Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : mu'assasatul thaqlain
Lahadi

12 Afirilu 2015

16:50:49
683117

AUNA ZABEN 2015 DA WASU MUHIMMAN AL’AMURA DANGANE DA SIYASAR NIGERIA kasha na{1} Daga Shaikh Hamzah Muhammad Lawal

Wanda ya rubuta Abu Ahmad Addaurawiy A’UZU BILLAHI MINASH SHAYDANIR RAJIM BISMIL-LAHIR RAHMANIR RAHIM WASAL-LAHU ALA MUHAMMADIN WA ALIYID DAYYIBINAD DAHIRIN

 

Mutane da yawa suna so su san ra’ayoyin mu dangane da zabukan da suka faru 28 ga watan Maris 2015 wato zabukan Shugaban kasa da kuma yan majalisun tarayya,sannan kila suna so su san ra’ayoyin mu akan wasu mas’aloli da maudu’ai da suka shafi duniya,Kaman rikicin da ake yi a Yamen a yanzu da kuma yarjejjiniyar da ake yi ta Nukliya wanda ake gab da cimma wa tsakanin Jamhoriyar Musulunci ta Iran da kuma membobi na dindin a hadi na daya wato P5+1,wato Permanent five da kuma European union.Wadannan guda biyun na baya kila nan gaba mu samu wani lokaci domin yin bincike akansu,amma na farkon wato zaben 28 ga watan Maris 2015 zamu yi bayaninsu saboda domin su muka zauna a yau da ikon Allah. Ina so in fara da wasu ASULLA wadanda na ginu akan su dangane da siyasa ta Nigeria,musamman a shekaru goma sha shida da suka wuce a yanzu wato daga 1999 zuwa yanzu 2015.Asullan ga su kamar haka:- ASALI na farko shine matsalar Nigeria itace Jam’iyyar PDP,wannan na fade shi kamar shekara hudu da suka wuce,ina maid a mutane zuwa ga bayanan guda biyu da na yi wato jawabi akan Janye tallafin albarkatun maid a kuma jawabi game da Zaben 2011.Na fadi haka kafin General Azazi ya fadi cewa matsalar Nigeria itace Jam’iyyar PDP duk da yake ni ba dan siyasa bane kuma ba ita nake yi ba amma awo ne wanda na yi akan asasin wasu HAQA’IQ,daga ciki har da wata masifa wanda jam’iyyar PDP ta jawo wanda ake ce ma ta Zoning ko kace kewayawa ko kewaya shugabanci ko makamai tsakanin larduna guda shida wadanda suka hadu suka yi taswiyar siyasa ta Nigeria(Political Map)wanda wannan Mafari ko Principle ko Mabda’a na Zoning ya haifar da babban matsala a Nigeria a 2011 ko kuma 2010,ko kuma biz zat a 5 ga Mayu 2010 a ranar da Umaru Musa Yar’adua ya rasu ya haifar da mishkila mai yawa wanda kila zan dan yi magana akanta .Ala kulli hal matsalan Nigeria itace Jam’iyyar PDP,wannan asali na farko kenan. ASALI na biyu wanda na ginu akanshi shine cewa a hankali a hankali wata rana za a kai lokacin da ba zai yiwu ba sojoji su bude wuta akan mutanen Nigeria,tabbas za a kai wannan lokacin in ma ba riga an kai ba a yanzu.A 2011 zuwa yanzu ikon gobnati na ta sanya sojoji su kashe Mutane babu dalili ya ragu sosai kuma ina ganin kamar zai cigaba da raguwa har ya zo ya zama sifur wato zero musamman saboda hukunce hukunce da kotuna dabam dabam na kasa suka yi kafin wannan zaben da kuma a lokacin zaben cewa soja bai da rawar da zai taka a cikin zabe,wannan ya riga ya zartu ,kuma kotuna sun tabbatar dashi ya riga ya zama daya daga cikin ababen da suke a kundin shari’a ta kasa. Sannan akwai wani Asali wanda yake cewa idan Mutanen Nigeria za su tashi gaba ki daya akan matsala dukkansu a lokaci daya to jami’an tsaro basu da karfin da zasu iya hana su akan wannan abun da suka tashi akanshi.Shima wannan mun girbe shi ne a wannan lokacin na janye tallafi. Akwai wani Asali daga cikin Asulla wanda yana gaayen muhimmancin gaske wanda shine mutane su kan koma ga Fitra din su domin matsi da masifa da wahala,ita kuma wannan Fitra din ta fi yalwa a da’ira daga addini,kenan lokacin da mutane suka tashi domin komawa zuwa fitrar su za ka ga suna komawa zuwa fitransu a matsayinsu na Mutane ne ba a matsayinsu na masu bin wani addini ba ko wani ra’ayi ba ko ittijahi ko sauransu ba.Kana iya kawo ishkal cewa to menene matsayin addini musamman addinin musulunci?,to kana nufin fitra ta soke addini kenan?Da’awar mu a matsayin mu na Musulmi shine addinin musulunci ya zo ne ya zama tarjama a aikace ta fitran dan adam,sannan ban da ta zama tarjama a aikace addini ya zo ne ya yi taujihin dan adam zuwa ga komawa ga wannan fitra din saboda dukkan musulmi mun hadu akan ita fitran amma a wajen shakkasa ta ne akwai matsala .Wani lokaci a wajen shakkasa ita fitran za a iya dacewa wani lokaci kuma muna iya kaucewa,addini ya zo ne kullum ya tabbatar da bamu kauce ma fitra din,saboda haka babu karo tsakanin Fitra da addini abin da yake akwai shine fitra na iya fin addini yalwa a da’ira a wasu lokuta musamman idan addinin bai zama addinin musulunci ba ko kuma ba dabbaqa addinin musulunci yanda ya kamata ba. Wadannan sune Asulla wadanda muka girba saboda tajribobi da gogayya a lokacin da muke kallon yanayin siyasar Nigeria a shekara goma sha shida. Dab’an!Matsalan siyasan Nigeria ba ta faro daga shekara sha shida ba amma wannan tarihin nake so mu bincika a wannan zaman . Bayan wadannan Asullan sai ince Bahsin da nake so in yi a yau zai ginu ne akan asasin abin da ake ce ma a ilmance EMPIRICAL EVIDENCE maimakon THEORY ko LOGIC ko CONJECTURE ko ILLUSION ko IMMAGINATION ko EMOTION,zan yi bayanin abinda nake nufi insha Allah amma lokacin da nace Imperical abin da nake nufi shine FACTUAL,PRACTICAL,PRAGMATIC,VERIFIABLE ,DEMONSTRABLE,wato kenan Bahasin da zan yi zai ginu akan HAQA’IQ a taqaice kawai ba akan asasin Nazariyyah ba ko zaci-fadi ko tsammani ko Adifa ko abinda yayi kama da wannan abadan,zai ginu ne akan abin da ake kira da EMPIRICAL EVIDENCE.Shi yasa,na biyu kenan, domin binciken zai ginu ne akan asasin haqiqa da hujja har ya zama gaba daya zai yi bayani akan mu’amala da Waqi’a kamar yanda yake wato kenan WHAT OBTAINS AS IT IS ko kuma mu ce AL-WAQI’U KAMA HUWA,wani lokaci akwai kana so ne ka sana’anta Waqi’in da babu shi,shi wannan hanyar shi da ban ne.Kana so ka sana’anta waq’i babu shi wannan hanya daya kenan,wani lokaci kuma akwai waqi’i kana so ka canja shi ne wato kayi tasarrufi a cikin waqi’i,wani lokaci zaka yi abinda mu ke so mu yi a yanzu shine mu karanta waqi’in da yake daman akwai shi a inda yake,da yake dama akwai shi da manufar fahimtar shi da kuma warware shi wato analysis akan waqi’in kamar yanda yake,wannan kuma bai nuni da mun yarda da waqi’in ko bamu yarda dashi ba.Wannan a wajen Bahsin yake kila idan mu ka zo girbi a lokacin ne zamu yi bayanin akan wannan,mun yarda ko ba mu yarda amma yanzu Muhimma dinmu ko in ce wazifar da muka dara kanmu shine mu karanta waqi’in wato Kira’atul waqi’i domin kokarin fahimtan shi waqi’in ba wai a zahirin shi haka yake ba muna so mu san haqiqanin shi ne.A lokacin da muka ce Empirical evidence muna nufin hujjoji da haqiqoqi wadanda suka zo a hannayen mu dangane dashi zaben.Kaman akwai mabubbugai masu yawan gaske na bayanai da labarai wadanda suka hannayen mu da suke da alaka da shi zaben.Wasun su kuna da su a hannayen ku kamar jaridu,jaridu kamar mabubbuga ne na farko na samun bayanai wanda aka dawwana shi dangane da abinda ke faruwa,kamar wasiqa c e ko kuma kace masdar ce ta tarihi.Misali na karanta na Nigeria da na waje kamar Dailytrust da Leadership,kamar online newspapers irin su Premium times,Sahara Reporters da sauransu.Sannan akwai mububbugan jaridu kafafen watsa labarai na kasashen waje kamar Reuters,kamar Associated Press na yi mu’amala dasu sosai ,kamar BBC World da Aljazeera International sun muhimmantar da zaben Nigeria sosan gaske a waqi’in shi kamar yanda yake.Sannan kamar Press Tv wanda abin taqaici shine ba ta muhimmantar da al’amarin zaben Nigeria ba saboda haka na je alternative source wato musanya kamar irin su BBC din da Aljazeera International da sauransu da sauransu.Press Tv a lokacin sun muhimmantar da batun yakin Yamen da Yarjejjiniyar Nukliyya da ake yi da kasar Iran shi yasa basu muhimmantar da zaben Nigeria ba wannan yasa bata zama mububbuga wadatatta ba a wurin bada labarin zaben da aka yi a Nigeria ba,sannan akwai shirin da Press Tv take yi na Africa Today su ma basu rufe zaben ba kuma bas u tahlil akan zaben ba a iyaka abinda na sani har zuwa yanzu.Sun yi bincike akan zaben kafin a yi shi,suka sami Panel na mutane guda uku suka tattauna dasu amma bayan nan basu yi ba amma watakila nan gaba za suyi. Akwai yan siyasa masu yawan gaskengaske da nake da alaka dasu wanda ita ma wata mububbuga ce muhimmiya ta samun bayanai dangane da zaben da kuma sakamakon zaben da yanda faru,wasu daga cikin yan siyasar muna da dangantaka da su ta jini,wasu kuma dangantaka ce ta ra’ayi sannan wasu daga cikinsu zababbu ne wasu kuma ba zababbu bane.Sannan banda haka akwai yan uwa wadanda muke tare dasu wadanda suka yi aikin zaben a kashin kansu wanda su ma sun zama mububbuga mai muhimmanci na samun bayani akan zaben da kuma yanayin zaben,kamar misali yin amfani da Card Reader da sauransu da sauransu.Mun samu bayani masu yawa ta hanyar irin wadannan yan uwa wanda yake nan gaba kila ya kamata in za su irin wannan aikin su sanar damu saboda suna da muhimmanci ko kuma nan gaba ya zama mu sanya wasu da za su dinga irin wannan aikin.Sannan banda haka akwai Yan uwan da suka dinga feeding dinmu da bayanai akan kasan a lokacin da abubuwan ke faruwa ta hanyar aiko mana da emails na text wato nassosi da kuma hotuna,har da na video wato hotuna masu motsi da sauransu,kamar yanayin da Kaduna take ciki da sauran garuruwa bayan da aka shelanta wanda yayi nasara da yanda mutane kowa na cikin gidanshi yana tsammanin masifa,tituna ba kowa akansu,duk wadannan mun sassame su akwai su.Akwai mutane masu yawa wadanda suka dinga bamu labaran yanda aka gudanar da zabubbukan da kuma sakamako a radiyo da telebijin da sauransu da sauransu,sannan banda haka akwai wadanda suka dinga aiko mana da jawabai na wasiku wato jaridu kamar jaridar Thisday wadda ta taya General Buhari murna tun kafin INEC ta shelanta cewa shine ya ci zaben.Akwai misalan su da yawa kamar misali daga cikin mububbugai akwai ita kanta Jam’iyyar APC,ina da sila wato hanya zuwa ga situation room din ita APC wanda wannan ba karamin abu bane,sannan na dinga samun sakamako daga situation room dinsu kuma da taqaitaccen bayani da suka yi game da yanda suka qayyama zaben gabaki daya wato suka ce: “The Summary of The Election Incidences and Results Reported at The APC Situation Room during the Presidential Election,Saturday March 28,2015”,ya kamata ya zama Tuesday April 1,2015 sabanin Saturday.Wannan Report din muna dashi sannan kuma sunyi bayanin wani Software da suka yi amfani dashi wajen samun sakamakon zaben,wato wani software wanda suke kiran shi E-MARS.Suna cewa :- Software da APC suka yi amfani dashi dan kada a cuce su tayi amfani sosan gasken gaske a wajen tunkuda bayanai zuwa ga wakilansu daban daban domin tabbatar da cewa sakamakon da suke tattarawa din duk da yake a rasmance ban so in ce a hukumance ko a gomnantance saboda yan radiyo suka kirkiro wannan wato suna fassara OFFICIALLY a da hukumance ko gobnantance saboda ba kowane abu da yake RASMANCE ko OFFICIAL yake GOVERNMENTAL ba.Akwai wannan matsalan ta tarjama a hausa,cewa domin tabbatar da sakamakon da ake samu duk da yake ba a shelanta shi a waje ba amma bai bambamta da ita hukumar INEC ta sanar. Shi wannan E-MARS software din in ji Sitaution Room din APC wanda Terable System suka yi shi,wani irin software wanda a cikin kasa aka yi shi kuma yana da Zarfiyya wato yana da ikon iya sa ido akan zabukan da suka faru a Nigeria,kuma shi wannan Software din zai iya bada bayani a lokacin da bayanin ke faruwa (wato real time)kuma a fassale(warware)akan zaben Nigeria.Shi wannan Software din wani irin magani ne da aka samo wanda yake karban bayanai ta hanyar gajerun sakonni(wato SMS) wadanda masu sa ido suke aiko wa daga dukkan rumfunar zabe zuwa Situation Room din.Sai suka cigaba da cewa ‘’BELOW ARE THE RESULTS CAPTURED BY THE SITUATION ROOM USING THE E-MARS SOFTWARE,RESULT ANOUNCED BY INEC AND ALSO SUMMARY OF SOME OF THE INCIDENCES REPORTED TO THE APC SITUATION ROOM.”To anan gurin sun kawo nasu sakamakon sannan suka kawo sakamakon INEC,wanda ina dashi sannan suka kawo duka waqi’o’in da suka afku a ranar zaben harda hotuna.Wannan mububbuga ce mai kyan gaske wadda zata iya baka IDEA na me ya faru,wannan sun shiga cikin abinda muke kira da EMPIRICAL EVIDENCE ko?ban da Emotion da Adifa,wanda mutane ba su sani ba a lokacin da muke rayuwar mu na yau da kullum muna dariya da mutane kuma muna irin wadannan ayyukan a background a lokaci guda tsabanin abinda su mutane suke tsammani. Sannan banda haka akwai Jaridar Thisday lokacin da ta tayi hasashen cewa shi Genaral Buhari zai ci zaben har taya shi murna,muna da wannan bayanin,gashi kamar haka: THE BOARD OF EDITORS OF THISDAY NEWSPAPER PROJECTS BUHARI WINNER,THE INDEPENDENT NATIONAL ELECTORAL COMMISSION ANNOUNCING COLLECTED RESULTS FOR THE PRESIDENTIAL ELECTION OF THE 36 STATES INCLUDING THE CAPITAL OF TERRITORY……cewa bayan da INEC ta fadi sakamako na jihohi 36 da kuma birnin tarayya Abuja sannan bayan sunyi tahlilin duka sakamakon da suka samu daga Kananan Hukumomi wadanda suke a hannayen yan jaridan Thisday to shine bayan da suka hada komai da komai da bayanai ,wannan ne Committee na Editocin Thisday sun shelanta cewa suna ganin Buhari shine ya ci zaben,a lokacin INEC bat a riga ta fadi ba na sami wannan.Jaridar Thisday suka ce jaridar su tana hasashe a cikin sauki da natsuwa cewa General Buhari shi ya ci wannan zaben kafin a fadi.Suka cigaba da cewa duk da yake Buhari da Jonathan sun cika wannan ka’idan ta tsarin mulki na samun wani kaso a jahohi amma duk da haka Buhari ya bada ratan da ba za a iya cimma ta ba ko da ko wane sakamako za a kawo a nan gaba.Muna taya Goodluck Jonathan murna na domin ya ba Nigeria gado na zabe wanda yake yantacce sannan kuma akwai adalci a cikin shi kuma muna kiranshi day a mika wuya,sannan muna taya Buhari murna saboda nasara mai wahala wanda ya samu bayan gwada was au hudu amma ai sau uku ne ya gwada ba hudu ba saboda a na hudun ne ya ci ai,kuma kiran shi ba ma kawai ya zama mai karimci ba a cikin nasaran daya samu ba amma muna so ya bada mawa magoya bayan Jonathan wadanda suke tsiraru kwanjiyar hankali.Sannan kuma Editocin Thisday din suna gaya way an Nigeria akan cewa lokacin warkar da miki ya fara. Banda wannan akwai kuma Sahara Reporters wanda su Sahara Reporters kamar sune na farko sun riga Thisday,sune na farko da suka yi has ashen Buhari ne ya ci zaben kafin a fadi wanda ya ci zaben.Saboda haka muna da Empirical Evidence wadanda ba su da iyaka wadanda suka wadatar damu daga nazariyyah da adifa da logic (Mandiq)da sauran da sauransu. To bayan wannan shimfidar bari ince wadannan shekara goma sha shidan ko kafin nan ince kenan ba dole bane abinda zan fadi ya yi maka dadi,kuma wasu za sum aka dadi saboda muna mu’amala ne da waqi’i a yanda yake,sannan baka san ra’ayi nab a sai n agama jawabi kuma sai ka ji shi duka,ba zaka iya sanin gamammen ra’ayi na ba wato tattararren ra’ayina ba sai lokacin da na gama jawabi na kuma ka ji shi duka.A yanzu ba ka san komai ba dangane da ra’ayi na ba kuma har in gama baka san duka ba sai dai ka din ga tsinkaya . Wadannan shekaru goma sha shida daga 1999 zuwa 2015 ba lokacin ne aka fara samun matsaloli a nan kasar ba dangane da zabe ko siyasa,sannan wadanda ake ganin su a yau kamar suna neman canji ko suna da’awan su wakilai ne na canji ko abin da yayi kama da haka,da yawa daga cikin su suna tare da wadanda suke zargi cewa bas a son canji a da.Metamophosis yake faru wa ko kuma ince cigaba ne yake faruwa,wani lokaci wadanda suka juya suka zama suna cewa yan canji da gaske ne wani lokaci kuma ba da gaske bane Maslahohi ne na siyasa da ababen da suka yi kama da haka,kuma kila wannan bahsin namu zai fitar da wannan din.Alal hakika ya faro ne kafin nan tun daga lokacin Babangida da kuma lokacin da yayi juyin mulki a 1985 bayan ya hambarar da Buhari.Anan wurin ina so in dan gyara kuskuren da nayi a lokacin da nake bada labarin tarihi na a Harka,kuskure ne guda biyu dayan su ya fi muhimmanci shine wanda nake so na gyara yanzu cewa ba Buhari ne ya saki Shaik Zakzaky kamar yanda akan kuskure na fada haka a lokacin duk da ban koma zuwa ga jawabin ba amma ina tsammanin na fadi haka din,in haka na fadi ba haka bane daidai domin wanda ya saki Shaik Zakzaky shine Babangida bayan ya hambarar da Buhari a Agusta 1985,a wannan lokacin ni ina UK day a faru din,wannan shine kuskure na farkon amma kuskure na biyu bai da muhimmanci saboda ya shafe ni a kashin kaina ne saboda haka ko an gyara ko ba a gyara ba bai da tasiri sosai. Babangida kamar zaka iya cewa shine sanadi ko dalili na mafi yawa daga cikin masifun da ake da su a cikin Nigeria a yau ko ma ba dukkan su gabaki daya ba.Babangida babu abin da bai lalata ba a cikin Nigeria,ya lalata abinda ake ce ma DISCIPLINE wato kenan rike kai (DAF’UN NAFS),ya lalata dukkan kyawawan dabi’u ya zama abinda ya damu Babangida shine EXPEDIENCIES wato Maslaha kuma maslahan ta kashin kanshi yawancin lokuta ko a dukkan lokuta.Babangida ne ya shugabanci zamanin rigingimu na addini a nan kasar kafin Babangida babu rigingimun addini,babu rigingimun kabilanci ko yaki domin kabila ko masarauta ko abinda yayi kama da wadannan,kuma shi kirkiro jihohi masu yawa saboda wannan Expediencies din sannan har a cikin kirkiran jihohin ma sun haddasa rigingimu wajen sanya su manyan biranen su jihohin.Babangida yayi abubuwa masu yawa shi wani bahasi mai zaman kansa.Shi ya rusa Naira,shi ya rusa Civil service ya zo da abin da yake ce ma Director General maimakon Permanent Secretary,ya office Director General ya zama ofishin siyasa wanda Director General yana tafiya ne da shugaban shin a siyasa wato Gomna kenan da sauran su,sannan shine ya rusa zaben Abiola.Abiola ba mala’ika bane tare yake da sojojin din yana masu kwangiloli domin aikin shi ne da sauransu.Sannan shine ya nada Earnest Shonikan da wani abu wanda ya kira da INTERIM NATIONAL GOVERNMENT sannan ya lalata ARMED FORCES ,wannan REGIMENTATION da ESPIRIT DE CORPS da suke cikin Armed Forces Babangida ne ya rusa su gabaki daya ta hanyar wajen Service Chief dinshi ya kan sanya wanda yake bai kai ba kamar a Police duk da yake Police baya cikin Armed Forces a lokacin,zan iya bada misali Babangida zai iya tsallake Deputy Inspector General na Police ya nada Assistance Inspector General a matsayin IG,in an gane abin da nake nufi.Haka yayi lokacin Ibrahim komasi,a lokacin day a sa Komasi ya zama IG,Komasi shi Assistance Inspector General ne a saman shi akwai Deputy Inspector General.To abin da yake nufi da sanya AIG ya zama IG shine kai tsaye Babangida yayi Retire din dukkan DIG din da suke Police a lokacin ko ya fadi ko bai fadi ba saboda ba yanda za a yi DIG ya bi AIG saboda yau ya zama IG,a wannan Cadre din ne akan sharudda na service yaushe ne tarihin shigowa service din ko da da kwana daya ne ko da awa 7 mutum ya riga ka shiga aiki ko da rank dinku daya da shi senior dinka ne da kuma sauran sharudda masu yawa Babangida ba ruwan sad a wannan,haka a soja haka a ko’ina ya rusa wadannan wuraren,tun daga wannan lokacin Armed Forces suka fara samu matsalolin.Akwai abubuwa da yawan gaske wanda aka dinga da’awan suna yi wanda banda lokacin bayaninsu anan wurin.Daga karshe lokacin da ya bada gobnati ga wannan Earnest Shonekan din da nufin kwarya wai ya koma gefe da ma’anar kila wata rana zai dawo,haka abubuwa suka dinga tafiya har Abacha ya zo ya kwace daga Shonekan din sannan yace duk mutumin da yake so ya testing me zamu yi dealing dashi appropriately wato duk wan da yake kokarin ya gwada ko ya jaraba ikon mu to za suyi mu’amala dashi yanda ya dace,daga karshe ya mutu a 1998 nake jin,sannan bayan ya kashe Ken Saro Wiwa,ya kasha mutane masu yawa ya daure Obasanjo da sauransu.Haka kuma ya saci kudi,a lokacin day a mutu ko kuma aka kasha yanda ake da’awa sai suka yi wannan arrangement din na cewa yanzu a saka way an kudu wato Yarbawa,daga nan abu ya fara zuwa kuma su Babangida suka yi wannan cewa a saka wa Yarbawa a hana Abiola ya zama Shugaban kasa to daga nan ne masifar ta faro.Sai aka Obasanjo wanda ya fito daga kurkukun Abacha shi da Oladipo Diya.Obasanjon da ba yana son Abiola bane bai ma goyon bayan Abiola ya zama Shugaban kasa ba,wannan tarihi ne mai yawa amma a lokacin da Obasanjo ya zo yayi barna mai yawan gaske sabanin yanda yayi a lokacin da yake shugaban kasa na soja. Akwai Nasiru el-Rufa’i ba kuma ina nufin ina goyon bayan Nasiru El-rufa’I bane abadaan,a cikin wani abu wanda yayi magana a littafinshi- wannan littafin gaba ki dayan sa na karanta shi duka wato THE ACCIDENTAL PUBLIC SERVANT na Nasiru el-Rufa’I,yana da wani abu da yayi magana akanshi a cikin littafin wanda ya kamata sosan gasken gaske mutane su karanta su fahimta na abinda yake cewa THE THEORY OF SECOND COMING wato Nazariyyar dawo wa ta biyu.Ina so in yi magana akan wannan Nazariyyar dawo wa ta biyu din sosan gasken gaske in da a lokacin da yake magana akan shi Obasanjo,ya kwatanta shi a lokacin da yake shugaban kasa a soja da kuma daga baya a lokacin da ya zama shugaban kasa a farin hula,ka karanta daidai wannan wurin saboda banda lokacin karantawa yanzu.Kuma yanzu muna so dabbaqa wannan Nazariyyar ta The Theory of Second Coming akan el-Rufa’I idan ya zama gobna da kuma akan Buhari a yanzu.A wurin ya fadi shi kanshi tajriban da ya samu wato el-Rufa’i din.Yana cewa Obasanjo lokacin yana soja yana ganin Kaman yayi wa Nigeria aiki amma duk da haka bai fita daga zargin sata ba daga mutane,kamar Fela ya ta zagin Obasanjo da wakoki kamar Zombi,International thief thief,da Vagabones in Power da sauransu da sauransu.To saboda haka lokacin day a dawo a farar hula ya ga ya kamata ya rama abinda ya rasa a wancan lokacin.Shi ma el-Rufa’in ya bad a na shi misalan abubuwan da suka faru dashi ma a lokacin yana Minister da lokacin da baya Minister.Yana cewa “Da ma’aikacin gomnati ya bar aiki sai wannan duk kyaututtuka da sauran su da komi da komi da ya saba da su rana daya sai ya zama sun tafi.Wanda ya aiko maka da katin murnan chrismas a shekaran da ta gabata yanzu da yake ka bar office ba zai aiko maka wannan ba,kowacce shekara a lokacin kana gomnati za ka iya samun kati 1000 na taya murna,duk na karya ne da fadanci amma a shekara mai zuwa bayan ka bar office kila ka kati 10 na taya murna,daga nan daga nan da sauransu,har yace wai ya fara tunanin ko wayanshi ta lallace ne domin idan da kana samun kira sau dari ne a rana saboda sunanka Minister da masu ziyara masu yawan gaske to a lokacin da ka bar gomnati zai wadannan ziyarce ziyarcen da kiraye kirayen su sauka zuwa kusan zero wato sifur.Ku karanta wannan wajen inda kira shi da kanshi cewa Theory of second coming. To lokacin da Obasanjo ya zo na biyu sai ya zama yayi abubuwa masu yawan gaske wadanda suke basu da kyau,ya kara raba mutanen Nigeria akan layukan addini da kabila,sannan yayi yaki na cin hanci da rashawa wanda yake babu adalci,babu lokacin bayani akan wannan.Su EFCC da ICPC Obasanjo yana amfani dasu ne wajen yaki da abokan gaban shi ne a siyasa suka zama kaman abinda ake ce ma ATTACK DOGS wato Karnukan hujumi akan abokanan adawansa na siyasa.Akwai abubuwa masu yawan gaske da suka dinga faruwa a lokacin,uwa uba a lokacin ya zo da wannan Agender din na THIRD TERM wato karo na uku wanda wannan karo na uku din inda yayi nasara to da zai cigaba ne har abada da kuma wannan furucin da aka naqalto shi ya fadi wato “NO THIRD TERM NO NIGERIA”ma’ana in ba zan dawo karo na uku ba to Nigeria ta kare wato sai dai Nigeria ta rushe amma dole sai na dawo karo na uku.Wannan Allah subhanahu wa ta’ala ne ya kautar da wannan masifar a wannan lokacin ta hanyar Bill din ya rushe a majalisar kasa kafin su kansu yan majalisan su gane ya rushe ya mutu,wannan ka je ka bincika akai.Mutane da yawa sun taka rawa a wannan lokacin wajen rusa bill din kaman akwai mutane irin su Ken Nnamani Shugaban Senate a lokacin da Hon Aminu Bello Masari shugaban majalisar wakilai a lokacin sun tsaya tsayin daka a lokacin,akwai irin su Toni Anini da su Ahmadu Ali su sunyi duk abinda za suyi domin abin yayi nasara,kamar su Nasiru Mantu sun yi duk kokarin su domin abin ya yiwu amma sai Allah ya rusa shi albakacin su Ken Nnamani da Masari wadanda a lokacin suka tabbatar abin bai faru ba sannan suka tabbatar abin da ke faruwa a ita majalisa an sanya shi a talabijin kai tsaye saboda haka ba wanda yake so a ga yana daga cikin wadanda suke son abin yayi nasara,abubuwa da yawa sun faru lokacin har abin ya rushe.A lokacin da abin ya rushe Obasanjo baya Nigeria saboda ta bayyana ba shi yasa ayi bad a ya dawo tafiya sai yace shi ana ta ce mashi third term third term alhali shi third term din nan bai san daga inda ya faro ba?wane ne ya taba gaya wa wani cewa yana so ya zarce wai shi bai taba gaya kowa ba yana so ya zarce ba,ya mursisi ya murje idanunsa yace bashi yace ayi ba,to amma daga nan sai yayi alkawari cewa duk mutanen da suka taimaka ko adawa da zarcewan shi sai sun ji a jika har da mutanen Nigeria,2008 kenan wato bayan ya bar mulki kenan amma tun daga 2007 ne ya fara.Irinsu Aminu Bello Masari din shi yaso ya zama gomnan katsina ya gaji Umaru Musa Yar’aduwa saboda dukkansu a lokacin suna PDP ne sai Obasanjo ya tabbatar da bai zama ba,shine kaman sadaukarwar da Masari ya yi a lokacin kuma shi (Obasanjo)ya maida su politically irrelevant wato dukkan wadanda suka ja da wannan third term din. Aka ce a lokacin Obasanjo yace a nemo masa mutunen da suka yafi kowa rashin lafiya a cikin yan siyasa kamar yanda aka ce sai aka ce a kawo masa Makarfi da Umaru Yar’aduwa sai yace daga cikin su biyun wane ne yafi tsanani a rashin lafiya?sai aka ce mashi Umaru ya fi tsanani a rashin lafiya saboda zai iya mutuwa a kowane irin lokaci sai yace to Umaru ne zai zama Shugaban Kasa.Na yanke maku abubuwa masu yawa daga cikin abubuwan da aka ce din domin in zo yau.Obasanjo ya dinga yawo a jirgin sama a ranar zaben 2007 daga jiha zuwa jiha sai day a tabbatar da yayi irin abin da NPN ta yi a 1983 wanda ya sababba juyin mulkin su Buhari.Shine duka jihohin kasar nan aka ce PDP ne ta ci musamman Arewa maso yamma wanda da ANPP ne duk gabaki dayansu suka koma PDP,to sai aka sa Umaru .To kafin 2007 din an gamsar da Buhari akan ya shiga siyasa saboda haka 2003 ya yanki katin jam’iyya a Daura.Kuskuren Buhari babba wanda zamani ya koya mashi darasi akan wannan kuskuren shine ran nan da ya yanki katin zaben a ran nan ne ya ayyana yana so ya zama shugaban kasa wato ya shiga siyasa don saboda ya zama shugaban kasa,to shine hakika ta koya masa darasin shekara 12 kuma yana bukatan wannan darasin kuma kowanne mutum yana bukatan wannan darasin,so kana bukatan lokaci saboda haka wannan shekara 12 sun koya masa yaudara da kulle kulle irin nay an siyasa,sun sa ya fahimci yanzu ba soja bane wanda suke aiki da Decree wato jinginar da tsarin mulki sannan ya samu bakin ciki mai yawan gasken gaske har kuka yayi a bainal jama’a,yana bukatan wannan. Sannan duk da haka ina ga kamar bai koyi duka darasin ba,har yanzu akwai darussan day a kamata ya koya saboda har yanzu bai san mutanen da suke tattare dasu ba a hakikanin su kamar yanayin mutane irin su Nasiru el-Rufa’i da Ahmad Sani Yariman Bakura ba.Nasiru el-Rufa’i dukkansu ana ce masu Mallam shi da Yariman Bakuran wato Malam Nasiru Ahmad el- Rufa’i,wanshi babba shine Ali Ahmad Rufa’i yace bai san a cikin gidan su a ina aka samu EL din ba wato bai san baban su sunansa el-rufa’i ba saboda haka ne shi wan nasa AGM Ali Ahmad Rufa’i bai kiran kansa da el-Rufa’i amma da Bashir wan Nasiru din dashi Nasirun suke kiran kansu el-Rufa’i kila Bashir din ne ya fara kiran kanshi da el din sai Nasiru shi ma ya fara,duk irin wadannan abubuwan kuna bukatan ku sani saboda haka ku daina raina kanakanan abubuwa. Nasiru el-Rufa’i wanda yake yayi Masion Fellowship a F Kennedy,kana bukatan ka san wannan,yayi rayuwa mai wahala a wajen karatun da yayi a Colarado da a Warshington DC Burston da kuma UK a lokacin da yake karatunsa LLB Law a Harvard a America,kana bukan ka san wadannan abubuwan day a sanya a cikin kwakwalwan shi da ya kwakwalwan take aiki,kun gane abin da nake nufi?shine Empirical Evidence da muke magana akai.Wannan Mansion Fellowship din wanda yayi a Kennedy School me ya haifar mashi?ba suran mutum ba aikin kwakwalwan shi wato yanda kwakwalwan shi take aiki,tunaninsa,akidansa,da Ideology dinsa.Kila idan muka zauna da Nasiru el-Rufa’i wata rana idan ta yiwu ya mana bayanin wannan Masion Fellowship din a Kennedy School meye Mustalzimat dinsu?Sannan kuma da sauran ra’ayoyinsa da tasarrufofinsa da sauransu da sauransu wasu masu kyau wasu bah aka ba tun lokacin da aka fara sanin sa a Bureau for Public Enterprices karkashin Atiku Abubakar a lokacin farko daga baya ya zo ya koma karkashin Obasanjo daga karshe ya zage su su duka shi yasa ake cewa shi Buhari yayi hattara kila shine na gaba wanda zai zaga.Sannan banda irin wadannan mutanen akwai mutane irin su Orubebe da su Femi Fani Kayode da sauran su duka tare suke da su Nasiru el-Rufa’i karkashin Obasanjo,kowa yana bukatan ya san haka,yana yi ne ya dinga canja canja su sai suka dinga rarrabuwa kamar Nuhu Ribado,kamar irin Ongozie da kaman su Obi da kaman su Soludo da sauransu da sauran su.A asalin su suna tare ne yanayoyi suka dinga caccanja su,to lokacin da suke rassa ya kamata ka da rassan su bace maka,ka dinga bin kowanne da rassan sad a sauransu da sauransu.Akwai ra’ayoyin Nasiru el- Rufa’i wand azan yi magana nan gaba kila a karshe lokacin da nake so in yi magana akan ya nake ganin shakalin gomnatin Buhari. To bana ganin kamar Buhari ya koyi komai da komai har yanzu kamar ra’ayinshi dangane da adalci misali da abubuwan da suka yi kama da wannan,kila a gaba ne zan yi magana akan su. WASAL-LAHU ALA MUHAMMADIN WA ALIHID DAYYIBINAD DAHIRIN.ABNA