Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

2 Janairu 2025

10:43:16
1519265

Tunawa Da Cika Shekaru 9 Da Aiwatar Da Hukuncin Kisa Shekh Nimr Baqir Al-Nimr Da Gwamnatin Al Saud Ta Yi.

An tuna da cika shekaru 9 da aiwatar da hukuncin kisa da shahadar Hujjatul-Islam Shekh Nimr Baqir al-Nimr da gwamnatin Al Saud ta yi.

A rana irin ta yau ne kotun hukunta manyan laifuka ta kasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan Sheikh Nimr tare da gicciye shi an kashe shi aka gicciye shi a bainar jama'a bisa laifin yin adawa da masarautar Al-Saud da yada mazhabar Shi'a. shi mabiyin shia’a ne Isna Ashari  wato Imamai sha biyu kuma ya zauna a birnin Qatif na kasar Saudiyya kuma ya kafa cibiyar addini ta Imam al-Qaim a kasar Saudiyya.

A cikin kalamansa, Sheikh Nimr ya kwatanta Sarki Salman da Yazid, ya kuma tsine masa albarka da cewa: “Da Yazid ne ma to da haka zai fadi irin maganar da Sarki Salman kuma da zai bi tafarkinsa ne. Wannan al'ummar da ake zalunta ba za ta zauna lafiya matukar ba kifar da gwamnatin Al Saud ba. Allah ya tsinewa Sarki Salman da Yazid”.

Bayan rasuwar yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya ya yi farin ciki ya ce a gaskiya: Ta yaya ba za mu ji dadin rasuwar Naif bin Abdulaziz ba. Ta yaya ba za mu yi farin ciki da mutuwar wani da ya jawo ta’addanci da fargaba ba. Muna godiya ga Allah, kuma Allah Ya dauki ran su gabaki daya, daya bayan daya na gidan Sarautar Al Sa’ud da na gidan Khalifa.

Ya bayyana a zargin da akewa Sheikh Nimr cewa: “Ya bukaci gwamnati da ta duba halin da makabartar Baqi’a ke ciki, kuma ta amince da mazahbar Shi’aa hukumance, da kuma ta dawo da martabar ‘yan Shi’a a Saudiyya.