Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA
Alhamis

16 Afirilu 2015

14:44:21
684227

Saudiya ce ta kawo rashin zaman lafiya/ Makka da Madina ba mallakin iyalin Sa’ud bane/ taya Ansarullah suka samu iko a Yemen? Da

Daya daga cikin mayan jami’an cibiyar Ahul-Baiti{a.s} ta Duniya ya bayyana cewa; idan kasar Saudiya ta kasa wurin kawo tsaro ga mahajjata na kasashe, ya kamata kasashen musulmi su kafa kwamiti wanda zai kula da Haramain.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-Ayatullahi Mahdi Hadawi Tehran yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Qum na Iran, ya bayyana abubuwan da suka faru na cin zarafin Alhazain Iran da kuma dagatar da zuwa aikin Umra wanda Iran tayi da kuma harin Saudiya akan Yemen.

Acikin hirar tasa Hadawi Tehrani ya bayyan abubuwan da suka kawo canji a Iran idan yake cewa kafin juyin musulunci kasashe Turai sun dauki Iran a matsayin kasa mai muhimmanci a siyasar su amma ba zato ba zammani aka wayi gari musulunci shine ke jagoranci kasar Iran yace, bayan fitar Iran daga hannun kasashen Turai, sai wasu kasashen suke neman amfanin da wannan damar domin su zamo masu kare bukatun Turawa a gabas ta tsakiya.

Ayatullahi Hadawi yaci gaba da cewa;jamhuriyar musulunci ta Iran da kunshi al’umomi da Mazhabobi daban daban saboda taken juyin musulunci shine raya addini da taimakon marassa karfi, duk da cewar al’ummar Iran da shuwagabannin su ‘yan shi’a ne amma hakan baisa sun canja taken juyin musulunciba duk da karerayin da makiya keyi na nuna Iran amatsayin wata Mazahaba ta daban da sauran musulmi.

Yace; abunda jamhuriyar musulunci ta nuna a aikace shine taimako masu rauni da kuma warware matsalolin duniyar musulmi shi’a ne ko sunna. Saboda haka Iran na kiyaye hakkokin kowa da kowa kuma juyin musulunci ya samu karbuwa a duniya idan muka lura da farkawar musulunci dake faruwa akasashe da daman a musulmi.

 Daya daga cikin misale da zamu iya nunawa na tasirin juyin musulunci na Iran ga kasashe shine abunda ya faru a Tunusiya saboda kasar na da muhimmanci wurin Faransa kuma shugaban kasar dan mulkin kama karya ne sanna mata basu damu dasa Hijabi ba kuma ana takurawa masu kishin addini amma duk da haka al’ummar kasar suka yunkura domin kawo canji kuma suka samu nasara

Malamin yace; duk da kokarin makiya na dakushe farkawar musulunci kamar kudadan Larabawa da ‘yan liken asiri na Turai da na Isra’ila wanda hakan ya canza juyin daga tushensa ba asali,inda kasar ta koma kasar da tafi kowace kasa yawan ‘yan ta’adda na Syria da kuma kirkiro jihadi aure wanda matan kasar keyi a Syria

Ayatullahi Hadawi ya kara da cewa; kokarin ‘yan mulkin mallaka na toshe farkawar musulunci shine samar da kungiyoyi na ta’adda akasar Syria kamar su Da’ish wanda masana ke ganin cewa ba’ataba samun dabbobin mutane ba wanda basu da hankali kamar Da’ish ba kuma basu da wata alaka da musulunci tahaka suka mamaye wani yanki na Iraki da Syria, saboda haka a siyasar kasar Iran na taimakawa masu rauni yasa ta shiga cikin al’amarin wadannan kasashe biyu wanda yanzu bayan shekaru amma hukumar Syria na cigaba da mulki kuma a  Iraki ‘yan kilomitocine suka rage ma Da’ish su kama Bagdada amma da kokarin Iran da hadin kan al’ummar Iraki hakar su bata cimma ruwa ba.

Ayatullahi Hadawi a cigaba dayananin say a tabo abunda ke faruwa a kasar Yemen inda yace, Ansarullah kungiyace ta al’ummar kasar Yemen wadda ke da karbuwa ga kowa ne bangare na kasar, duk da cewa da farko kungiyace ta kabilar ‘yan shi’a Zaidi kuma sun samu takon saka sau tari da tsohon shugaban kasar wato Abdullah Sale, amma daga karshe kungiyar Ansarullah ta Husi ta zama babar kungiyar siyasa ta kuma samu karbuwa a kasar.

Hadawi yayi nuni da harin kasar Saudiya akan al’ummar Yemen inda yace, lokacin da Saudiya daga Ansarullah sun samu karfi maimakon suyi amfani da siyasa ta kasa da kasa sai kawai suka afkama kasar da hare-hare.

Ayatullahin ya bayyana cewa abunda ya faru a filin jirgin Jidda abun bakin ciki ne inda aka wulakanta al’hazan kasar Iran guda biyu ta mumunar hanya{ an yimasu fyade wato luwadi wanda wasu yan sanda filin jirgin Jidda suka yi a watan da ya shige} yace garuruwan Makka da Madina garuruwa ne na al’ummar musulumi duk da cewa suna cikin kasar Saudiya amma abun bakin ciki shine sarakuna kasar suna nuna bam-bamci ga wasu mazahabobin na musulmi ba wai Shi’a ba kadai saboda haka abunda da ya faru a Jidda ya nuna kasawar sarakuna kasar wurin kiyeye mahajatta kuma sarakunan basu can-canta da tafiya da wurare masu tsarkiba na al’ummar musulmi saboda haka malamin ya bukaci akafa wata majalissa ta musulmi wadda zata dauki nauyin tafiyan da Haramain din.wannan kuma shine mahangar Imam Khumaini{r.a}.

Malamin yace, dagatar da zuwa umra da kasar Iran tayi abune wanda ya dace domin kiyayi hakkokin al’ummar ta.. Bayan kare jawabin malamin ya amsa wasu tambayoyi kamar haka, shin akwai maluman da suke goyan bayan Da’ish ya halin yanzu?

Ayatullahi Hadawi ya amsa da cewa, duk da yake Da’ish na da akidar wahabiyanci ne amman hakan bayana nufin cewa wahabiyawa na koyan bayan su bane. Kuma wadanda suka kafa Da’ish ba malamai bane, wasu na ganin kungiyoyin liken asiri ne suka kafa Da’ish.

Wani kuma ya tambaya minene alaka zakanin Da’ish da ‘yan uwa musulmi na Masar?.

Ayatullahin ya amsa kamar haka, kungiyar ‘yan uwa akidar su salafiya ce kuma salafanci yana da rassa da dama wahabiyanci daya ne daga cikin rassan salafiya amma asiyasance ‘yan uwan musulmi basu da wata alaka ko tunani mai kama dana Da’ish ba sai dai ga akida tushen su daya

Wani ya tambaya minene alaka zakani Ansarullah da ‘yan Shi’a Zaidiya?

Hadawi ya amsa kamar haka, mafiya yawan mutanen Yemen Zaidiya ne sunna yan kadan ne Husi kabilaci ta ‘yan Shi’a Zaidiya  wadanda ke fada da zalunci  saboda haka amma daga baya sun fadada siyasar su inda suka samu karfawa ga al’ummar kasar. Saboda haka abunda ke faruwa yanzu akasar a mahangar Iran shine mutane Yemen ne suke da alhakin warware matsalolin sub a tare sa kasar Saudiya tasa baki ba.ABNA