Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ASSAQALYN
Lahadi

11 Oktoba 2015

06:47:46
714591

AN GUDANAR DABABBAN TARON BABAN EIDIN GADEER AGARIN KADUNA

AN GUDANAR DA BABBBANR TARON EI EIDIN GHADEER DA CIBIYAR SAQAFAR SAQAKALYN TA GUDANAR A GARIN KADUNA KARKASHIN JAGORANCIN SHAIKH HAMZA MOHAMAD LAWAL

GHADEER 1436-2015,BANGARE NA 1 WAJIBCIN RIKO DA IMAM ALI DA A’IMMAH (AS) A BAYAN MANZON ALLAH (SAAW) NA MAULANA AL-MUJAHID SHEIKH HAMZAH MUHAMMAD  LAWAL (AMA) YUSUF SULAIMAN NE YA RABUTA

A’UZU BILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJEEM BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM WASALLALLAHU ALA MUHAMMADIN WA ALIHID DAYYIBINAD DAHIREEN ALHAMDULILLAHIL LAZIY JA’ALANA MINAL MUTAMASSIKINA BI WILAYATI ALI BIN ABI TALIB ALAIHIS SALAM . Yanayi ya riga ya sanar da kanshi,cewa mun taru ne domin taya juna murna dangane da Eideen Wilaya ,Eideen Ghadeer Al-Agar .Ba wai domin cewa a ilimin Allah Subhanahu wa Ta’ala bid darura cewa dole yau ta zama 18 ga watan Zulhijjah ba,saidai domin cewa muna cikin yanayin ne da kuma zamanin.Tabbas tabbas muna cikin yanayin saboda AL-KADARUL MUTAYAKKAN shine muna cikin Zulhijjah,sannan kuma mun wuce goma gare shi ,ko yau ko gobe sha takwas ,ALAL AZ’HAR gobe .Mun taru yau saboda muna da karatu gobe ,so kila zai wahala gobe ya zama mun yi munasabobin guda biyu a lokaci daya ya zama mun yi majalisin Ghadeer,sannan kuma da la’asar muje mu yi karatu shi yasa ya zama muka zo dashi yau . Imam Ali Alaihis Salam,ya kamata ace a bayyane yake cewa shine ya cancanci ya gaji Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Alihi wa Sallam a dukkan janibobi na wazifofi na shi Manzon Allah(saw) din banda abinda hankali da kuma shi Manzon Allah ya kebe,wanda shine karbar wahayi .Cewa Imam Ali (as) shine ga Manzon Allah(saw) kwatankwacin Harun ga Musa saidai cewa babu Annabi a bayan shi Manzon Allah(saw) .B a ma ganin akwai wajibcin bijiro da dalilai akan haka saboda wadatuwar su dalilan da kuma yawan maimaita su,saidai kawai domin neman albarka,amma ba wai domin bid daruwa kafa hujja ba . A lIttafan Ahlus Sunna wal Jama’a akwai riwayoyi wadanda suke basu da iyaka ,ya ishe ka ka sani cewa Imam Ahmad bin Hanbal yace “BABU WANI DAGA CIKIN SAHABBAN MANZON ALLAH (SAAW) WANDA FALALOLI SUKA GANGARO DANGANE DASHI KAMAR YANDA YA GANGARO DANGANE DA ALI ALAIHIS SALAM”.Kuma wannan fadin na Imam Ahmad bin Hanbal akwai shi a cikin FATHUL BARIY na Ibn Hajar  Al-Asqalani  a lokacin da yake magana akan fada’il din Imam Ali,har Ibn Hajar yayi kokarin yayi bayanin mai yasa haka din,mutum zai iya duba wa a wurin .Ba dole ya zama mun karbi jawabin Ibn Hajar din ba amma dai akalla muna so mu ce a wurin Ibn Hajar din ma hakika ce tabbatatta .Sannan banda Imam Ahmad bin Hanbal da kuma Shaarihin Sahihul Bukhari akwai malamai na sunnah wadanda suke masu yawa wadanda suka yi I’ITIRAFI da wannan hakikan.Wannan Fada’il kenan,wato babu wanda aka ambaci falaloli akan shi kamar yanda aka fadi akan Imam Ali(as).Amma kuma akwai KHASA’IS  wadanda shi Imam Ali ne kadai ya kebanta dasu .Daga ciki akwai wannan: wannan dalilin wanda domin shi muka taru a nan na gadon Manzon Allah (saaw),saboda kamalolin shi ZATIYYA daga farko tukuna,da kuma I’IDADI daga Allah ta’ala wato tanajin da Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi mashi ta hanyar Manzon Shi  wanda masoyi da abokin gaba duka gabaki daya sunyi I’itirafi da wadannan.Wadannan ina fadi ne saboda babu bukatan kawo dalilai akansu .Da sauri mutum zai iya tunawa UMUMAN dangane da Ahlul Bait Alaihimus Salam irshadoji daga Manzon Allah (saw) ,kamar inda Manzon Allah yake cewa : “TAURARI SU LAMUNI NE GA MA’ABUTA SAMA DAGA BACEWA ,SU KUMA  AHLUL BAIT DINSHI AMANA NE WATO  LAMUNI NE GA MAZOWA KASA DAGA SAMUN SABANI”.Wannan MADMUNIN riwaya yana da muhimmanci sosai cewa Manzon Allah (saw) ya sanya al’ummar Shi ta zama cewa tana kewayawa akan markazi wanda yake shine Ahlul Bait (as).In mutum bai fahimci ma’anar wannan riwayar ba kila ba zai fahimci kowanne irin riwaya ba Asasan .Cewa Ahlul Bait Alaihimus Salam sune lamuni ga al’ummar Manzon Allah (saw)daga sabani-wato muna so mu kawo hujjoji na gamagari kenan kafin muyi  ZOOMING  akan shi Imam Ali (as) bil-kusus-wato matukar al’umma ta kewaye Ahlulbait UMAMAN ba tare da la’akari da janibin wilaya ko shugabanci ko abinda yayi kama da wannan .Idan al’umma ta kewaye Ahlulbait to zata samu lamuni daga sabani ba zata saba . Sannan kila zamu iya tunawa da hadisin Thaqalain,wanda shi kuma ya lamuntar da al’ummar daga bata kamar yanda hadisin taurari ya amintar da al’umma daga sabani shi (wadannan kalmomin suna da muhimmanci ),to shi kuma hadisin thaqalain ya lamuntar ya amintar da al’umma daga bata da sharadin bin Ahlulbait ,idan al’umma ta bi Ahlulbait to ba zata bata ba wato sune sharadi.Akwai inda yake cewa MA IN AKHASTUM ko MA’IN TAMASSAKTUM BI HIMA da sauran na’o’I da sigogi daban daban na riwayoyin hadisin thaqalain ko thiqlain  da ma’anar cewa idan al’umma ta bi A’immah ba zata bata ba sam sam ,kenan in tabi A’immah da Alkur’ani a lokaci guda.Idan ta rike  Alkur’ani  da kuma rike A’immah to ba zata bata ba.Abinda yasa a yanzu mutane Alkur’ani baya yin tasiri akan su wato bai kare su daga sharrace sharrace da masifu da fitintuni,alhali wannan Alkur’anin shine wanda yake a lokacin Manzon Allah(saaw),kuma yake a lokacin Sahabbai kuma yake a farkon Musulunci ,abinda yasa Alkur’ani bai aikata wannan aikin a cikin mu kamar yanda ya aikata a cikin wadanda suka gabace mu, shine rashin dabbakawa wato TADBIQ . A lokacin an sanar damu cewa idan ayoyi suka sauka akan Annabi ya kan umurci Sahabbai su dabbaka ,Yana karantar dasu su haddace,sannan sai su aikata abinda yake cikin ayoyin,sannan sai wasu su sauko a gaba saboda haka wannan dabbakawa din da suke yi ma ayoyin Alkur’ani shine asirin da ya sanya Alkur’anin ya dinga yin tasiri,ya kuma sa ya zama kariya gare su a abokan husuma da abokan gaba da sauran su .To shi Alkur’anin ya umurce mu akan mu bi Ahlulbait  a wurare da yawa,sannan Manzon Allah (saw) shima yayi haka,saboda haka da a ce muna dabbakawa da zai zama muna ganin amfanonin shi Alkur’anin a tare damu . Sannan Manzon Allah (saaw) ya fadi abubuwa masu yawa,zan iya kara guda daya kawai yana cewa : “WANDA YAKE SO YA RAYU IRIN  RAYUWATA  YA MUTU IRIN MUTUWA TA SANNAN YA ZAUNI ALJANNA WADDA UBANGIJINA YA DASA DA HANNUN SHI TO YA JIBINCI ALI (AS) DA A’IMMAH A BAYA NA”.Baka bukatan abinda yafi wannan fitowa fili daga cikin irshadojin Manzon Allah (saaw).Kuma gabaki daya ba ina fadin abinda Shi’a suka ce bane,abadan ba abinda shi’a suke ce kawai bane,wadannan hadisan sanannu ne a wajen Ahlus Sunna wal Jama’a,saidai kila wajen tawili ko taujihi ko tafsir ko abinda yayi kama da wannan da sauransu .Cewa to ya jibanci Imam Ali (as) da A’immah a baya na,yana cewa “RUZIKU FAHMI WA ILMI ma’ana an azurtar dasu fahimta ta da ilimi na wato an basu arzikin wannan,an shayar dasu fahimta ta da ilimi na’.A wasu wurare kari kadan Manzon Allah (saw) yana cewa “kada ku karantar dasu domin sun fi ku sani (wannan hani daga Manzon Allah ),ka da ku shiga gaban su sai ku halaka ,ka da ku tsaya a bayan su sai ku halaka in ji Manzon Allah (saw).” Sannan akwai hadisin “MAN KUNTU MAULAHU FA HAZA ALIYU MAULAHU”. Wannan wani hadisi ne wanda yake a dukkan UMMUHAT din littafan Sunnah,sun rawaito shi ,guda kawai wanda nake so na kawo shine  AL-ALLAMAH SUYUDI a cikin TARIKHUL KHULAFA dinshi,a lokacin da yake magana akan falalolin Ali (as),Ya kawo su da yawa,amma wanda yake da dangantaka da munasabar da muke akai kawai zamu kawo.Yana cewa : “ WA AKHRAJAL TIRMIZIY AN ABIY SURAIHA AN ZAID BIN ARQAM ANIN NABIY SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM QAL ma’ana….. daga Manzon Allah (saw) yace  MAN KUNTU MAULAHU FA ALIYUN MAULAHU wanda duk na kasance maulanshi to Ali ma maulanshi ne.”Wannan jumlar tana da wani irin mikdari na SARAHA yanda yake ma’anar ta ba zata faku ba ga wanda ya ji ta a lokacin da aka fada mashi ita .Babu hadisin da yafi wannan inganci,sannan kuma babu wanda ya fi shi fitowa fili.Kuma a lokacin Hajjin bankwana ne  Manzon Allah (saw) ya fade shi.Kuma ya sha fadi kafin nan.Tun daga farkon MINISTRY dinShi yake fadin wannan,har lokacin da aka zo Hajjin bankwana ya fade shi ta wannan sarahan,wato “DUK WANDA NA KASANCE MAULAN SHI TO ALI MAULAN SHI NE”baka bukatan abin da yafi haka fitowa fili,kamar yanda nake cewa shi yasa saidai ya zama ana tawile tawile ko shiga cikin tafsirai ko taujihohi da sauransu.Cewa to me Maula ke nufi.?Asalin hadisin ba wai ana gardama akan shi bane, kowa ya san cewa Ali shine Maulan wanda Manzon Allah ya kasance Maulan shi,amma meye ma’anar Maula?wannan ba zamu shiga cikin shi ba shima.Ba bukata,saboda bayyanar al’amarin na “TO WANDA NA KASANCE MAULANSHI (da sharadi fa wato wannan jumla  ce ta sharadi) TO ALI (AS) MAULANSHI NE.”Sai Suyudi Ya cigaba da cewa banda Tirmizi : “WA AKHRAJAHU AHMAD AN ALI WA ABI AYYUB AL-ANSARIY WA ZAID BIN ARQAM”wato Ahmad ya fitar dashi daga Ali da Abi Ayyub Ansariy da Zaid bin Arqam(wannan hanyoyin hadisin kenan wato DURUQ din Ahmad bin Hanbal kenan na hadisin )da Amr bin Zimur  da Abi Ya’ala daga Abu Huraira,banda Ahmad bin Hanbal  Dabarani ya rawaito shi daga Ibn Umar da Malik bin Huwail da Jarir da Sa’ad bin Abi Wakkas da Abi Sa’id Alkudriy da Anas da Bazzar daga Ibn Abbas da Ammara da Buraida .Sai ya cigaba da cewa a mafi yawa daga cikin riwayoyin akwai karin ALLAHUMMA  WALI MAN WALAHU WA ADI MAN ADAHU wato Allah Ka jibanci wanda ya jibance shi,sannan kayi gaba da wanda yayi gaba dashi.Sannan ya kawo wata riwaya wanda yake cewa -babu ruwana wannan ya inganta ko bai inganta amma zan karanto saboda  so nake nace wannan itace AQLIYYAH din Ahlus Sunnah wal Jama’a dangane da hadisin Man kuntu Maulahu  - daga Ahmad ibn  Hanbal kamar yanda Suyudi ya rawaito cewa ‘’IMAM ALI (AS) YA TATTARA MUTANE A SHEKARA TA 35 (wato shekarar day a zama Khalifa) SANNAN SAI YACE MASU :INA GAMAD DA KOWANE MUTUM MUSULMI DA ALLAH ,WATO DUKKAN WANI MUTUM MUSULMI WANDA YA JI MANZON ALLAH YACE A RANAR GHADEER KHUM ABINDA YA FADI A RANAR GHADEER KHUM TO YA MIKE YA FADI ABINDA MANZON ALLAH YA FADI DIN ,SAI MUTUNE 30 DAGA CIKIN SU SUKA TASHI SUKA YI SHEDA CEWA MANZON ALLAH(SAAW) YACE “MAN KUNTUMAULAHU FA ALIYU MAULAHU ,ALLAHUMMA WALI MAN WALAH WA ADI MAN ADAHU”.Wanda suke inkarin wannan riwayar daga cikin malaman shi’a zahiran,sun yi inkarin ta ne saboda suna cewa ba zai yiwu Ali (as) ya kafa hujja akan cewa shine maulan mutane ba,yace wanda yake sheda ya fadi .Duk da yake COUNTER ARGUMENT din zai iya yi ne ta babin kafa hujja da ILZAM,wato yana so ya lizamta masu ne da kansu su tashi suyi I’itirafi .Ala kulli hal Malaman Sunnah duk gaba dayan su sun rawaito wannan riwayan na MAN KUNTU MAULAHU  amma dangane da Shi’a mu I’itikadin mu dangane da Ali (as) na me yasa muka nace akanshi muke binshi.Sai mu ce binshi shine bin Allah Subhanahu wa Ta’ala ,bin Manzon Shi sannan akan wannan asasin muke bin shi Ali (as) din,saboda hujjojin da suka bayyana mana .Akwai hadisin da kuka riga kuka sani wanda yake daga A-USULU MINAL KAFI juz’I na 1   a babin IKHTILAFUL HADIS wato babin sabanin hadisi ,hadisin yana da tsawo amma ba laifi kila in ga ko zan iya karanto shi , “DAGA SULAIM BIN QAIS AL-HILALI (wato isnadin ya tuku dashi,shine mubasharatan daga Ali )YACE :NACE MA ALI (AS) NI NA JI DAGA SALMAN DA MIQDAD DA ABU ZARR WANI ABU DAGA TAFSIRIN ALKUR’ANI KUMA NA JI HADISI DAGA MANZON ALLAH (SAW) A WURIN SU UKU DINNAN SABANIN ABINDA YAKE A HANNAYEN SAURAN SAHABBAI KO SAURAN MUTANE -wato a duk lokacin da naji tafsirin Alkur’ani da hadisan Annabi a wajen su ukun nan sai inji ya saba da na sauran mutane-SANNAN SAI NA JI GASGATAWAN ABINDA NA JI DAGA WAJEN SU (su ukun )SABANIN NA SAURAN SAHABBAI –wannan littafin shi’a ne saboda haka hujja akan mu –KUMA NA GA DA YAWA A HANNAYEN MUTANE DAGA TAFSIRIN ALKUR’ANI DA KUMA HADISAI DAGA ANNABI KU KUNA SABA MA MUTANE A CIKIN WADANNAN TAFSIRAN DA HADISAI DIN ,KAI ALI DA KAI DA WADANNAN GUDA UKUN NA GA KUNA SAMA MUTANE A WADANNAN HADISAN DA TAFSIRIN ALKUR’ANI DIN ,KUMA KUNA RIYA WA CEWA DUKKAN ABINDA YAKE HANNUNSU BATA NE (wato ba daidai bane) SHIN KANA GANIN DA GASKE MUTANE GABA DAYA SUNA KARYA AKAN MANZON ALLAH (SAW) NE ?ZAI YIWU ?-Sulaim yake tambayan Ali (AS) MANDIQIYYAN zai yiwu ya zama cewa mutanen gaba daya suna tafiya akan abinda yake ba daidai bane,za su ma Manzon Allah (saw) karya da gangan (MUTA’AMMIDEEN)-KUMA KANA GANIN MUTANEN SUNA FASSARA ALKUR’ANI DA RA’AYOYIN SU? SAI ALI (AS) YA JIYO YA FUSKANCE SHI SABODA MUHIMMANCIN TAMBAYAN DA YAYI MASHI DIN ,SAI YACE MA SULAIM ;KA YI TAMBAYA YANZU KA TSAYA KA FAHIMCI JAWABIN DA ZAN MAKA YANZU.SAI (IMAM ALI ) YACE : LALLAI A HANNAYEN MUTANE AKWAI DAIDAI   DA BATA ,AKWAI GASKIYA DA KARYA ,AKWAI NASIK DA MANSUK ,AKWAI HUKUNCI MAI GOGEWA DA WANDA AKA GOGE ,AKWAI HUKUNCI GAMAGARI DA KEBANTACCE ,AKWAI MUHKAM AKWAI MUTASHABIH ,AKWAI ABINDA SUKA KIYAYE DA GASKE WANDA BASU KUSKURE BA,KUMA AKWAI ABINDA SUNA TSAMMANIN SUN FAHIMTA AMMA BASU FAHIMTA BA ,KUMA HAKIKA ANYI KARYA AKAN MANZON ALLAH (SAW) A ZAMANIN SHI YANA DA RAI HAR SAI DA YA TASHI WATA RAN YANA HUDUBA YACE :YA KU MUTANE HAKIKA KAZZABA TAYI YAWA AKAINA –nace Kazzaba saboda a wata riwayar  tana cewa KIZBA  wato karya da ma’anar MASDAR ,sannan ta zo a wannan da KAZZABA,KAZZABA yana nufi AL-WAHID ALKHASIRUL KAZIB  wato TA din sai ta zama TA ta MUBALAGA ko TA’ANIS ,WATO HAKIKA MAI YAWAN KARYA AKAI NA YAYI YAWA .Idan kace KASURAT ALAIYAL KIZBA,to KIZBA yana iya zama da ma’anar MAF’UL,wato kenan MAKZUB,wato kenan labaran karya  da ake kirkiran su akaina sunyi yawa ,ko kuma ka tafi akan KAZZABA din da ma’anar mai yawan yin karya akaina akwai shi da yawa,ko kuma  kace KAZZABA din tana nufin Jam’in masu karya sun min yawa,wanda mutane suka fi dauka wato KAZZABA da ma’anar masu karya sun yi min yawa in ji Manzon Allah (saw) –SABODA HAKA DUK WANDA YAYI KARYA AKAINA DA GANGAN TO YA NEMI MATSUGUNIN SHI A CIKIN WUTA ,SANNAN ANYI KARYA AKAN MANZON ALLAH A BAYANSHI ,TO HADISAN MANZON ALLAH SUN ZO MAKU NE DAGA JINSIN MUTANE GUDA HUDU BABU NA BIYAR .NA DAYA SHINE DAGA MUTUM WANDA YAKE MUNAFUKI WANDA YAKE BAYYANA IMANI A ZAHIRI AMMA BA DA GASKE YANA DA IMANIN BANE ,YA BAYYANA KAMAR DA GASKE YANA MUSULUNCI AMMA YA BOYE KUFUR AMMA MUTANE A ZAHIRI BASU GANE SHI BA KUMA ZASU AMSA DAGA WAJEN SHI ,BAI DAMU DA YAYI LAIFI BA ,ZUCIYAR SHI TA RIGA TA KYEKYESHE BABU IMANI SABODA HAKA BAYA JIN NAUYIN YAYI LAIFI ,SANNAN KUMA BAYA JIN KUNYAN LALURAN YA KAME DAGA LAIFI ,BAYA CIKIN KUNCI AKAN YAYI LAIFI ZAI IYA FADAN KARYA YA RANTSE MAKA DA ALLAH YACE MANZON ALLAH YACE MIN KAZA KAZA,BAYA JIN KOMAI YAYI KARYA AKAN MANZON ALLAH DA GANGAN .DA ACE MUTANE ZA SU SANI AKAN CEWA SHI MUNAFUKI NE MAI YAWAN KARYA BA ZASU KARBA DAGA WAJEN SHI BA  KUMA BA ZASU GASKATA SHI BA ,AMMA IDAN MUTANE SUNJI YANA MAGANA SAI SU DINGA CEWA HAKIKA WANNAN YA SAHABBANCI MANZON ALLAH,WATO WANNAN SAHABIN MANZON ALLAH NE –daga nan shubhar  take,shine Imam Ali yake cewa INNAMA SUMMIYA SHUBHATU SHUBHATAN LI ANNAHA TASHBAHUL HAQQA ma’ana an sa ma shubha shubha ne saboda tayi kama da gaskiya saboda sai ka dinga tsammanin ko itace –KUMA YA GA MANZON ALLAH KUMA YA JI DAGA GARE SHI SABODA HAKA SAI SU AMSA DAGA GARE SHI ALHALI SU BASU SAN YANAYIN SHI NA HAKIKA BA ,KUMA HAKIKA ALLAH (SWT) YA BA MANZON SHI LABARIN MUNAFUKAI ,KUMA YA SIFFATA SU DA ABINDA YA SIFFATA SU DASHI,SAI ALLAH AZZA WA JAL YACE “WA IZA RA’AITAHUM TU’UJIBUKA AJSAMUHUM WA IY YAKULU TASMA’A LI KAULIHIM  wato in ka gansu jikkunan su zasu dinga baka mamaki da sha’awa saboda kushu’I da Akhlaqiyat masu kyau domin yaudara da batarwa ,sannan idan suka fadi zaka dinga jin maganar su saboda yanda suke zuwa da siqoqin su da sauran su.Saboda haka mutum basid ba zai iya tantancewa ya gane wannan manufarsa ba ta addini bane sai yace Sahabin Annabi ne,sai ya amsa daga gare shi”.SANNAN IRINSU SUN WANZU BAYAN MANZON ALLAH ,SAI SUKA NEMI KUSANCI ZUWA GA SHUGABANNIN BATA ,SUKA  KUSANCI MASU KIRA ZUWA GA WUTA TA HANYAR SHEDAR ZUR DA KARYA SAI WADANNAN SHUGABANNIN SUKA BASU AYYUKA SABODA SUN KIRKIRO MASU HADISAI SUNCE MANZON ALLAH YACE SABODA HAKA SAI SUKA ZAMA SUNE MANYA MANYAN MINISTOCI DA JEKADU ,SUKA DORA SU AKAN WUYAYEN MUTANE SUKA ZAMA SUNE SHUGABANNI SUKE FADI A JI ,SUKA CINYE DUNIYA TARE DA ABINDA SUKE FADI . SAI NA BIYU KUMA SHINE WANDA YA JI DAGA MANZON ALLAH (SAW) AMMA BAI DORA WANNAN FADIN MANZON ALLAH DIN BA AKAN FUSKAN SHI BA (wato bai fahimci abinda Manzon Allah din ya fadi ba ,zai ce maka Manzon Allah ne yace kaza ai amma bai fahimci abinda Manzon Allah din ya fadi din ba .Ya zo a hadis cewa RUBBA HAMILI FIQHIN LAISA BI FAQIHIN ,RUBBA HAMILI FIQHIN ILA MAN HUWA AFQAHU MINHU zai yiwu mutum yana dauke da fahimta amma shi ba mai fahimtar bane ,zai yiwu a samu mutum yana da fahimta amma sai ya kaita zuwa ga wanda ya fishi fahimta wato in ya naqaltowa wani maganar sai ya zama wanda yake naqalta din ya fi mai naqatowan fahimta ,shi yasa yake cewa LA HADISUN WAHIDUN TADRIHI AFDALU MIN ALFI HADISIN TARWIHI wannan Diraya ba Riwaya ba wato hadisi daya daka fahimce shi ya fi hadisai dubu da kake  riwaito shi )SAI YA SAMU WAHAMI DANGANE DA ITA RIWAYAR KUMA BAIYI KARYA DA GANGAN BA SABODA HAKA ITA RIWAYAR TANA A HANNUNSA SABODA DA KANSHI YA JI MANZON ALLAH YA FADI KUMA YANA GAYA WA MUTANE KUMA YANA AIKATA RIWAYAN DA YAKE TSAMMANIN YA FAHIMTA AMMA BA HAKA BANE KUMA YANA RAWAITOWA KUMA SAI YACE NI DA KAINA NE NA JI DAGA MANZON ALLAH ,INDA ACE MUTANE SUN GANE CEWA WAHAMI NE YA SAMU DA BASU AMSHE SHI BA . SAI NA UKU SHINE WANI MUTUM WANDA YA JI WANI ABU WANDA MANZON ALLAH YAYI UMURNI DASHI SANNAN SAI MANZON ALLAH YA HANA  WANNAN ABIN DA KANSHI (wannan da gaske ya ji umurnin farko ya tafi dashi amma bai ji umurnin daya biyo baya ba wato bai san an canca umurnin farkon ba ,shi kawai ya ji Manzon Allah yayi umurni da wani abu sannan sai daga baya Manzon Allah ya hana wannan abun )ALHALI BAI SAN CEWA MANZON ALLAH YA HANA WANNAN ABIN DA YA JI YA UMURTA DA FARKO ,KO KUMA YA TABA JIN MANZON ALLAH YA HANA WANI ABIN NE SAI DAGA BAYA KUMA YAYI UMURNI DA WANNAN ABINDA YA HANA ALHALI SHI KUMA BAI SANI BA.SAI YA ZAMA YA KIYAYE MANSUKH AMMA BAI KIYAYE NASIKH DIN BA (sai ya din ga nakaltowa mutane mansukh ba nasikh ba alhali bai sani ba )INDA ACE SHI DA KANSHI YA SAN CEWA WANNAN HUKUNCIN MANSUKH NE DA YA BARSHI AMMA BAI SANI BA YANA BUKATAN AHLUL ZIKR SU BAMBAMCE MASHI SUCE MASA WANNAN KAZA NE WANCAN KAZA NE . NA HUDUN KUMA NA KARSHEN SU SHINE WANDA BAIYI KARYA BA (wato Imam Ali ) AKAN MANZON ALLAH (SAW) BA YANA MA GABA DA KIYAYYA DA KARYA NE SABODA TSORON ALLAH DA GIRMAMA MANZON ALLAH KUMA BAI MANTA ,WANNAN ABINDA YAKE NAKALTOWA MUTANE KIYAYEWA CE WANDA YA KIYAYE DAIDAI DA DIQQA KAMAR YANDA YA JI A YANDA YAKE SABODA SAI YA ZO DASHI KAMAR YANDA YA JI ,BAI KARA BA KUMA BAI RAGE BA AKAN SHI,KUMA YA SAN NASIKH DA MANSUKH SABODA HAKA SAI YAYI AMFANI DA NASIKH YA WURGAR DA MANSUKH DOMIN UMURNIN ANNABI KAMAR ALKUR’ANI NE ,WATO HADISI AKWAI NASIKH DA MANSUKH ,MUHKAM DA MUTASHABIH .MANZON ALLAH YA KAN FADI MAGANAR DA TAKE DA FUSKA GUDA BIYU KUMA DOLE SAI KA SANSU GABAKI DAYAN SU ,YANA DA MAGANA AMM (gamagari) YANA KUMA MAGANA KASS(kebantatta )KAMAR ALKUR’ANI ALHALI GASHI ALLAH TA’ALA A ALKUR’ANIN SHI CEWA YAYI “MA ATAKUMUR RASULU FAKHUZU HU WA MA NAHAKUM ANHU FANTAHU  wato abinda Manzon ya zo maku dashi ku amsa abinda kuma ya hane ku dashi ku hanu”SABODA HAKA SAI NASIKH DA MANSUKH SU ZAMA SUN CAKUDE MA WANDA BAI SANSU BA WANDA BAI IYA TANTANCE WA ,WANDA BAI SAN ABINDA ALLAH DA MANZON SA SUKE NUFI BA……….har zuwa karshen abinda yake fadi dangane da wannan ,sai ya zo karshe yake cewa :KUMA HAKIKA NA KASANCE  A KOWANE WUNI INA SHIGA MA MANZON ALLAH (SAW) SAU DAYA A KOWACCE RANA SANNAN SAU DAYA A KOWACCE DARE (wato shiga biyu da safe da kuma dare kenan )TO SAI YA KEBE NI A CIKIN WANNAN DAKLA DIN NI KADAI IDAN NA JE MASHI ,SAI IN DINGA KEWAYAWA TARE SHI DUK INDA YA KEWAYA (ka ga kenan ba zai iya bayanin abinda ya fi haka ba ba mu san me yake nufi ba,kawai yace mana me?sai in kewaya tare dashi duk inda ya kewaya shi kenan ya wadace ka,wato ilmuka wadanda suke na rubutu da wadanda ban a rubutu ba ,na magana da wadanda ban a magana ba shine inda yake cewa ALLAMANI RASULULLAH ALFA BABIN MINAL ILMI YANFATIHU ko YAFTAHU MIN KULLI BABIN ALFU BABIN ,irin wannan yake nufi ,ba ilimin karatu bane saboda ilimin karatu haka ba zai yiwu ba kuma lokacin day a fadi wannan maganan a lokacin wafatin Manzon Allah ne wato a lokacin rashin lafiyan shit a barin duniya Sahabbai suna zaune a dakin day a shigo ya je kusa da Manzon Allah ya sanya kunnensa kusa dashi a lahza kadan sai ya taso ,yana taso sai fadi wannan ALLAMANI RASULULLAH ,to wannan lahzan bat a isa a koya maka babi miliyan na ilimi ba musamman idan miliyan din ramzi ne ba adadi ba  )KUMA HAKIKA SAHABBAN MANZON ALLAH SUN SANI CEWA MANZON ALLAH BAI TABA AIKATA WANNAN DA KOWA BA A CIKIN MUTANE IN BANDA NI ,WANI LOKACI A GIDA NA NE MANZON ALLAH (SAW) YAKE ZUWA SANNAN MAFI YAWANCIN LOKUTA A GIDA NA NE YAKE SAMU NA SAI YA ZAMA MUN YI WADANNAN SESSION DIN TARE DASHI ,RAN DA YAKE NI NAKE ZUWA WURIN SHI TO IDAN NA JE MASHI A DAYA DAGA CIKIN GIDAJEN SHI SAI YA KEBE NI YACE MATAN SHI SU TASHI MU ZAUNA MU BIYU KAWAI BA WANDA YAKE WANZUWA IN BANI BA TARE DASHI AMMA IDAN GIDA YA ZO MAWA DOMIN YA KEBANCE TARE DA NI A GIDAN A AZZAHRA DA SAURAN YAYANA BABU WANDA TASHI SABANIN A GIDANSHI NA JE ,KUMA NA KASANCE IDAN NA TAMBAYE SHI YA KAN BANI AMSA ,KUMA IN NAYI SHIRU NA KARAR DA DUKKAN TAMBAYOYI NA SAI YA FARE NI WATO KARA MIN DA ABINDA BAN TAMBAYE SHI BA BAN TUNANO BA .SABODA HAKA BABU WANI ABU WANDA YA SAUKA AKAN MANZON ALLAH NA DAGA AYOYIN ALKUR’ANI FACE YA KARANTAR DANI DA ITA KUMA YAYI MIN IMLA’IN TA SAI IN RUBUTA AYAN DA RUBUTU NA SANNAN SAI YA KARANTAR DA NI TAFSIRIN TA DA TA’AWILIN TA ,YA KARANTA MIN NASIKH DIN TA DA MANSUKH DIN TA ,DA MUHKAM DIN TA DA MUTASHABIH DINTA ,DA KASS DIN TA DA AMM DIN TA ,SANNAN SAI YAYI WA ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA ADDU’A AKAN YA BANI FAHIMTAR TA DA KUMA IN KIYAYE TA SABODA HAKA BAN TABA MANTA WA DA AYA DAGA ALKUR’ANI BA ,HAKA BAN TABA MANTA WANI ILIMA BA WANDA YAYI MIN IMLA’IN SHI KUMA BAN TABA MANTA WATA AYA WADDA NA RUBUTA TA BA TUN DA MANZON ALLAH YAYI MIN ADDU’A DA ABIN DA YAYI MIN ADDU’A DASHI BA ,KUMA MANZON ALLAH BAI BAR KWARZANE DAGA ABINDA ALLAH YA SANAR DASHI NA HALAL KO HARAM KO UMURNI KO HANI WANDA YA KASANCE NE KO ZAI KASANCE NE A NAN GABA ,HAKA KUMA BABU WANI LITTAFI WANDA YAKE SASSAUKE WANDA ALLAH YA SANAR DASHI KO SAUKAR DASHI AKAN WANI GABANIN SHI (wato Manzon Allah) NA DAGA BIYAYYA KO SABO FACE SAI DA KARANTAR DANI WANNAN  KUMA NA KIYAYE SHI SABODA HAKA BAN TABA MANTA WA DA KO HARAFI DAYA BA …….har ya zo inda yake cewa Sahabbai sun kasance basa iya tambayar Manzon Allah (saw),sukan jira bakauye ya zo daga kauye yayi mashi tambaya sannan sai  su ji amsar abinda tuntuni suke so su sani . Banda wannan Imam Ali yayi da’awan sanin komai da komai .Abin yana da ban mamaki ,ku saurara ku ji I’itikadojin mu .Imam Ali (as) Yana cewa a wata huduba tashi ‘’ WALLAHI LAU SHI’ITU AN UKHBIRA KULLA RAJILUN MINKUM BI MAKHRAJIHI WA MADKHULIHI WA JAMI’I SHA’ANIHI LA FA’ALTU ma’ana WALLAHI INDA INA SO IN FADAWA KOWA DAYA DAGA CIKIN KU WATO KOWANE MUTUM MUTUM DAGA CIKIN KU MAFITAR SA DA MASHIGAR SA DA KUMA DUKKAN SHA’ANONIN SA GABAKI DAYA DA NA GAYA MAKU DOMIN NA SANI ,WALA KIN AKHAFU AN TAKFIRU BIYYA FI RASULILLAH ma’ana INA JIN TSORO KADA KU KAFIRCE DAGA MANZON ALLAH DANNI,Ku ce ya fi Manzon Allah sani wato ku kafirce ku kasa gane Manzon ne ya fada min .AMMA KU SAURARA ZAN ZUBA MA KEBANTATTU WADANNAN ILMUKAN WADANDA SUKE AN LAMUNTA SU BAZA SU BACE BA (wato abinda Manzon Allah ya zuba min zan yi transfer dinshi zuwa ga kebantattu amma ku in na fada maku zaku kafirce ga Manzon Allah saboda ni ),wannan zaka same shi a Nahjul Balagha a huduba ta 175 domin mutum ya kara bahasi akai.Wannan daya kenan . Sannan banda wannan, Imam Ali yana cewa FAS’ALU NIY QABLA AN TAFQIDUNIY  ma’ana SABODA HAKA KU TAMBAYE NI KAFIN KU RASA NI (FAS’ALU gini ne akan wata jumla wanda ban karanta ba .Wannan FA’UN din ta TARATTUBI ce wato ta JAZA’I )FAWALLAZIY NAFSIY BI YADIY ma’ana DOMIN INA RANTSUWA DA WANNAN WANDA RAINA KE HANNUNSA BA ZAKU TABA TAMBAYA NA DANGANE DA WANI ABU DA YAKE A TSAKANIN KU DA SA’A BA WATO DAGA WANNAN LOKACIN HAR ZUWA TASHIN KIYAMA FACE NA BAKU LABARIN SHI …….har zuwa karshe .Wannan za a same shi Nahjul Balagha a huduba 63 . Sannan a wani wurin yana fadin cewa YAKU MUTANE KU TAMBAYE NI KAFIN KU RASA NI FA (ka san ba wani wanda zai iya fadin wannan in ba Ali ba ,wato gani a cikin ku ku tambaye ni kada ku bari bana nan ko kuma ku rasa ni )DOMIN NI NAFI SANIN HANYOYIN SAMA AKAN HANYOYIN KASA (wato yafi sanin DURUQ din sama akan DURUQ din kasa ),za a samu wannan a huduba ta 189 a Nahjul Balagha .Sannan da ire irensu masu yawa . A nan yana cewa Manzon Allah yace ma Imam Ali “HAKIKA ALLAH YA IDDILA’ANTAR DANI AKAN ABINDA YA GA DAMA NA DAGA GAIBUN SHI TA HANYAR WAHAYI DA TA HANYAR TANZIL ,NI KUMA NA IDDILA’ANTAR DAKAI DA WANNAN TA HANYAR ILHAM”,wannan shine wannan DAKLA  da muke magana,Shi Allah mubasharatan ya saukar min kai kuma da wasida ta wato ba Allah ya sanar da kai ba amma duk abinda nake dashi nayi maka transfer .Shi yasa Imam Sadiq yake cewa “ WALLAHI HAKIKA AN BAMU ILIMIN NA FARKO DA NA KARSHE “,banda haka akwai su da yawa.Akwai wani abu da Imam Ali ya taba fadi  yana cewa ‘’BAYA NA WANI MUTUM ZAI BAYYANA AKAN KU …..ya basu labarin siffofin mutumin sannan ya cigaba da cewa:SHI WANNAN MUTUMIN IN YA BAYYANA ZAI UMURCE KU KU ZAGE NI SANNAN UMURCE KU KU BAR’ANTA DAGA GARE NI -Malamai da yawa sun yi kokari su fadi ra’ayoyin su akan waye wannan mutumin,wasu sun ce Hajjaj wasu sun ce wane ,wasu kuma sun ce wane amma Ibn Abul Hadid Al-Mu’utazili yace yana ganin Mu’awiya ne saboda siffofin sun dabbaqu akan shi wadanda Imam Ali ya fadi a lokacin da yake bada labaran gaibu -AMMA  ZAGI KU ZAGE NI IDAN YACE KU ZAGE NI KU ZAGE NI DOMIN SHI ZAGIN GARE NI TSARKAKA NE GARE KU KUMA KUBUTA ,AMMA BARA’A TO KADA KU BAR’ANTA DAGA GARE NI (wannan yana da dangantaka day a wato kenan WILAYA )DOMIN NI AN HAIFE  NI AKAN FITRA AKAN TAUHIDI BAN TABA SHIRKA BA ,SANNAN NA RIGAYA ZUWA GA IMANI DA HIJRA .To Allamah Suyudi zamu iya amfani da abin day a fadi daga cikin Mu’ayyidat ,ya kawo wani abu wanda yayi kama da wannan ZAHIRAN wato yayi kama dashi sosai.Yana cewa “ABDURRAZAQ YA FITAR DASHI YACE IMAM ALI YACE MIN YA KAKE GANIN KANKA RANDA AKA UMURCE KA KA LA’ANCE NI ,SAI INA MAMAKI NACE HAKA ZAI FARU ?SAI YACE ZAI FARU ,SAI YACE IDAN LOKACIN YA ZO ME ZAN AIKATA ,KA TSINE MIN DIN AMMA KADA KA BAR’ANTA DAGA BARI NA . TO WATA RANA SAI MUHAMMAD BIN YUSUF DAN UWAN HAJJAJ BIN YUSUFU ATHTHAQAFI YA UMURCE NI A LOKACIN SHINE AMIR A YAMEN CEWA IN LA’ANI ALI ,TO YA UMURCE SAI NACE : INNAL AMIRA AMARANIY AN AL’ANA ALIYAN FA LA’ANUHU LA’ANAHULLAH  ma’ana HAKIKA SARKI YA UMURCE NI DA IN LA’ANCI ALI TO KU TSINE MASHI ALLAH YA TSINE MASHI .TO LOKACIN DUK BASU GANE BA SAI WANI MUTUM DAYA .Wannan yana cikin Tarikhul Khulafa na Suyudi ,littafin sunna .Wannan yana daga cikin abubuwan da banda lokacin magana akan su saboda basu da iyaka dangane da Imam Ali (as) da kuma matsayinshi a cikin al’umma da kuma ababen da suka sanya AHAQQIYYAH dinshi da kuma HAQQANIYYAH din Ali (as) wannan kenan idan mutum ya bincika zai ga sun fito kiri kiri a bayyane wato babu shubha duk da ma’abuta shubha sun yi kokari su sanya shubha .Imam Ali shike da Nasikh da Mansukh ,yake da Muhkam ,Mutashabah ,Amm  da Kass da komai da komai .Addinin shi addinin hankali da adalci ,addinin tsinkaya da sanin duniya da lahira .Addini wanda yake na Yan Adamtaka wanda yake dan Adam idan ya ga irin wannan addinin zai yi sha’awa ya ga cewa ya karbe shi .288

Top of Form

 

Bottom