Jagoran juyin juya halin Musulunci
a cikin jawabinsa a wurin taron cika shekaru biyar da shahadar Sulaimani:
Abubuwan da suka faru a cikin wadannan ’yan shekarun nan da masu kare haramin sun nuna cewa juyin juya halin Musulunci yana nan a raye.
Bayan isar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran a Husainiyar Imam Khumaini (Qs) da kuma fara gudanar da taron tunawa da cika shekaru biyar da shahadar Laftanar Janar Hajj Qasim Sulaimani.
Farkon jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi a wajen taron cika shekaru biyar da shahadar Hajj Qasim Sulaimani ya fara ne da yin nasihohi game da shigowar watan Rajab.
Inda yace watan Rajab: Watan Rajab watan addu'a da yin ibada da tawassuli ne.
Bayan nan jagoran juyin juya halin Musulunci yayi gaba da jawabi game da matakin da Shahidi Sulaimani ya dauka na ceto kasar Iraki a farkon harin da dakarun kasashen waje suka kai.
Jagoran juyin juya halin
Musulunci a wata gabar ta bayanansa ya tabo banagren masu kare wurare masu
tsarki in da ya ce: Kare wurare masu tsarki wata ka'ida ce ta asali ga Haj
Qasim Sulaimani. Ya kuma kira Iran wuri mai tsarki.
muna tafe maku da fassarar cikakken bayaninsa nan gaba In Sha Allah...