Yusuf wannan kuma ba zai rufe min ido ya zama na ce ko naji dadin abin da ya same shi ba.Sannan ko shi kanshi Malam Zakzaky a lokacin da aka kashe Albani in ka tuna,yayi maganganu masu kyau dangane da Albani.To!haka ya kamata mutum ya kasance,ka da wadannan ra’ayoyin suna mutum ya zama dan Adam.
RARIYA:Sai ga shi kotun duniya wato ICC an ce akwai yiwuwan ta gayyaci Buhari da Burutai wanda su ‘yan uwa mabiya Malam Zakzaky suka kai kara,yaya Malam yake ganin wannan al’amari?
SHAIKH HAMZAH:Kotun duniya abin da take bincike akan shi,akwai abinda ake ce ma GENOCIDE,akwai abin da ake ce ma WAR CRIME,sannan akwai abinda ake ce CRIME AGAINST HUMANITY,wato kenan yakin kare dangi shine abu na farko.Ka kashe mutane gabaki dayansu saboda su mutanen sune su wato baka son irin wadannan mutanen ya zama akwai su a doron kasa,daya kenan.Na biyu kuma laifuffukan yaki,ana yaki a cikin duniya amma yaki na da dokoki da ka’idoji.To idan aka yi yaki aka samu an karya wadannan dokoki da ka’idojin to wani abu ne wanda kotun duniya ke bincika.
Sannan na uku shine HUMAN RIGHT VIOLATION,ya zama cewa take hakkin yan Adam a cikin.To wadannan abubuwan da suka faru zaka iya sasu a karkashin daya cikin wadannan manya manyan dalilai guda uku wa’yanda na ambata a baya.Kuma da gaske ya kamata su je kotun duniya din.Kuma su kansu ‘yan uwan wato ‘yan harkan Musulunci a ce tun farko suna da tunani day a kamata su fahimci hakan ba sai wasu daga waje sun fahimtar masu.Cewa ko ba dade ko bajima irin wannan abin ko shekara nawa aka yi za a iya kama mutum kuma ko da ya mutu ne,ka ga shugaban Yogoslabia,a kwanan nan akwai wanda aka daure shekara arba’in kuma shekaran sa saba’in a duniya wato ya sakankance har ga Allah zai mutu a prison.Amma kafin a kawo haka a yanke masu hukunci ya dauki kaman shekara ishirin .
RARIYA:Sakamakon wannan rikici da abubuwan da suke faruwa mutane da yawa musamman matasa suna ta bincike akan wai mecece wannan shi’a din,sannan irin bayanan ka suna sabawa da ayyukan wasu yan shi’a din,to wacce shawara Malam zai ba su irin wadannan mutanen?
SHAIKH HAMZAH:Idan mutum yana neman gaskiya,ya kamata ya san ita gaskiyan kafin ma’abutan ta.Imam Ali (as) yana cewa “KU SAN GASKIYA SAI KA SAN SU WAYE AHALIN TA”-wato ka da ka dinga auna gaskiya da mutane,ka dinga auna mutane da gaskiya ne.Ka nemi gaskiya ba ruwan ka da mutum,idan ka nemi gaskiyan ka gane ta,to sai ka ga wane ne baya a karkashinta,ba ruwanka da kowa.Duk wanda ya saba sai ka saba dashi ba tare da mutum yace wannan dan shi’a ne ko dan sunnah ne ko dan kaza,wadannan sunaye ne da mutane suke ba kansu amma ita gaskiya aiki ce.
To wannan abun da ya duk da yake abu ne nab akin ciki zai iya zama alheri ga shi’a daga karshe amma ya danganta daga su ‘yan shi’an ya suka yi mu’amala da rikicin.Su matasa abinda ya kamata suyi shine su binciki gaskiya domin haka yake da kyau,saboda irin wannan abin ya riga ya faru ya zama hujja akan mutane.Sunan shi’a ko da alheri ko sharri ya shiga ko’ina,ko’ina shi’a shi’a.Saboda haka yanzu mutum bai da hakkin yace bai san shi’a ba,tunda ya ji sunan shi’a ya kamata ya bincike ta ya gani ya take.
Yanzu ba ma so mu ce gaskiya ce ko ba gaskiya bace,mutum da kanshi ya kamata ya bincika,idan ya gano sai ya bi ta a yanda take ba a yanda shi yake so ba,matsalar kenan,yin ta a yanda take ba a yanda yake so ya zama ba.288