Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

27 Disamba 2024

18:21:44
1517428

Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Sojojin Yahudawa Suka Kona Asibitin Kamal Udwan Da Ke Arewacin Zirin Gaza

Sojojin mamayar Isra'ila ta sun ƙona wannan asibitin inda hayaki mai duhu da karfi ya bazu a sararin samaniyar wannan yanki.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya kawo maku rahoton cewa: Zuwa yanzu sojojin Isra'ila sun ƙona asibitoci 34 a zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Tun daga farkon mamayar zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, gwamnatin sahyoniyawan ta kona asibitoci 34 a wannan tsibiri, wanda na baya bayan nan shi ne asibitin "Kamal Udwan" da ke arewacin zirin Gaza.