Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na AhlulBaiti (As) -ABNA- ya habarto maku cewa: Tashar talabijin ta 12 ta yahudawan sahyuniya a hukumance ta sanar da mutuwar wasu sahyoniyawa 3 da suka jikkata a wani farmaki da aka kai kusa da garin Kodomim da ke yankin Qalqilye a arewacin gabar yammacin kogin Jordan.
Akalla wasu yahudawan sahyoniya 7 ne kuma suka jikkata a wannan farmakin.
Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da sintiri a sararin samaniyar arewacin gabar yammacin kogin Jordan domin neman maharin a kusa da Kodomim.
Yahudawan sahyoniya 6 ne suka jikkata sakamakon farmakin da aka kaiwa yahudawan a yammacin gabar kogin Jordan
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta gwamnatin Sahayoniya (Star of David) ta bayar da rahoton cewa, an jikkata yahudawan sahyoniya 6 sakamakon wani harbi da aka yi a kusa da garin "Kedomim" da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan.