Falasdinawa 40,000 ne suka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa.
Adadin shahidan yakin Gaza ya kai mutane 45,436
Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a zirin Gaza ta sanar a cikin wata sanarwa a rana ta 448 ta yakin:
A cikin sa'o'i 24 da suka gabata sojojin mamaya na gwamnatin yahudawan sahyoniya sun sake yin kisan kiyashi har sau 3 kan fararen hular Palasdinawa a wannan yanki.
A cikin wadannan hare-haren, Palasdinawa 37 ne suka yi shahada sannan mutane 98 suka jikkata.
Adadin shahidan yakin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoban bara ya kai mutane 45,436 kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 10,8038.
Fiye da mutane 11,000 ne har yanzu ba a gansu ba kuma a karkashin baraguzan yankin Zirin Gaza.