Parachenar, birni ne da 'yan
Shi'a suka fi yawa, wanda ke da mutane sama da 800,000, an shafe kwanaki 80 ana
ci gaba da yin kawanya a birnin. In da sojojin sun rufe hanyoyin sadarwa tare
da haifar da babbar matsala ga jama'a. A makon da ya gabata ma ‘yan Shi’a biyu aka
kasha a cikin wata guda kuma an yi wa ‘yan Shi’a sama da 50 kisan kiyashi,
sannan sama da mutane 150 ne suka mutu sakamakon rashin magani.
Dakarun takfiriyya da suka hada da Sipah Sahaba Pakistan (SSP) da wasu mayakan sa kai masu dauke da makamai suna aikata laifuka a wannan yanki. Wadannan kungiyoyi suna neman share Parachenar daga mazaunanta na Shi'a don taimakawa wajen gina sansanin sojin Amurka a Korem.