Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA
Talata

3 Faburairu 2015

11:51:56
669039

Cibiyar Ahlulbaiti{A.S} ta duniya tayi tofin Allah wadai a kan abunda ya faru a Pakistan

Fatan da muke ga kungiyoyin kasa da kasa shine suyi aiki da abunda ya doru akan su wajan yaki da ta'addanci da kuma kauda duk wani nau'I na fizara acikin al'umma,kuma suyi Allah wadai da abunda ya faru a Pakistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-ABNA- cibiyar Ahlulbaiti{A.S} ta duniya tayi tofin Allah wadai a kan harin ta'addancin da aka kai ma yan shi'a a yayin gudanar da sallah a garin shikorfur na Pakistan wanda yai sanadiyar rasa rayu kan mutane sama da 60 wasu 50 kuma suka jikkata.

Ga sanarwar kamar haka.

Da sunan Allah madaukakin sarki.

Yan ta'adda masu wuce gona da iri sun sake aukama bayin Allah wadanda basuci basu shaba kuma suka zubdar da jinanain su a kan zalunci.

Tsanani kishin mazahaba ya dade acikin tarihi amma a yanzu yan mulkin mallaka na kasashen yamma irin su Amurka da haram tacciyar kasar Isra'ila na Ingila suna amfani da wannan damar domin kawo sabani acikin al'ummar musulmi.don haka cibiyar Ahlulbaiti{ A.s} ta duniya abisa nauyin da ya rataya akan ta tana Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kaima masu sallah a Hussainiyar Karbalaye mu'alla wadda ke yankin shikorfur na kasar Pakistan kuma cibiyar na kira ga dukkan mabiya mazhabobi daban daban a Pakistan dasu zauna da junan su cikin aminci.

Kuma tana kira ga wadanda abun ya shafa da karsu dauki doka a hannunsu wajan rama abunda a kai masu abunda yafi dacewa shine subi hakinsu a hukumance.

Sobada haka cibiyar na kira ga majalisar dinkin duniya da kuma kungiyoyin musulmi da suyi aiki da nauyin da ya rataya a wuyan su wajan la'antar wannan hari na ta'addanci kuma su tashi haikan domin kawar da duk wani nau'I na ta'addanci a Pakistan da kuma duniya baki daya.

Cibiyar Ahlulbaiti{A.S} ta duniya.ABNA