Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HAUSA.IR
Alhamis

3 Disamba 2015

16:13:46
722874

An Gudanar Da Juyayin Arba'een Din Imam Husain (a.s) A Karbala Ta Kasar Iraqi

Miliyoyin musulmi daga sassa daban daban na duniya suke gudanar da juyayin arbaeen na shahadar Imam Husain (a) a haraminsa da ke karbala a kasar Iraqi

Ruhotanni sunce an karfafa matakan tsaro a dukkan wuraren da masu juyayin su kayi dafifi don tabbatar da cewa babu wata matsala da zata kunno kai dangane da lafiyarsu.

Wasu labarai sun bayyana cewa jami’an tsaron kasar ta Iraqi sun sami nasara dakile wani kokarin da yan ta’adda suka yi a jiya na kai harin kan masu tattaki zuwa haramin na karbala.

Miliyoyin mabiya mazhabar Ahlul-baiti{a.s} da kuma na sunna har ma da wasu kiristoci suna shiga cikin jerin masu juyayin shahadar Imam Hussain (a.s) jikan manzon Allah(s.a.w.w) wanda yayi shahada a shekara ta  1376 da suka gabata a ranar 10-Muharram..288