Bayan kwashe kwanaki 456 na tsarewa, Kataib Al-Qassam ta wallafa faifan bidiyon halin da wannan fursuna take ciki. Amma ba a sake watsa wannan faifan bidiyo a kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya ba bisa bukatar danginta.
A ranar 7 ga Oktoba, 2023, sojojin Falasdinawa sun kama Leri Elbeg daga wani sansanin gadi a sansanin sirri na Nahal Oz tare da sauran abokan aikinta.
Albagh ta bayyana a cikin wannan faifan bidiyo cewa sama da kwanaki 450 da Hamas ke tsare da ita amma kuma hukumar Isra'ila ba ta yi wani yunkuri ba wajen kubutar da ita ba.