Dan jaridar mai wakiltar soja na
Channel 13 na gwamnatin Sahayoniya ya ce: Na kasance a Jabalia kwanaki 2 da
suka gabata. Dakaru da yawa suna nan a wannan yanki amma duk basu san me yah au
kan su ba.
Babu alamar kawo karshen Hamas da kuma samun wanda zai maye gurbinta da zai jagoranci Gaza. Ta hanyar kashe kowanne daga cikin sojojinta, mutane da yawa masu shekaru daban-daban suna shiga Hamas.
Yaqub Omidror, tsohon shugaban kwamitin tsaron cikin gida na gwamnatin Sahayoniya ya ce: Duk wanda yake tunanin Gaza za ta mika wuya, to ya rudu. Ba za a taba iya samun sallamawa da miqa wuya a Gaza ba.