Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Lahadi

29 Nuwamba 2015

16:08:25
722154

Masu Tattakin Arbaeen a Nageria sun tuna da shahidan Tattaki

A yau Lahadi 29g watan Nuwamba 2015 ne daidai da rana ta hudu ta Tattakin da ak somo daga yankin Kano dubun dubatan masu Tattakin na Arbaeen suka tsaya tsaya a daidai inda aka samu shahidan Tattakin Arbaeen na shekara ta 2012 watau shekaru uku ke nan da suka gabata, inda aka yi musu Addu'a

Su dai wadannan Shaidai Muhammad Jawad Kabir da Husain Ishaq Gano dukkanin su matasa ne 'yan makarantar Fudiyyah sun yi shahada ne sakamakon wata mota data bi ta Kansu a lokacin Tattakin wanda yayi sanadin shahadar su bayan nan. 

Malam Muhammad Turi yayi musu addu'a sannan ya roki Allah Ta'ala da ya taraita su a cikin ladan wannan Tattakin na Arbaeen.

Haka nan kuma yayi addu'a ga iyayen su da sauran al'ummar musulmi.

In ba'a manta ba a shekarar 2012 ne a lokacin Tattakin Arbaeen aka sami wani mummunan hadari akan hanyar masu tattaki daga Kano zuwa Zariya inda wata mota kirar GULF ta hau kan yan uwa goma sha bakwai, wanda yayi sanadin shahadar yaran su biyu.

Allah ya karbi shahadar su ya tayar da su tare da Sayyidush shuhada Imam Hussaini[AS].288