Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

1 Janairu 2025

18:23:49
1519107

Archbishop Robert Lugal: Tawali’u Da Kankan Da Kai Na Daga Cikin Halayen Annab Isa As

A Ci Gaba Da Gudanar Da Taron Tunawa Da Annabi Isa (AS) A Jami'ar Ahlul-Baiti (AS) / Jaddada Matsayin Iran Na Tarihi Da Goyon Bayan Addinai Na Ubangiji.

Bayan haka, Robert Lugal, Archbishop na Toulouse a Faransa, ya gudanar da jawabi in da ya ce: Tawali’u, sassauci da Kankan da kai su ne halayen fansa na Annabi Isa Almasihu (A.S).

Yayin da yake ishara da halin Annabi Isa (AS) a cikin Littafi Mai Tsarki, ya kara da cewa: Allah ya aiko da Mala’ika Jibrilu zuwa ga Maryamu, su ne dai mala’ikun da su kasance manzanni ne da Allah ya bayyana mana manufarsa ta hanyarsu.

Robert Lugal ya ambaci Maryamu a matsayin uwa mai tsarki, mai kirki, mai cike da gafara, tagomashi, alheri kuma mai gata, ya ce: Mala’ika Jibra’ilu ya ɗauki tsoka daga cikinta ta wurin Ruhu Mai Tsarki domin a haifi “Almasihu” da Allah ya tsarkake.

Babban Bishop na Toulouse a Faransa ya kara da cewa: Allah Maɗaukakin Sarki, ta wurin mala’ikansa, ya sa wa ɗan Maryamu suna Isa, wanda ke nufin mai ceto, ɗan da aka haifa ta hanyar mu’ujiza kuma zai zama mai ceton mutanensa da kuma dukan ’yan Adam.

Robert Lugal ya jaddada cewa: Yesu mai ceto, ya zama mutum domin ya cece mu, mai mulki na iya tsoratar da mu kuma babban shugaba zai iya rinjayar mu, amma a ƙarshen zamani Annabi Isan da aka kashe a matsayin hadaya, zai bayyana kuma ya ci nasara.

A cewar Robert Lugal, Bisharar Matta ta kira Yesu (A.S) a matsayin mai sassauci, tawali’u da Kankan da kai.