Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Laraba

25 Nuwamba 2015

18:21:18
721558

Dalilin mu na yin Tattakin munasabar Arbaeen - Takardar manema labarai

Ranar 20 ga watan Safar na shekarar 1435 bayan hijira, tana alamta cikan kwanaki 40 cif da shahadar Imam Husain (AS), Jikan Ma’aikin Allah Annabi Muhammad (SAWA). Imam Husain (AS) ya yi shahada ne a wannan ranar tare da iyalansa da kuma daukacin mabiyansa a hannun azzalumin basaraken Umayyawa

 

Ranar 20 ga watan Safar na shekarar 1435 bayan hijira, tana alamta cikan kwanaki  40 cif da shahadar Imam Husain (AS), Jikan Ma’aikin Allah Annabi Muhammad (SAWA). Imam Husain (AS) ya yi shahada ne a wannan ranar tare da iyalansa da kuma daukacin mabiyansa a hannun azzalumin basaraken Umayyawa Yazid Dan Mu’awiyya a shekara ta 61 bayan hijira, a Karbala da ke cikin kasar Iraki.

Jama’a daga kusan dukkanin kasashen musulmi na duniyar nan suna yin wannan tattakin zuwa hubbaren Imam Husain (AS), domin su nuna alhininsu da kuma girmamawarsu ga wannan Jika na Ma’aikin Allah (S). Yawan masu wannan haduwa ta sa shafin tattara bayanai na “Wikipedia” ya bayyana taron Arba’in na Imam Husaini (AS) da ake yi a Karbala da cewa yana daya daga cikin manyan tarukan da ke hada al’umma mafiya yawa a wannan duniyar tamu.

DON ME MUKE YIN MAKOKIN ARBA’IN?

Annabin Allah (SAWA) Yana cewa, “Kasa tana yin makokin mutuwar duk wani mumini har na kwanaki arba’in”. Imam Hasan Al-Askari (AS) ya bayyana cewa, alamar mumini ne mai imani na gaskiya, lizimtar ziyarar Arba’in. Wannan ziyara dai kamar yadda muka sani, tana alamta girmamawarmu ne ga shuwagabanninmu, gwarazanmu kuma ababen koyinmu. A bisa wannan dalilin ne kuma wasu daga cikin ’yan uwa ma’abota Harkar Musulunci daga wannan kasa tamu suka shiga cikin jerin miliyoyin jama’ar da suke yin wannan tattaki zuwa Karbala.

FALSAFAR TATTAKIN ARBA’IN

Imam Muhammad Bakir (AS) yana cewa; “Sama ta yi kuka kan kisan Imam Husain (AS) har na tsawon kwanaki Arba’in, ta rika fitowa Ja, ta kuma rika fafuwa Ja”. Bisa al’ada duk abin da aka dawwama ana yi na kwanaki arba’in, to yakan zama hali da dabi’a na mai yin sa a tsawon rayuwarsa. To, don me za a ce kwanaki arba’in? To, a tuna Annabi Nuhu (AS), ya tsartar da rayuka ne daga halaka a zamanin ruwan Dufana a cikin kwalakwalensa, ya rika tafiya a kan ruwa ba dare ba rana har na tsawon kwanaki arba’in, kamar yadda Alkur’ani ya bayyana mana. Haka abin yake ga Annabi Musa da jama’arsa, sai da suka shafe shekaru arba’in suna bugawa nan su buga can a cikin jeji, kafin su cimma kasa mai tsarki, watau alkaryar da Allah ya yi masu alkawari a wancan lokacin.

Don haka mu a nan a duk kwatankwacin wannan lokacin mukan yi wannan tattaki ne domin mu tunatar da kawukanmu abin da ya hau kanmu na tsayuwa da dakewa a kan gaskiya komai dacinta, da kuma tawayenmu ga duk wani azzalumi da tsarin karya da zalunci a kowane mataki na rayuwarmu. A takaice a nan muna shelanta wa duniya duka cewa, mu rayuwarmu kacokaf ta doru ne a bisa koyarwar Imam Husain (AS), na tsayuwa da dakewa a kan gaskiya da kuma tunkara da kalubalantar azzalumi ko wane ne shi, kuma komai matsayinsa, kamar yadda muke sauraron bayyanar Limamin shiriya wanda zai kawo karshen karya da zalunci a doron duniyar nan tamu, Imam Mahadi (AS).

MANUFAR LIZIMTARMU GA YIN TATTAKIN ARBA’IN

Babbar manufarmu da yin wannan tattakin mu a nan gida, shi ne mu nuna alhininmu da kuma girmamawarmu ga Hubbaren Jikan Ma’aikin Allah, Imam Husain (AS) da ke Karbala. Wannan kuma wata hanya ce ta nuna zahiri da badinin juyayinmu na rashin wannan babban Shugaba Jikan Ma’aikin Allah (AS), Imam Husain (AS), da duk wadanda aka yi masu kisan gilla a tare da shi.

WADANDA SUKA ASSASA YIN TATTAKIN ARBA’IN

Jabir bin Abdallah Al-Ansari, Sahabin Ma’aikin Allah (SAWA), yana daya daga cikin wadanda tarihi ya ruwaito da fara yin wannan tattakin a shekara ta 61 bayan hijirah, ya zuwa inda aka rufe Imam Husain (AS). Wannan ziyarar da Jabir bin Abdallah Al-Ansari ya kawo ta yi daidai da lokacin da wadanda suka saura daga Iyalan Ma’aikin Allah suka kawo ziyarar ga wannan makwanci na Imam Husain (AS), a karkashin jagorancin magaji kuma Dan Imam Husain (AS), Imam Aliyu Zainul Abidin (AS), wanda jim kadan kafin wannan lokacin, azzalumin Shugaban wannan lokacin Yazid Dan Mu’awiyya yake tsare da shi a Damascus.

Tattakin Arba’in wani yanki ne na juyayin Ashura. Tasowarmu da yin wannan tattaki daga shiyyoyi daban-daban na kasar nan, kamar wadanda suka taso daga Kano, Kaduna, Pambeguwa, Malumfashi da sauransu. Muna kara tunawa kawukanmu ne irin wahalhalun da Imam Husain (AS) da jama’arsa suka dandana a falalen jejin Karbala. Haka nan wannan tattaki namu tunawa ne da kamu, tilastawa da kuma jan Iyalansa mata da dan karamin dansa marar lafiya a wulakance, cikin kunci da wahala babu mai ko takalmi a kafarsa cikin rairayi mai dauke da matsanancin zafi tun daga wannan fili na Karbala har ya zuma Damascus. Ta hanyar wannan tattaki namu, muna kara tuna wa al’ummar musulmi muhimmin sakon da Imam Husain (AS) ya bar mana a wannan shahada tasa, kamar yadda kanwarsa Sayyidah Zainab (AS) ta ci gaba da shelanta wannan sakon a birane da kauyakun da mugayen fadawan Yazid suka rika bi da ita a matsayin kamamma.

MU FA KARA SANIN WANENE IMAM HUSAIN (AS)

Imam Husain (AS) Jikan Ma’aikin Allah ne (SAWA), Dan Imam Ali (AS) kuma Dan Diyar Ma’aikin Allah, Sayyidah Fatimah (AS). Yana daya daga cikin ma’abota falalan nan na cikin mayafi, kamar yadda ya zo a mashahurin hadisin nan na Kisa’i. Imam Husain (AS) yana daya daga cikin tsarkakan iyalan gidan Ma’aikin Allah, wadanda Allah Madaukakin Sarki ke cewa dangane da martabarsu; “ …Allah Yana nufin Ya gusar da duk wata kazanta ne daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida! Ya kuma tsakake ku tsarkakewa.” Yana daya daga cikin iyalan Ma’aikin Allah wadanda Allah Ya umurci al’umma baki daya da ta nuna masu kauna da yin biyayya a gare su a cikin ayar da aka san ta da ayar nuna so da kauna “Mawaddah” aya ta 23 a cikin sura ta 42: Allah yana cewa; (Ya Muhammad), ban tambaye ku da ku biya ni wata lada ba (a kan shiryatar da ku ta hanyar isar da sakon Mahaliccinku a gare ku), face dai neman ku da nuna kaunarku ga makusanta na (Iyalan gida na). “Duk wanda ya aikata kyakkyawa, za mu (Allah) kara masa a kan kyakkyawan aikinsa. Tabbas Allah mai yawan gafara ne mai yawan jin kai.” Don haka kamar yadda muke dabbaka wannan tattaki ya zuwa Karbala, muna amsa kiran Imam Husain (AS) ne, a lokacin da ya tsaya yana mai fuskantar wannan babbar rundunar zaluncin da ke gabansa shi kadai, yana mai kira da madaukakiyar muryarsa: “Hal min nasirin yansuruna, (ko akwai wani mataimakin ya taimaka mana)?” Don haka a nan gabaki dayanmu muna masu amsa wannan kira da mika wilayarmu, LABBAIKA YA HUSAIN! LABBAIKA YA HUSAIN!! LABBAIKA YA HUSAIN!!!

AbdulHamid Bello A madadin ‘Yan Uwa Musulmi na Nijeriya Safar 21, 1437 (December 3, 2015)288