Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

30 Disamba 2024

20:11:14
1518366

Yau Majalissar Ahlul Bait As Ta Duniya Ke Cika 34 Da Kafawa

Majalisar Ahlul Baiti ta Duniya majalisa ce mai zaman kanta wacce aka kafa ta da nufin gabatar da addinin Musulunci da yada koyarwar Alkur'ani da Ahlul Baiti (AS) da karfafa hadin kan Musulunci da tallafawa mabiya Ahlulbaiti (as) a duniya,

Majalisar Ahlul Baiti ta Duniya majalisa ce mai zaman kanta wacce aka kafa ta da nufin gabatar da addinin Musulunci da yada koyarwar Alkur'ani da Ahlul Baiti (AS) da karfafa hadin kan Musulunci da tallafawa mabiya Ahlulbaiti (as) a duniya, kuma tana da ayyuka da suka dace da wadannan manufofin. An kafa wannan kungiya a shekara ta 1369SH tare da goyon bayan Sayyid Ali Khamenei jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya ke nada babban sakataren wannan majalisa. Raza Ramazani Gilani shine babban sakatare na wannan majalisa a yanzu.

Tarihi, Manufofi Da Tushenta

An kafa Majalisar Ahlul Baiti ta Duniya ne a ranar litinin 10 ga Day, 1369 wanda yayi daidai  13 ga watana Jumadas Sani shekara ta 1411 kuma ya dace da 31 ga watan December 1990; shekarau 34 kenan da suka gabata. Kafin haka dai malamai 300 musamman mabiya tafarkin Ahlul-baiti sun halarci wani taro a birnin Tehran, sannan kuma suka samu izini da amincewar Sayyid Ali Khamenei jagoran Jamhuriyar Musulunci na Iran na kafa Majalisar Ahlul-baiti (AS) ta duniya.

Kadan daga cikin manufofin kafa Majalisar Ahlul-baiti (AS) ta duniya, sune:

Kare addinin Musulunci gaba daya da alfarmar Annabi da Alkur'ani da Ahlul Baiti (SAW).

Zurfafa da karfafa hadin kai a tsakanin al'ummar musulmi musamman mabiya Ahlul Baiti (AS).

Tallafawa hakkin musulmi a duniya da matsayin mabiya Ahlul Baiti (AS).

Bunkasa ababen more rayuwa na zahiri da ruhi na mabiya Ahlul Baiti (AS) a duk fadin duniya

Cire mabiya Ahlul Baiti (a.s) daga zaluncin kafafen yada labarai da tauye ilimi da tattalin arziki.

Ƙoƙarin samar da zaman lafiya, abokantaka, haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin dukkan mutane da al'ummomin duniya.

Babban Sakatare shi ne babban jami’in zartarwa na Majalisar Ahlul-baiti (AS), wanda aka nada shi bisa hukuncin jagoara waliyul Faqih don majalissar da aiwatar da manufofin da aka amince da su. Zuwa yanzu an zabe sakatarori biyar tun bayan kafa majalisar sune kamar haka:

Muhammad Ali Taskhiri (tun watan Urdubisht 1369),

Ali Akbar Welayati (tun watan Murdad 1378),

Mohammad Mahdi Asefi (tun Mehr 1381),

Mohammad Hassan Akhtari (tun Farwardin 1383),

Reza Ramezani Gilani (tun watan Shahriwar 1398).

Ayyukan Da Majalissar Ta Gabatar

1- Tashar Al-Saqlain: Cibiyar sadarwa ta tauraron dan adam da ke aiki a cikin harsunan Larabci da Ingilishi. Rijista a hukumance na wannan hanyar sadarwa tana cikin Netherlands kuma hedkwatarta tana cikin Türkiye. Daya daga cikin manufofin wannan hanyar sadarwa shi ne samar da abubuwan da suka shafi Musulunci ga bangarori daban-daban na al'umma. An kafa wannan cibiyar sadarwa a cikin shekara ra 1388 shamsiya.

2- An gudanar da taron kasa da kasa na Imam Sajjad (a.s) a ranar 24 ga watan Agustan shekarar 1394 tare da halartar baki sama da 500 na kasashen waje a zauren taron.

3- Taro na ilimi da na al'adu da nune-nune: don bugawa da faɗaɗa al'adun Ahlul-Baiti (AS) da kuma shigar da masana duniyar musulmi cikin lamurran tunani da akida, tarurrukan ƙasa da yanki da na duniya daban-daban da taruka da tarurruka kamar su.

4- Taron kasa da kasa na Imam Hasan Mujtaba (a.s.): majalissar ce da nufin karfafawa da fadada kokari da sadaukar da kai ga tafarkin Ahlul Baiti, da samar da dandali da ya dace na sanin addini bisa dabi’ar Ahlul Baiti (a.s.). Bayyanawa da kuma gabatar da siffa ta Imam Hasan (a.s.) da kuma bayanin ka'idar Aminci da magance rikici a hangen Imam Hasan As.

5- Nasser Kabir International Conference

6- Babbar lambar yabo ta Manzon Allah (SAW): An kafa bikin al'adu da fasaha na Ahlul-Baiti (a.s) da nufin amfani da sifofin fasaha wajen kare addini. An gudanar da bugu na farko na wannan biki ne a karkashin taken babbar lambar yabo ta Manzon Allah (SAW) tare da taken Annabi Muhammad Mustafa (SAW) a shekara ta 2012-1393.

7- Ranar Kudus ta Duniya: A cikin watan Ramadan na shekara ta 1435 bayan hijira, an gudanar da taron ranar Qudus na kasa da kasa na farko mai taken ranar Quds, ranar hadin kai da tsayin daka ga al'ummar musulmi.

8- Kamfanin Dillancin Labarai na Abna: An kafa wannan kamfanin dillancin labarai ne a shekarar 2004 cikin harsuna uku domin nuna labaran ‘yan Shi’a na duniya da kuma sanar da ‘yan Shi’a halin da juna ke ciki.

9- Wiki Shi'a: Wiki Shi'a manhajja ce ta yanar gizo wacce ke aiki a fagen gabatar da mazhabar Ahlul Baiti (a.s) da buga koyarwar Musulunci da Shi'a. Wannan kundin sani ya fara aikinsa a watan Yuni 2013 kuma a halin yanzu yana aiki a cikin harsuna 22 kuma yana da labarai 8,761 a cikin Farsi…