Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

9 Janairu 2025

20:30:33
1521638

Al-Huthi: Isra'ila Na Neman Mamaye Kasashen Gabas Ta Tsakiya Ne

Ya kamata kasashen Gabas ta Tsakiya su dauki shirin Isra'ila a matsayin barazana ga kansu. Tun daga farko yahudawan sahyoniyawan sun zo Palastinu ne da nufin samar da babbar Isra'ila.

Sayyed Abdul Malik Al-Houthi, Babban Sakatare Janar na Ansarullah Yaman:

Ya kamata kasashen Gabas ta Tsakiya su dauki shirin Isra'ila a matsayin barazana ga kansu. Tun daga farko yahudawan sahyoniyawan sun zo Palastinu ne da nufin samar da babbar Isra'ila.

Amurka na satar man fetur na Siriya kuma ta sami iko akan rijiyoyin man Siriya. Amurka da Isra'ila ba za su gamsu da mamaye Siriya ba, kuma sannu a hankali za su fadada yankunansu da suka mamaye.

Dangane da shirin da yahudawan sahyoniyawan suka sanar a baya-bayan nan mai suna Babbar Isra'ila mai girma, ya kamata mu sani cewa Isra'ila na neman mamaye kasashen yankin gabas ta tsakiya ne.

Kalaman jami'an gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da suka hada da ministan kudi, ministan tsaro, da sauran ministocin kasar, sun nuna matukar bacin rai da kyamarsu ga al'ummar Palastinu da Larabawa.

Sannan Duk gwamnatocin da ba ruwansu da yunwar Falasdinu suna da hannu cikin laifukan Isra'ila.

Sayyed Abdul Malik Al-Houthi, Babban Sakatare Janar na Ansarullah Yaman:

Laifin kashe al'ummar Palastinu bai takaitu ga makiya yahudawan sahyoniya ba kawai, a'a, dukkanin gwamnatocin da suke nuna halin ko in kula, Marowata, matsorata da suke kallon irin wahalar da al'ummar Palastinu suke yi na yunwa, suna da hannu cikin wannan laifin.

Makiya yahudawan sahyoniya sun kafa kungiyoyin mayaudara da sojojin haya domin wawashe kayan agaji da aka aika zuwa Gaza kusa da shingayen binciken sojojin gwamnatin kasar.

A wannan makon, sojojin Isra'ila da kansu sun wawashe kayan agajin da ke shiga yankin zirin Gaza kai tsaye.

Da gangan makiya yahudawan sahyoniya sun haifar da wani mummunan yanayi a zirin Gaza tare da kai hari bisa dukkan ababen more rayuwa na lafiya.

Laifin da makiya Isra'ila suka aikata a asibitin Kamal Udwan babban laifi ne kuma daya daga cikin manyan laifukan da aka aikata a zirin Gaza.

Yanzu haka dai makiya Isra'ila na kai hari kan asibitin Indonesiya da wasu asibitocin da ke ba da ayyuka kadan a karkashin mummunan yanayi na kawanya.